
24/07/2025
Tsohon fitaccen ma'aikacin BBC, Ibrahim Isa, ya buƙaci a kai zuciya nesa
Ibrahim Isa ya bayyana hakan ne ta cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, bayan ce-ce-ku-cen da ya barke kan tsangwama da kyara da wasu tsoffin ma'aikatan BBC Hausa s**a ce sun fuskanta daga abokin aikinsu lokacin da suke aiki a gidan rediyon.
A cewar Ibrahim, BBC gida ne da ya gina zumunci da haɗin kai tsakanin ma’aikata, kuma da dama sun amfana da zaman su a can ta fannoni da dama, ciki har da ɗaukaka da samun masoya. Ya ce yana jin takaici matuƙa da yadda cece-ku-ce ke ci gaba da yawo kan al’amarin, yana mai jaddada cewa ya kamata a saurari ɓangarori biyu kafin a ɗora laifi.
Ya ƙara da cewa akwai bukatar tsoffin ma’aikata da ke jin bacin rai su daure, su rungumi yafiya da juriya, domin a cewarsa, fusata da bayyanar da ɓacin rai a fili ba shi ne mafita ba. Ya yi kira da a daina cin mutunci da ɓata suna, yana mai jan hankali kan muhimmancin ci gaba da sada zumunci da mutunta juna.
Ku bayyana ra'ayoyinku...