Fityanul Islam Of Nigeria

  • Home
  • Fityanul Islam Of Nigeria

Fityanul Islam Of Nigeria Yada Soyayyan Annabi ﷺ Da Salihan Bayin Allah Waliyai Tare Da Fadakarwa Tunatarwa Ga Al'ummar Musulmi Alhamdulillah

BARKA DA JUMA'AT: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR, Allah Ya Bamu Albarkan ANNABI MUHAMMADU saww. Amiin Yaa Allah
11/07/2025

BARKA DA JUMA'AT: Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR, Allah Ya Bamu Albarkan ANNABI MUHAMMADU saww. Amiin Yaa Allah

SON ANNABI MUHAMMADU SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA IMANI NE. Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da saba...
09/07/2025

SON ANNABI MUHAMMADU SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA IMANI NE.
Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da sababbansa, da duk wanda yake biyayya ko koyi da abin da ya bari.
Duk wanda babu soyayyar ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA a ransa ko Yaji soyayyar wani tafi ta ANNABI a ransa, To Ya binciki imanin sa.
A cikin Hadisai Guda 2 ANNABI ya sanar da mu.
“Babu dayan ku da zai zama yana da imani
Sai ya zamo yafi kauna ta fiye da kansa, mahaifinsa/mahaifiyar sa, Ko dansa/'yarsa da sauran mutane.”
Mutane sun hada da malaminka/oganka/ mai kula da kai, ko wanda ya ke ba ka kariya cikin mutane in ka shiga kunci ko damuwa.
Muyi koyi da ayyukan ANNABI da maganganun sa, Duk wanda ya saba da Umarnin da ANNABI (S.A.W) ya bayar, ko waye! kabi ANNABI ka kyaleshi.
Muyi tutiya da son ANNABI (S.A.W) kuma ku bayyana shi a ko ina, a ko da Yaushe.
Domin yafi kaunar da mu ke tutiya da ita ta matan mu, iyayenmu, ‘Ya’yanmu, da Makusantan mu.
Yin salati ga Annabi yana cikin kauna da soyayyar sa.
Mu yawaita salati gareshi.
Allah ya kara mana son ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA
Amin.

Madinah garin Manzon Allah (saw). Allah ya kaimu birnin Madinatul Munawwara. Ameeeen
08/07/2025

Madinah garin Manzon Allah (saw). Allah ya kaimu birnin Madinatul Munawwara. Ameeeen

06/07/2025

SHI DA KANSA MAI MAGANAR SAI DAI YA FITO YA BAYYANA NADAMAR SA DA TUBAN SA (Malam Abdul Jabbar Yayi Nadama).

06/07/2025

RADDI ZUWAGA ABDUL JABBAR TARE DA SAQO ZUWA GA IYAYE AKAN 'YA'YAN SU DAGA SHEIKH FERFESA UMAR SANI FAGGE KANO.

06/07/2025

GASKIYAR ZANCE: Kada a kautar mana da hankula mana daga irin wannan katobarar har ma a dinga bashi mafita da kariya kamar ba annabin ne a gaban mu ba.

Tare da dukkan girmamawa zan so Prof ya saurari maganganun Abduljabbar Kabara da sune s**a janyo kotu ta hukuntashi.Daga...
06/07/2025

Tare da dukkan girmamawa zan so Prof ya saurari maganganun Abduljabbar Kabara da sune s**a janyo kotu ta hukuntashi.

Daga: Malam Aminu Daiba Kano

Lokacin ƙadayyar Abduljabbar idan ban manta ba Naji Prof din yace bai saurara ba kuma baya so ya saurara, to tunda Malam yana so yace wani abu game da batun to zan so ya saurara domin yiwa ko wane ɓangare Adalci.

Abin da yasa na magantu na samu halartar zaman shari'ar Abduljabbar 70%100 kuma na saurari tuhume tuhumen da ake masa da zaman muƙabalar da akayi, tun kafin nan nata bibiyar karatuttukansa da raddin da malamai suke masa, kaga kuwa zan dan fahimci wani abu dan gane da lamarin.

Bayan gama shari'ar Abduljabbar naji Prof ya magantu, yanzu ma ya dawo da zancen, dan haka zan so na kusa kusa su isar da saƙona ga shugabanmu Prof Ibrahim Maƙari Rahimahullah.

Allah yahanamu zamewa a cikin hadara ta Annabi S.A.W yasa mufi ganin girmansa fiye da komai da kowa. Amiiiin Yaa ALLAH

Allah Ya Saka Maka Da Maficicin Alkhairi, dan'adam yana dai-dai yana kuskure. Allah ya yafe mana kurakuran mu. Amiiiin Y...
06/07/2025

Allah Ya Saka Maka Da Maficicin Alkhairi, dan'adam yana dai-dai yana kuskure. Allah ya yafe mana kurakuran mu. Amiiiin Yaa ALLAH

06/07/2025

DAGA KARSHE PROF MAQARY: Ya yarda Malam Abdul Jabbar yayi batanci ga janibin fiyayyen halitta Annabi MUHAMMADU saw, Amma irin tsarin zaman da hukunci da aka yiwa Abdul Jabbar bai yi ba. Ya kuma bada shawara akan tsarin wa'azi a kasar Najeriya.

Muna kira ga mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shirya Muqabala akan magagganun Malam Lawan Triumph akan w...
06/07/2025

Muna kira ga mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shirya Muqabala akan magagganun Malam Lawan Triumph akan wasu Hadisai fassaran gatari. Yin haka zai zama adalci ga al'ummar musulmai na Kano, Najeriya har duniyar Musulunci.

Allah yasa gwamnati ta amsa wannan kira na al'umma. Allah ya shirye mu. Amiiiin

Idan kana son gaskiya ka saurari dukkan karatun Malam Abdul Jabbar Kabara ko ka kirawo Malam Madatai ya fada maka rubutu...
06/07/2025

Idan kana son gaskiya ka saurari dukkan karatun Malam Abdul Jabbar Kabara ko ka kirawo Malam Madatai ya fada maka rubutun da ya yiwa Abdul Jabbar ba. Kafin ka yanke hukunci.

Na kare mutunci Farfesa Ibrahim Maqary da yawa don gaskiya, Amma idan kayi kuskure dole mu fada maka.
...Inji malamin musulunci mabiyin Tijjaniya Sheikh Ahmed Abdul Fath Yola

06/07/2025

Ka saurari abu daya 1 bisa 100 ka fahimci abu 1 bisa 4 kuma kayi hukumci a kan 100 bisa 100 wannan rashin adalci ne gaskiya.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fityanul Islam Of Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share