Ilimin Fiqhu da tasawwuf. Daga Malaman Addini na Gaskiya

  • Home
  • Ilimin Fiqhu da tasawwuf. Daga Malaman Addini na Gaskiya

Ilimin Fiqhu da tasawwuf. Daga Malaman Addini na Gaskiya Ilimin fiqhu da tasawwuf. Wannan shafi ne. Wanda akayi shi Don kawo muna ilmoma Daban Daban.

Riko da Sunnah Tafarkin Manzon Tsira da Magabata Nagari shine Dacewar Rayuwar Duniya Lahira.

MAFI KYAWUN ABUBUWAN DA AKA TAƁA FAƊA GAME DA MACE(Ku Kwantar Da Hankali Ku Karanta Akwai Darasi)1. Kada ka danne mace, ...
22/06/2025

MAFI KYAWUN ABUBUWAN DA AKA TAƁA FAƊA GAME DA MACE

(Ku Kwantar Da Hankali Ku Karanta Akwai Darasi)

1. Kada ka danne mace, domin fushinta na iya zama mai lalata rai!

2. Mace k**ar ciyawa ce mai laushi – tana lankwasawa ga iska mai laushi, amma ba ta karyewa a gaban hadari!

3. Idan kana son ka samu soyayyar mace, ka kula da ita. Idan kana so ta zauna da kai har abada, ka girmama ta. Mace abu ne mai sauƙi ga wanda ya ƙaunace ta da gaske!

4. Ƙoƙarin fahimtar mace mai fushi, k**ar karanta jarida ne a cikin guguwar iska – ka rungume ta kawai, zata natsu!

5. Namiji wanda ba ya gafarta wa ƙaramin kuskuren mace, ba zai taɓa jin daɗin manyan halayenta ba!

6. Mace tana so ta rayu a ƙarƙashin mutunci da kariyar namiji, ba a ƙarƙashin zaluncinsa ba!

7. Ko da mace ta girma, za ta ci gaba da kasancewa k**ar yaro – ta farin ciki da kulawa, ta kuka da wulaƙanci!

8. A cikin al’ummarmu, idan an haifi ɗa namiji, ana ɗaukar hakan a matsayin fata mai kyau; idan mace ce – ana ɗauka a matsayin faɗuwa, duk da cewa burin kowanne namiji ita ce mace!

9. Idan tunani da basirar mace s**a mutu, to hankalin gaba ɗaya al’umma ya mutu!

10. Idan ka ƙaunaci mace saboda kyawunta kawai, ba ƙauna ba ce. Amma idan ka ƙaunace ta duk da laifuffukanta, to haƙiƙanin soyayya kenan!

11. Ya ke Mace, ki zama k**ar Sallah – ba wanda ke kusantarki sai wanda ya tsarkaka!

12. Namiji na zaton mace na son mai kuɗi, ko mai kyau ko mai suna, amma gaskiyar ita ce: ta na son wanda zai zama mata ɗan’uwanta, abokinta, kariyarta kuma ya girmama hankalinta da mutuncinta.

13. Namiji ba zai taɓa lashe zuciyar mace ba, sai idan mace ta yarda da hakan!

14. An halicci mace domin a ƙaunace ta, ba wai domin a shige cikin sirrinta da bincike ba!

15. Mace tagari, ta fi ma namiji ido da hannu – ta fi komai alkhairi!

16. Mace na ƙaunar namijin da zai sanya ta sake jin ta tamkar yarinya – da dariya, da wasa da farin ciki.

17. Namiji yana shan ƙauna daga shayarwar mace, haka kuma zuciyar mace tana bugawa ne saboda kulawar

20/06/2025

Can a woman satisfy her husband 100%?

Wani lokaci mace tana jin k**ar idan ta biya wa mijinta bukatu, yi masa girki kala-kala, gyara jiki, , ta tsaftace, girmamawa, ladabj biyayya, kwantar da kai… to zata iya gamsar da shi shalelen 100%.
Sai dai gaskiya daya ce
Mace ba za ta iya cika dukkan burin mijinta ba, k**ar yadda shima ba zai iya cika nataba.

Why?
Saboda dan Adam bashi da iyaka a bukata.
Yau yana son shiru, gobe yana son hira.
Yau yana son tuwo, gobe yana son noodles.
Yau yana so ki zauna da shi sosai, gobe yana buƙatar sarari.
Yau yana so ki yi masa magana da tausayi, gobe yana fushi saboda wani abu da ba ki yi ba.
Zuciyar mutum tana canzawa. Rayuwa tana da nauyi.

To me mace zata iya yi?
– Ki yi niyyar kyautatawa saboda Allah, ba don yawan yabo ba.
– Ki fahimci cewa mijinki ba kullum yana buƙatar abu iri ɗaya ba, yau soyayya, gobe space.
– Ki gina kawanki da basira ki dinga karanta sauyin yanayinsa.
– Ki yawaita addu’a sosai. Saboda ko kina da niyyar gamsar da shi, idan Allah bai sa ki gane hanyar ba, zai zama k**ar ba kya yi.

Mace mai basira ba wadda ta iya komai bace...
Ita ce wadda ta san iyakokinta, amma tana kokari da zuciya daya.
Ita ce wadda ta mayar da gida masaukin salama, ko da mijin yana da tabo.

Shin zai yiwu ki cika shi 100%?
A'a. But you can make him FEEL like he's 100% loved, 100% respected, 100% at peace.
Kuma hakan yana da girma fiye da k**alalliyar mace.

Kuma ku mazan…
Ku fahimci cewa mata na kokari. Idan tana da himma, tana ƙoƙari, tana daraja ka, to kada ka dinga ganin ƙurucinta ko kuskurenta a matsayin gazawa.
Girmama ƙoƙari shine soyayya.

A ƙarshe
You can't be a perfect wife.
But you can be a real, intentional, prayerful woman, and that is even more powerful.


HIJABI QUEENS.

KAFIN KI YI AURE...(Karanta A Nutse, Za Ki Ƙaru)Ki san halin mutumin da k**e shirin aura.Idan rayuwarsa tana tafiya ne b...
20/06/2025

KAFIN KI YI AURE...
(Karanta A Nutse, Za Ki Ƙaru)

Ki san halin mutumin da k**e shirin aura.
Idan rayuwarsa tana tafiya ne bisa tafarkin Ubangiji, to ki dogara da Allah ki ci gaba.

Ki bayyana masa manufofinki da burinki — ki zaɓi wanda zuciyarsa na ɗauke da damuwar al’umma, da kishin Musulunci da wa’azin da’awah.

Wataƙila tafiyarku ba iri ɗaya ba ce — idan rayuwar ku tana tafiya a mabambantan hanyoyi, ba za ku haɗu ba.

Ba laifi ba ne ki jira shekara guda ko biyar ko goma, amma ki guji yin aure domin kawai ki ce kin yi aure!

Kada ki yi aure saboda kawai kin girma ko kuma wai lokaci yana tafiya, lokaci zai wuce ko kin yi aure ko baki yi ba.

Kada ki yi aure saboda kawai yawan maganganun mutane — domin su ba za su daina magana ba sai dai ki samu fikafikai ki tashi sama.

Ki zaɓi wanda ya dace da halayyarki, wanda zuciyarki ke kwanciya da shi, wanda idanunki ke hutawa da ganinsa, wanda zai karɓi burinki da tafiyarki.

Ki zaɓi wanda k**e jin k**ar kuna da wata tsohuwar zumunci tun daga duniyar aljanu kafin ku zo duniya, wanda k**e ganin kanki cikinsa ko wani ɓangare na kanki yana cikinsa. Wanda idan kina tare da shi, zaki iya nuna raunin ki ba tare da jin kunya ba, zaki iya bayyanar da duk wasu lahani na kanki ba tare da jin nauyi ba.

Ba dole ne ku zama daidai ba, amma ku yi k**a da juna, domin shi rabinki ne da zai cike giɓinki, ba madubinki da zai nuna miki kanki ba.

Ki faɗa masa cewa:
Ke k**ar Asiya ce wajen sadaukarwa,
Kamar Khadija ce wajen ƙarfi da juriya,
Kamar Aisha ce wajen soyayya da kishi,
Kamar Maryam ce wajen ibada.
Kuma a fahimtarki ta soyayya — alheri a cikin gyara da nasiha ne.

Ki sanar da shi ke ba cikakkiya bace — ba kya buƙatar cikakken mutum, sai dai wanda shi ne naki.

Ba lallai ne ya zama mai kyau ko mai barkwanci ba, abin da yafi muhimmanci shi ne: ki gan shi da idon ƙaunarki k**ar yadda k**e so.

Ki nemi rabinki na ruhi (twin soul) — idan kin same shi, to ki yi aure da yardar Allah.

Amma in har ba ki gan shi ba tukuna — to ki cigaba da ray

YAN UWA MATA GA TSARABA...!!!Haqqin miji a kan matarsa yana da yawa cikin addinin Musulunci, kuma yana taka muhimmiyar r...
03/06/2025

YAN UWA MATA GA TSARABA...!!!

Haqqin miji a kan matarsa yana da yawa cikin addinin Musulunci, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaito a cikin aure. Ga wasu daga cikin manyan hakkokin da miji ke da su akan matarsa:

1. Bin Umarshi (Ta’a)

Matar dole ne ta bi mijinta cikin halal. Wannan na nufin ta yi masa biyayya a cikin dukkan abubuwan da ba su sabawa shari’a ba. Annabi (SAW) ya ce:

> "Da zan umurci wani ya yi sujada ga wani, da na umurci mace ta yi sujada ga mijinta saboda girman hakkinsa a kanta."
(Tirmidhi: 1159)

2. Kare Sirrin Gida

Matar na da alhakin kiyaye sirrin mijinta da gidansu, musamman dangane da abubuwan da ke tsakanin su biyu a sirrance.

3. Rashin fita ba tare da izini ba

Ba ya halatta mace ta fita daga gidan mijinta ba tare da izninsa ba, sai da uzuri na shari’a ko matsanancin hali.

4. Kare Kanta da Dukiyarsa

Matar na da alhakin kare mutuncinta da dukiyar mijinta. Kada ta yi zina, kuma kada ta kashe ko bata dukiyarsa ba tare da izninsa ba.

5. Kyautatawa Miji

Addini ya karfafa cewa mace ta kasance mai nuna soyayya, ladabi da saukin hali ga mijinta. Wannan yana kara dankon soyayya da zaman lafiya.

6. Kulawa da Gidan Miji

Matar tana da alhakin gudanar da gida: tsafta, kula da abinci, da kula da 'ya'ya (idan akwai).

7. Cikakken Halaccin Jima’i

Idan miji yana da bukata (ba tare da cuta ko uzuri ba), mace dole ne ta amsa kiran mijinta domin jima’i. Wannan wani muhimmin haqqi ne da Musulunci ya bayyana.

02/06/2025

MATSALOLIN MU A FILI SUKE

1. Muna aure ba tare da soyyayya ba.

2. Muna haihuwa ba tare da yin tarbiyya ba.

3. Muna salla ba tare da tsaron Allah ba.

4. Muna koyan ilmi ba tare da aiki ba.

5. Muna magana ba tare da gaskiya ba.

6. Muna daukan alƙawari ba tare da cikawa ba.

7. Muna karɓar amana ba tare da kulawa ba.

8. Muna son kuɗi ba tare da Sana'a ba.

9. Muna son Annabi (SAW) ba tare da bin koyarwar sa ba.

10. Muna son Aljannah ba tare da aiki ba.

11. Muna son a amsa mana addu'a ba tare da cin halal ba.

12. Gamu da bala'in son duniya da ƙin mutuwa.

Mafita kawai mu tuba mu gyara, muce Allah mun tuba ka yafe mu.

01/06/2025

Wata matace kullum sai mijinta yayi mata kyautar kudi, watarana 500, watarana 200 watarana Kuma 1K.

Ita Kuma kullum sai tayi Sallah walaha domin Allah ya kara masa budi.

Watarana ta tafi anguwa sai ya tsara yayi mata surprised, dama ya sayi sabbin kujerun daki, bayan ta tafi anguwa sai yasa aka kawo aka cire nata na dakin sai aka saka sabbi, lokacin da zata dawo sai ta wuce ta bawa Baban mijinta wasu kudi da mijinta yake bata take tarawa, Wanda shi be Sani ba, shi a tunaninsa tana kashe kudin, Ashe kudin yakai mataki me yawa 86K, haka ta bawa mahaifinsa 25K, sai ta biya ta sayawa mijinta turare, singlets, boxers, Mai da sabulu da Omo, Sannan Kuma Ashe kudin data bawa Baban SA sai tace Inji mijinta, haka Baban SA ya kirashi yayita godiya tare da masa Addu'oi masu kyau, to bayan ta dawo sai ta shiga daki harta canza kayan jikinta bata Kula da surprised da yayi mata ba!

Sanda tazo parlour ta zauna sai tagani shikuma Yana ban daki, hakan ta shiga bandaki a guje cikin mamaki da godiya gareshi, Shima yayita gode mata bayan ta bashi labari.

Dalilin Baku labarin shine ya samu kyautar kujerar Makkah ne guda biyu, shine yake tambaya, waye ya k**ata ya bawa mahaifinsa kokuma matarsa sai nace masa mahaifi shine ya deserving, Amma a bisa yadda kuke rayuwa da ita cikin Amana da soyayya tare da tausayi, tabbas ta deserving, sai nace masa da kana da kudi sai ka biyawa mahaifin naka tun Shima shekaru sunja sai ku tafi tare dukkan ku uku, Amma da mahaifiyarka tana raye to dole dukkansu zasu hakura sai ka kaita first.

Yanzu dai Masha Allah sun tafi dukkansu uku, ya biyama mahaifinsa kudin hajjin, sun tafi tare..

Abinda nakeso nace shine, idan Allah ya baka mace me tunani da sanin ya k**ata, ma'ana me hangen nesa, to tabbas Koda wata ta baka sha'awa a suffance, wallahi idan ka tuna girman darajar matar taka zakaga wannan kyan suffar ba komai bane, Allah yasada mu da mataye nagari masu Addini.

Bilal Omar Baba Gombe ✍️

ZUMUNCI" ```Yan uwa murike zumunchi domin abun alkhairi ne, anaso kajewa wanda ya kaurace maka domin shi zumunchi ba bik...
30/05/2025

ZUMUNCI

" ```Yan uwa murike zumunchi domin abun alkhairi ne, anaso kajewa wanda ya kaurace maka domin shi zumunchi ba biki bane b***e kace sai amma zakayi, duk wanda kaga yana wasa dashi ka bashi shawara domin yayi raguwar da bara, mara zumunchi ko guri yazo Allah ya na dauke rahama a gurin".

*Ya ubangiji ka kara san zumunchi da riko dashi dan Allah*

National President POSDAN```

Idan Allah ya baka hankali, ya baka fahimta, sannan ya baka ikon kiyaye harshenka wajen cin naman bayinsa haqiqa kayi ba...
29/05/2025

Idan Allah ya baka hankali, ya baka fahimta, sannan ya baka ikon kiyaye harshenka wajen cin naman bayinsa haqiqa kayi babban rabo a irin wannan zamanin namu!

Don haka ayi karatu mai zurfi domin a samu fahimta na kwarai sannan abi 'ka'ida.

Allah yasa mu dace

28/05/2025

🌤️ Azkar Lokacin Tashi Daga Barci

1. Alhamdu lillahilladhi ahyana ba’da ma amatana wa ilaihin-nushur.
Ma’ana: Duk godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya rayar da mu bayan Ya kashe mu (da barci), kuma zuwa gare Shi ne dawowa.

2. La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa huwa ‘ala kulli shay’in qadeer. Subhanallah, walhamdulillah, wa la ilaha illallahu, wallahu akbar. Wala hawla wala quwwata illa billahil ‘Aliyyil ‘Azeem.

Ma’ana: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, babu abokin tarayya gare Shi. Mulki na Shi ne, godiya ta tabbata gare Shi, kuma Shi ne mai iko akan komai. Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma. Babu ƙarfin canji ko ƙarfi sai da Allah.

3. Alhamdu lillahilladhi radda ‘alayya roohi, wa ‘afani fi jasadi, wa adhina li bidhikrih.
Ma’ana: Duk godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya mayar min da raina (daga barci), Ya bani lafiya a jikina, kuma Ya bani dama in ambace Shi.

✅ Shawara: Idan ka tashi daga barci, ka fara da waɗannan Azkar kafin kayi wani abu, domin suna kawo albarka, kariya da ƙarin kusanci da Allah.

📿 Zaka iya haɗa da sauran Azkar na safe k**ar:

Ayatul Kursiyyu

Suratul Ikhlas, Falaq, da Nas (3x kowanne)

Addu’ar asuba da salati ga Annabi (SAW)

LABARIN WANI MA'ABOCIN HIKIMA...Me yasa namiji yake ganin matarsa bata da kyau fiye da sauran mata?!Ɗaya daga cikin Maza...
28/05/2025

LABARIN WANI MA'ABOCIN HIKIMA...

Me yasa namiji yake ganin matarsa bata da kyau fiye da sauran mata?!

Ɗaya daga cikin Mazaje ya je wurin wani malamin addini da ya shahara da hikima da gogewa, yana ƙorafi yana gaya masa:

Lokacin da nake sha'awar matata, ita ce a ra'ayi na k**ar Allah bai halicci wata k**ar ta ba a duniya..!
Kuma da na yi aure, na ga mutane da yawa k**ar ta.
Kuma da na aure ta, na ga wasu kyawawa da yawa.
Lokacin da mukayi aure shekaru kaɗan...
Na ga duk mata sun fi matata kyau.

Mai Hikimar yace:
Shin in gaya maka abin da ya fi wannan munin muni?
Sai mutumin yace: Eh!
Sai mai hikima ya ce:
Idan da ka auri duk matan duniya, za ka ga ɓatattun karnuka a t**i sun fi duk matan talikan zama kyawawa.

Sai mutumin yace:
Me yasa kake faɗin haka?
Sai mai Hikimar ya ce:
Domin matsalar ba daga matarka take ba...
Matsalar ita ce; idan mutum ya kasance yana da zuciyar kwaɗayi, da karkatacciyar idaniyar gani, da rashin kunya ga Allah, to babu abin da zai cika idanuwansa sai dai ƙurar ƙabarinsa.

Haba malam! Matsalar ku ita ce, ƙin rufe ido ga abin da Allah ya haramta.
Shin kana son abinda zai dawo mata da zamaninta, k**ar matan da s**a fi kowa kyau a duniya?

Sai mutumin yace: Eh..
Mai hikima ya ce:
Ka rufe ido. Maɗaukakin Sarki ya ce: {Ka ce wa muminai su rufe ido, su tsare farjojinsu, da kyautatawa ga abin da suke aikatawa}.

Abin da ba a hannunka ba, za ka ga nai mafi kyau, duk abin da ka yi. Kuma idan ka samu, zai zama al'ada a idanunka.

Ka wadatu da abin da kake da shi kada ka kasance mai son kai. Domin za ka ci gaba da haske da kyawo da jin daɗin duniya har sai an kwantar da kai a cikin ƙabarinka.

Akwai wani abu mafi kyau da ban mamaki fiye da wannan duka. Bautawa Allah da aikata ayyuka na gari. Wannan wani abin jin daɗi ne da waɗanda s**a rayu saboda shi kaɗai s**a sani.

Kuma kar ka manta da addu'a Allah Ya ƙara Ƙawata matarka a idonka Ya kuma saka maka soyaya

ZIKIRAI GUDA BAKWAI MAFI TSADA A RAYUWAR MUSULMI1.MAFIFICIN AMBATON ALLAH"Laa ilaha illallaahu wahdahu la shariyka lahu ...
26/05/2025

ZIKIRAI GUDA BAKWAI MAFI TSADA A RAYUWAR MUSULMI
1.MAFIFICIN AMBATON ALLAH
"Laa ilaha illallaahu wahdahu la shariyka lahu lahul-Hamdu wahuwa ala kulli shay'en qadir"
2.MAFIFICIN TASBIHI
"Subhanallahi wabihamdihi adadi khalQihi warida Nafsihi wazinata arshihi wa midada kalimatihi"
3.MAFIFICIYAR ADDU'A
"Rabbana atina fiy-dduniya hassanataw-wafil akhirati hasanah waQina azabar Nar"
4.MAFIFICIN ISTIGFARI
"Allahumma anta rabbiy la ilaha illa anta kalaQ-taniy, wa'ana abduka, wa'ana ala aHdika, wa-wa' adika matsa-'daat, a-uzubika min sharri ma sana'ata, abu ula-ika bini'-imatika alayya, wa-abu'u bizambiy, fagfirliy fa-innahu la yagfiruz-Zunubu illa ant"
5.MAFIFICIN NEMAN KARIYA DA TSARI
"Bismillaahilladziy la yadurru ma-asmihi shay'un fiyl-ardhi wala fiys-sama' , wahuwassamiy'un alaiym"
6.MAFIFICIN ZIKIRIN NEMAN YAYE DANUWA
"La ilaHa illa anta subhanaka inniy kuntu minaz zalimiym"
7.MAFI ZIKIRIN DOGARO GA ALLAH DA SALLAMAWA AGARESHI. SHINE
"La haula wala Quwwata illa billaahil aliyyil azim"
ALLAH YABAMU IKON DAUWAMA AKAN YAWAITA AMBATONSA AKOWANI LAKACI ALBARKAN ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA

25/05/2025

Muhimman Shawarwari 20 Ga Mai Aure Da Mai Neman Aure:👇🏿

1. Idan kai tsoho ne, kar ka auri matashiya, saboda ba za ka Iya biya mata buƙatar sha'awa ba, dalilin haka za ta ƙosa da kai, kuma ƙarshenta ta shiga neman wasu mazan kuma ba yadda ka iya, sai dai ka zamo mara kishi (dayyus), ka yi asarar mutuncinka, rayuwarka ta yi ƙunci, lahirarka ta lalace. Sannan za ka rayu cikin cutuwa, saboda za ka fuskanci gatsali da maganganun banza daga gare ta, da mu'amala mara daɗi.

ولا تنكحن إن كنت شيخا فتية
تعش في ضرار العيش أو ترض بالردي

2. Kar ka auri wadda ta fi ka matsayi da ɗaukaka, idan ka aura za ka samu ƙuncin zama tare da ita, saboda za ta dinga maka alfahari, kuma ba za ta damu da kai ba saboda ƙasƙancinka, da tawayarka a idonta, kai za ka zamo kana rayuwa ƙarƙashin dokokinta, ba ita ba.

ولا تنكحن من نسم فوقك رتبة
تكن أبدا في حكمها في تنكد

3. Kada kwaɗayin dukiyar mace da abin hannunta ya sa kana talaka ka je ka auro mai kuɗi, lallai idan ka auro mai kuɗi alhalin kana talaka za ka ƙasƙanta saboda rashin fifikonka a kanta, da kasa biya mata buƙatu da za ka yi, da buƙatuwarka ga dukiyarta, gwargwadon gajartan hanunka (wajen mata hidima), gwargwadon tsawon harshenta (wajen jefa maka maganganun rashin kyautawa), kuma gwargwadon yadda za ta buwaye ka, ta raina ka, ta ɗamfaru da ƴan'uwanta ta watsar da kai, za ka ƙasƙanta a gabanta irin ƙasƙantar da manemi yake yi a gaban wanda ake nema wajensa, ga tsawon lokaci (da za ku rayu) da yawan gori, sai lamari ya cakuɗe maka, ka ƙare a damuwa.

ولا ترغبن في مالها وأثاثها
إذا كنت ذا فقر تُذَلُّ وتضهدِ

4. Kar ka yarda ka yi aure ka zauna a gidan matarka, musamman tare da danginta, saboda za ka ji maganganu mara sa daɗi daga wajensu, na daga aibatawa da zagi da gori da cutarwa, saboda izzarta da ƙasƙancinka, da wadatarta da talaucinka, da ɗamfaruwarta da danginta a yayin da kai kuma kake bare, za ta dinga maka girman kai da nuna falala/fifiko, a yayin da kai kuma kake kwantar da kai kana ƙasƙanta. To duk wanda wannan ya zama halinsa, makomarsa a aure ta zama haka, babu alheri a cikin rayuwarsa kuma ba shi ba jin daɗi.

ولا تسكنن في دارها عند أهلها
تُسَمَّع إذا أنواع من متعدد
فلا خير فيمن كان في فضل عرسه
يروح على هون إليها ويغتدي

5. Idan matarka ta yi sadaka ko ta kyautar da ɗan abin da bai kai ya kawo ba daga cikin abin da ka kawo, kar ka mata inkarin hakan kana mai nuna rowa da kwaɗayi da son abinka, abin da ya dace da kai a irin wannan halin shi ne ka kau da kai ka zamo mai kyauta da karamci, idan ka yi haka za ka samu lada, kuma za ka samu daɗin zama da ƙarin ƙauna tsakaninka da iyalinka, Annabi (SAW) ya ce: "Idan mace ta ciyar daga dukiyar mijinta ba tare da ɓarna ba, tana da ladar ciyarwarta, mijinta yana da ladar nemowa, mai ajiya ma yana da ladansa, ba tare da wani ya tauye ladan wani ba daga cikinsu". (Bukhari:1359, Muslim: 1024).

ولا تنكرن بَذْلَ اليسير تَنَكُّدًا
وسامح تنل أجرا وحسن التودد

6. Kada ka zama mai binciken ƙwaƙwaf a kan komai, saboda ƙoƙarin tona komai ƙeƙe da ƙeƙe yana daga cikin ɗabi'un marowata da masu son kai. Sannan ka rintsa idonka ka basar daga kasawar matarka idan ba a kan abin da yake na zargi ba a shari'ance, saboda dagewa wajen kallon aibi shi ma aibi ne, shi ya sa abin da ya fi shi ne kawar da kai, wani mai hikima yana cewa: "Mutum mai hankali shi ne mai hikima mai kawar da kai".

Amma idan ta aikata abin zargi a shari'a ne to wajibi a yi tanbaya da bincike, saboda ana kawar da kai ne a harkar rayuwa kawai ko wajen rashin cika wani ladabi cikin ladubban zamantakewa, amma cikin lamarin addini da kare mutunci, ba kyau a dinga ɗauke kai daga kuskure, musamman a kan wajibai.

ولا تسألن عما عهدت وغُضَّ عن
عَوَارٍ اذا لم يذمم الشرع ترشد

7. Ka sani da kyau cewa mata kayan amana ne kuma tamkar k**ammun yaƙi a hannunka, saboda haka ka yi riƙo da wasiyyar Annabi (SAW) da ya ce a riƙe su da alheri.

وكن حافظا أن النساء ودائع
عَوَانٌ لدينا احفظ وصية مرشد

8. Kar ka yawaita s**a da ƙorafi a kan matarka, idan ka yi haka za ka sa a dinga tuhumar ta (ka ɓata mata suna) saboda yawan inkarinka a gare ta, har mutane su yanke hukuncin ita mai munanan ɗabi'u ce. Sannan kar ka zama daga wani ya yi laifi cikin ƴaƴanka ko matanka ka hau shi da duka, lallai rashin duka ya fi tabbatar da ƙauna, ka yi koyi da Annabi (SAW) da Nana A'isha (R.A) take cewa: "Bai taɓa duka da hannunsa ba sai a wajen jihadi" (Bukhari:3367, Muslim: 1814).

ولا تكثر الانكار تُرْمَ بتهمة
ولا ترفعن السوط عن كل معتد

9. Kar ka yi ƙoƙarin miƙar da karkatar matarka ka ce sai ta zama ɗari bisa ɗari, saboda misalinta wajen karkacewa k**ar ƙashin haƙarƙari ne, saboda hadisin da ya zo cikin Bukhari:3153 da Muslim: 1090, Annabi (SAW) ya ce: "An halicci mace daga ƙashin haƙarƙari, kuma mafi karkacewar haƙarƙari shi ne na can samansa, idan ka ce za ka tsayar da shi za ka karya shi, idan ka bar shi kuma zai zauna a karkace.

ولا تطمعن في أن تقيم اعوجاجها
فما هي إلا مثل ضلع مردد

9. Kar ka yi ƙoƙarin miƙar da karkatar matarka ka ce sai ta zama ɗari bisa ɗari, saboda misalinta wajen karkacewa k**ar ƙashin haƙarƙari ne, saboda hadisin da ya zo cikin Bukhari:3153 da Muslim: 1090, Annabi (SAW) ya ce: "An halicci mace daga ƙashin haƙarƙari, kuma mafi karkacewar haƙarƙari shi ne na can samansa, idan ka ce za ka tsayar da shi za ka karya shi, idan ka bar shi kuma zai zauna a karkace.

ولا تطمعن في أن تقيم اعوجاجها
فما هي إلا مثل ضلع مردد

10. Kar ka zauna ko kai kaɗai ko da iyalinka a gida/ɗakin da masu wucewa kan hanya za su dinga gano ku, saboda hakan zai iya haifar da tuhuma, a yi zaton kun yi hakan ne don ku dinga leƙa mutane, ko kuma wani yana iya ganin matarka dalilin hakan, kuma ƙarshe abu ya haifar da fitina.

وسكنى الفتى في غرفة فوق سِكَّةٍ
تؤول إلى تهمى البريء المشدِّدِ

11. Ka kiyayi auren kyakkyawar mace daga gidan da ba su da kamun kai ko da kuwa ita mai kamun kan ce, saboda da da ƙyar ne ka ga halin gidansu bai rinjaye ta ba.

وإياك يا هذا وروضة دمنة
سترجع عن قرب الى أصلها الردي

12. Kar ka yi aure idan kana fama da talauci in ba don larura ba, k**ar tsoron faɗawa zina, idan ka samu kanka a wannan yanayin to ka nemi macen ƙwarai daga gidan talakawa, wadda ka san za ta dinga girmama kaɗan ɗin da kake ba ta, sannan kuma ka cike gurbin talauci naka da kyawawan ɗabi'u da sakin fuska da daɗin zama. Idan ba ka yi auren ba ka nemi kariya ta hanyar yawaita azumi, saboda wasiyyar Annabi (SAW).

((مَنِ اسْتَطاعَ الباءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فإنَّه أغَضُّ لِلْبَصَرِ، وأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، ومَن لَمْ يَسْتَطِعْ فَعليه بالصَّوْمِ، فإنَّه له وِجاءٌ.)) البخاري (١٩٠٥) مسلم (١٤٠٠)

((وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّى يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ)) نور: ٣٣

ولا تنكحن في الفقر الا ضرروة
وَلُذْ بوجاء الصوم تَهْدِ وتهتدي

13. Ka san cewa mata abokan wasanmu ne, da muke raha da su muke nutsuwa izuwa gare su, kuma ranmu yake daɗi idan muka gan su, saboda haka ka kyautata wajen nema ka samu mai kyawawan halaye, mai kyakkyawan asali, don ka samu cikar buri.

وكن عالما أن النسا لُقَبٌ لنا
فَحَسِّنْ اذا مهما استطعت وجَوِّدِ

14. Ka san cewa mafi alherin mace ita ce wadda idan mijinta ya kalle ta yake farin ciki, ida ba ya nan ta tsare gidansa da mutuncinta, mai gajeren harshe, ba ta magana sai mai amfani, ba ta yawon gidajen mutane da kasuwanni, mai gajeren gani, ba ta sha'awar kowa sai mijinta, ya zo cikin sahihu Muslim:1467, Annabi (SAW) ya ce: "mafi girman jin daɗin duniya shi ne mace ta gari".

وخير النسا من سرت الزوج منظرا
ومن حفظته في مغيب ومشهد
قصيرة ألفاظ قصيرة بيتها
قصيرة طرف العين عن كل أبعد

15,16,17,18. Ka nemi budurwa (mai ƙananan shekaru), ma'abociyar addini, ma'abociyar asali, mai son ka a matsayin mijinta, kuma mai haihuwa. Idan kana neman rabauta da ƴaƴa na gari, ka zaɓa musu uwa mai asali nagari, saboda idan mutum ya yi aure daga tushe mai kyau, ɗan zai zo yana k**anceceniya da jinin mahaifiyarsa a ɗabi'u da ayyuka.

عليك بذات الدين تظفر بالمنى
الودود الولود الأصل ذات التعبد
حسيبة أصل من كرام تفز إذًا
بولد كرام والبَكَارةَ فاقصد

Ga wasiyyoyin Manzon Allah (SAW) da s**a zo a kan haka:

١. ((تُنْكَحُ المَرْأَةُ لأرْبَعٍ: لِمالِها، ولِحَسَبِها، وجَمالِها، ولِدِينِها، فاظْفَرْ بذاتِ الدِّينِ، تَرِبَتْ يَداكَ)).
البخاري (٥٠٩٠)، مسلم (١٤٦٦)

٢. ((تزوَّجو الولودَ الودودَ فإنِّي مُكاثرٌ بِكُمُ الأممَ يومَ القيامة)) أبو داود (٢٠٥٠)

٣. ((عليكُم بالأبكارِ فإنَّهنَّ أعذَبُ أفواهًا وأنتَقُ أرحامًا وأرضى باليَسيرِ)) ابن ماجه (١٥٢٠)

19. Ka wadatu da mace ɗaya idan ka samu kamewa da ita, saboda hakan zai fi maka sauƙin yin adalci da kuɓuta daga zalunci, idan kuma ka buƙaci ƙari kana da damar yin har huɗu, kar ka ƙara a kan haka, (saboda shi ne iyakar shari'a).

وواحدة أدنى من العدل فاقتنع
وان شئت فابلغ أربعالا تُزَيِّدِ

20. Ka sani cewa duk wanda tsoron Allansa ya sa ya kame daga lalata da zuri'ar wasu, to shi ma za a kare masa nasa zuri'ar daga zina.

ومن عَفَّ تَقْوًى عن محارم غيره
يَعَِّف اهْلُهُ حَقًّا وان يَزْنِ يُفْسِدِ

Asalin karatun yana cikin littafin تحفة الأحباب شرح نظم الآداب, shafi na 108-116: فصل في آداب النكاح. Allah ya sa mu dace.

bahaushe

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ilimin Fiqhu da tasawwuf. Daga Malaman Addini na Gaskiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ilimin Fiqhu da tasawwuf. Daga Malaman Addini na Gaskiya:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share