Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba

Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba, Digital creator, Masjid Aba Huraira, Ungwan Sarkin Fada, Wamba.

Ustadh Muhammad Tahir  Almisry (Abu humaid) keana . Allah yafimu yabawa
01/04/2025

Ustadh Muhammad Tahir Almisry (Abu humaid) keana . Allah yafimu yabawa

18/11/2024

Raddi ga Prof. Maqari a kan Saukowar Allah zuwa Sama ta Duniya

Dazu dan'uwa Malam Nura ya turo min takaitaccen faifan bidiyo na Prof. Maqari, wanda a cikinsa yake inkarin saukowar Allah zuwa sama ta Duniya, yana tallata Mazhabarsu ta Tawilin Nassoshin Alkur'ani da Sunna.

To, ganin yadda ake ta yada bidiyon, ana fitinar mutane a Addininsu da shi, ana jefa musu shubuha game da Siffar Allah da girmansa, sai Malam Nura ya nemi a warware wa mutane shubuhohin da shi Maqari ya yada.

To, farko dai Hadisin saukowar Allah Hadisi ne Mutawatiri, wato wanda babu shakka wajen tabbatuwar Annabi (saw) ya fade shi. Saboda Hadisi ne da Sahabbai 39 s**a ruwaito shi, kuma cikin Malaman Hadisi Abu Zur'ah, Ibnu Hibban, Ibnu Abdulbarr, al-Baihaqiy da al-Zahabiy duk sun tabbatar da cewa Hadisi ne "Mutawatiri".
To irin wannan Hadisi kuwa dalalarsa ma yankakke ne, wato babu kokonto a kan abin da Hadisin yake nuni gare shi. Shi ne abin da ake cewa: (قطعي الثبوت والدلالة).

Ai abu ne da ya tabbata a hankalce; idan Nassi ya zama (قطعي الثبوت) to dole ya zama (قطعي الدلالة). Abin nufi, in dai ya tabbata bisa yakini, babu shakka cikin ingancinsa daga Annabi (saw) to ai kuwa dole abin da Hadisin yake nuni gare shi ya zama tabbas babu shakka ko kokonto a kansa.

Amma abin mamaki, wadannan mutane 'yan bidi'a, wadanda ake kira da sunan "Asha'ira" a yau, sai s**a ce: sun yarda Alkur'ani da Hadisi Mutawatiri sun tabbata babu shakka (قطعي الثبوت), amma ba su yarda abin da yake nuni a kansa tabbatacce ne bisa yakini ba. Don haka Alkur'ani da Hadisi Mutawatiri abin da suke nuni gare shi zato ne (ظني الدلالة).

Wannan shi ne barna mafi girma da aka yi wa Addinin Muslunci, aka zo aka ce: Alkur'ani da Hadisi Mutawatiri zato ne.

Wannan ya sa wadannan mutane suke Tawailin Ayoyi da Hadisai Mutawatirai, b***e Hadisai Ahaad, su zo su juya su, su fassara su bisa ra'ayoyinsu, sabanin zahirin Nassin.
Miye dalilinsu? Shi ne Nassoshin sun saba ma ra'ayoyi da ka'idojinsu na hankali. Don haka asali su hankulansu suke bi, a maimakon su bi Alkur'ani da Sunna.

Wannan shi ne farkon abin da ya raba hanyar 'yan bidi'a, da hanyar Ahlus Sunna. Su kam Alkur'ani da Sunna ne gaba da ra'ayoyinsu da fahimtarsu.

To, Maqari ya fadi wasu shubuhohi, yana tambaya a kansu ta hanyar hikaya, -wai- yake cewa:
"An ce Allah yana saukowa, zuwa sama ta uku ko? a tsakiyan dare... Ai zuwa sama ta daya. Sai su ce: a "Sulusul lailil akheer"".

Sai ya ce:
"Sai su fara tambaya to, wa ya bari a can wajen, a lokacin da ya sauko, wajen ya zama babu shi ne?".
"Kuma "sulusul laili" din wani gari? Tun da "sulusul lailin" daya ne yana canzawa, na wane gari?".
"Sannan da ya sauko, can din sun koma saman shi kenan? Sun zama a saman Allah kenan?".

To ka ga matsalar da Maqari ya samu, shi da sauran 'yan Mazhabarsa ita ce, suna kamanta Allah da mutum ne a kwakwalensu, suna ganin cewa; saukowar Allah irin ta mutum ce. Shi ya sa suke yin irin wadannan tambayoyi.
Mutum ne za ka yi irin wadannan tambayoyi game da saukowarsa ba Allah ba. Saboda a saukowar mutum ne za a samu irin wadannan abubuwa ba na Allah ba. Mutum ne muka san irin saukowarsa, amma saukowar Allah ba mu san yadda take ba, b***e mu yi tunanin za a samu wadannan abubuwa da ya yi tambayoyi a kansu.

Misali: idan an ce: Alhaji Idi yana saukowa a "sulusin" dare na farko, daga beni hawa na 12, zuwa hawa na 2, a nan ne za ka yi wadancan tambayoyi, ka ce: Wa Alhaji Idi ya bari a can hawa na 12, a lokacin da ya sauko, wajen ya zama babu shi ne?
Kuma "sulusul laili" na farkon wani gari ne Alhaji Idi yake saukowa? Tun da "sulusul lailin" na farko daya ne, yana canzawa, to na wane gari ne?
Sannan da Alhaji Idi ya sauko beni hawa na 2, can sauran hawannin sun koma saman shi kenan? Sun zama a saman Alhaji Idi kenan?

To mutum ne za ka yi irin wadannan tambayoyi a kan saukowarsa, ba saukowar Allah ba. Saboda siffofin Allah gaibi ne. Ba mu san yaya yake yinsu ba, kuma bai ba mu labari ba. Kuma shi ba shi da makamanci, b***e mu yi irin tambayoyin da za mu yi a saukowar Alhaji Idi a saukowar Allah! Allah ya ce:
﴿لَیۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَیۡءࣱۖ﴾ [الشورى: ١١]

Saboda haka asali wadannan tambayoyi da Maqari ya yi duka kuskure ne, don ya yi su ne bisa abin da ya zo a tunaninsa cewa: saukowar Allah irin ta halittu ne, don su ne muka san cewa: idan sun sauko daga sama to sun sauko gaba daya, ba su bar sauransu a can ba. Kuma su ne lokaci a wurinsu guda daya ne, idan sun sauko a "sulusin" dare na Nigeria, to a lokacin rana ne, ko safiya a wasu yankuna na duniya. Amma saukowan Allah, ba mu sani ba. Amma dai mun san cewa: Allah mai iko ne a kan komai, babu abin da zai gagare shi. Ma'ana; Allah shi ya halicci lokacin, yana da iko ya sanya sulusin dare da yake saukowa ya zama duka sulusin dare ne a dukkan duniya. Yana da iko a kan haka. Amma yaya yake saukowa, shin idan ya sauko sama ta daya, sama ta biyu har zuwa ta bakwai, da Kursiyyi da al-Arshi duk suna sama da shi kenan?
Sai mu ce mu ba mu sani ba, Allah bai ba mu labari ba. Amma yana da ikon ya sauko sama ta daya, ba tare da sauran sammai sun zama a sama da shi ba. Don shi mai iko ne a kan komai. Kuma shi mai girma ne, duka sammai da kassai da halittu a tafin hanunsa suke.

Wallahi da a ce mutane sun san girman Allah da ba su yi tunanin a saukowar Allah za a samu irin abubuwan da suke gani ana samu a saukowar halittu ba.
﴿وَمَا قَدَرُوا۟ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦ وَٱلۡأَرۡضُ جَمِیعࣰا قَبۡضَتُهُۥ یَوۡمَ ٱلۡقِیَـٰمَةِ وَٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تُ مَطۡوِیَّـٰتُۢ بِیَمِینِهِۦۚ سُبۡحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا یُشۡرِكُونَ ۝٦٧﴾ [الزمر: ٦٧]

Saboda haka duka wadannan shubuhohi ne masu rauni, wadanda Maqari ya dauko daga magabatansa, yake maimaitawa, irin su Raziy, Ibnu Jama'a da sauran Malaman Asha'ira, alhali tun tuni Malaman Sunna sun markade wadannan shubohohi, sun warware su, sun tona asarinsu, s**a nuna yadda s**a kunshi kamanta Allah da mutum.

Sai kuma Maqari ya yi wata magana wacce fadinta kawai ta isa duk mai hankali ya fahimci bacinta. Inda ya nuna cewa: wai daga karni na hudu, har zuwa karnin Ibnu Taimiyya, har wannan zamani, wai Malaman Muslunci Tawili suke yi.
Ma'ana yana nufin, su wadannan Malamai da yake nufi (Malaman Asha'ira), sun saba wa Malaman farko, a karni na daya har zuwa karni na uku. Wato su wadannan Malamai ba su san Tawili ba, su suna aiki da abin da ya zo a cikin Nassi ne. Ma'ana: tun da Allah ya ce yana da fiska, hanu, kuma ya yi Istiwa'i a saman al-Arshi. Annabi (saw) ya ce: Allah yana da kafa, kuma yana saukowa, to suna tabbatar da su a haka ne ba tare da Tawili da canza maganar Allah da Manzonsa ba.
To don Allah, yaya za a yi wadanda s**a sake hanyar Sahabbai, da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'ina, su zama su ne a kan dadai?!
Yaya za a yi wadanda s**a canza maganar Allah da Manzonsa, s**a canza abin da Malaman karni na farko da na biyu da na uku suke kai su zama su ne a kan dadai?!
Wannan ba zai yiwu ba.
Don haka su wadannan Malaman karni na hudu iyo baya - wadanda Maqari yake nufi - sun kirkiri bidi'a, sun zo da sabuwar hanya, wacce ba a santa a karnoni ukun farko ba, alhali su ne karnoni mafi alheri da shiriya kamar yadda Annabi (saw) ya fada.

To don Allah, saba hanyar Malaman karni na daya, na biyu da na uku, abin yabo ne ko abin zargi?!
Amma shi Maqari har cika baki yake yi, wai sai ka samu Malamai dari ko hamsin suna Tawili, kafin ka samu Malami daya da ba ya yi. To ai wannan din ba gwaninta ba ne ya Prof.!
Wannan din abin zargi ne, saba tafarkin Muminan farko ne. Shi ya sa Allah ya zargi wannan Manhaji, inda ya ce:
﴿وَمَن یُشَاقِقِ ٱلرَّسُولَ مِنۢ بَعۡدِ مَا تَبَیَّنَ لَهُ ٱلۡهُدَىٰ وَیَتَّبِعۡ غَیۡرَ سَبِیلِ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ نُوَلِّهِۦ مَا تَوَلَّىٰ وَنُصۡلِهِۦ جَهَنَّمَۖ وَسَاۤءَتۡ مَصِیرًا﴾ [النساء: ١١٥]

Don haka saba tafarkin Malaman karnoni ukun farko abin zargi ne ba abin yabo ba. Saboda saba Ijma'i ne. Imam Abul Hassan al-Ash'ariy ya ce:
"الإجماع الثامن:
وأجمعوا على أنه عز وجل يجيء يوم القيامة والملك صفا صفا، لعرض الأمم وحسابها وعقابها وثوابها...
وأنه عز وجل ينزل إلى السماء الدنيا، كما روي عن النبي صلى الله عليه وسلم...".
رسالة إلى أهل الثغر (ص: ٢٢٧ - ٢٢٩).

Ga shi karara saukowar Allah zuwa sama ta duniya mas'ala ce ta Ijma'i, kamar yadda al-Ash'ariy da kansa ya hakaito.

To miye hukuncin wadanda s**a saba Ijma'i?!

Saboda haka maganganun Prof. Maqari maganganu ne marasa hujja. Kuma shubuhohi don yada barna da bata a cikin al'umma.

A cikin maganarsa ya ayyana ma'anar da ya bayar wa saukowar Allah din, inda ya ce: -wai- abin nufi shi ne rahmar Allah tana kara kusantar bayi!
Ta yaya ya gane wannar ma'ana?
Ma'ana kenan rahmar Allah ba ta kara kusantar bayi sai a wannan lokaci?
Ta yaya ka san haka?
In ka ce daga Hadisin ne, sai mu ce: a'a, Hadisin saukowar Allah da kansa aka ambata ba rahmarsa ba.

Prof. Maqari ya yi ta wasu maganganu wadanda babu hujja a cikinsu ko kadan, sai kame-kame.

Saboda haka Tawilin da Prof. Maqari ya yi wa Hadisin saukowar Allah zuwa sama ta duniya, ya ce: saukowar rahmar Allah ce ba saukowar Allah ba, bidi'a ce da bata mummuna, da canza maganar Annabi (saw) da saba hanyar Muminai, Malaman karnoni ukun farko, masu falala da alheri.

04/08/2024

ZATO NA JAWO ZUNUBI DA NADAMA:

Shari'a ta hana mu jefa zargi a Juna musamman cikin iyali, abokan Hulda da masu yi Maka hidima da sauran makusanta

Yarda da jita jita na haddasa mugun zato, da sa ka tsani mutanen kirki masu son cigaban ka, ko ka rabu da masu tsare maka mutuncin ka

Zato da yawan zargi na sa mutum ya kamu da ƙaunar munafukai maƙiya marasa san zaman lafiyar mu a cikin iyalan mu ko abokan mu ko wurin zaman mu

A rayuwa mubi a hankali wajan hukunta mutane akan zato, mu gujewa zargi don zuciyar mu ta samu natsuwa

Ya Allah ka tsaremu daga mummunan zato ga Junan mu, amin

13/07/2024

YAN UWA MUYI TUNANI DA HANKULAN MU👇
Kowace zanga - zanga daga ta lumana take farawa. Daga nan kuma sai control ya kwace, sai ta koma ta fasa shaguna, sai ta daukar makami, daga nan kuma ba a san inda za ta tsaya ba.

Mu wannan muke tsoro.

Ita zanga - zanga in an san farkonta, to ba a san karshenta ba.

Allah ya mana tsari da fitina.

Ta gefe guda kuma, dole ne shugabanni su yi dukkan abin da ya kamata na kokarin fita daga mawuyacin halin tsadar rayuwa da talakawa suke ciki.

12/07/2024

Maslahar Zanga-zanga

Shi Addinin Muslunci ba komai ba ne illa samar da Maslaha, wato gyara da samun amfani, da kawar da Mafsada, wato barna da cutuwa. Komai na Muslunci ya ginu ne a kan wadannan abubuwa biyu.

Ka dauki tushen Addini, wato Tauhidi, me ya sa ya zama tushen Muslunci? Saboda idan an kadaita Allah da bauta to zuciya za ta gyaru, gabobi za su gyaru, halaye za su gyaru. Sai a samu zaman lafiya, da walwala da amfanar da juna. Amma in kuma aka samu shirka, to akasin haka ne zai faru, zuciya za ta baci, halaye da dabi'u da aiyuka za su gurbace, ba za a ga komai a tsakanin mutane ba sai munanan aiyuka, da rarrabuwar kai, da ta'addanci da zaluntar juna.

Haka idan ka dauki Sallah, Zakka, Azumi, haka Aikin Hajji. Da sauran aiyukan Ibada.

Haka mu'amaloli, na cinikayya, da auratayya, da zamantakewa, duka Shari'a ta zo da hukunce-hukuncensu ne don a samu maslaha a kawar da barba.

Haka Shari'a ta hana alfasha da munkari ne don suna kawo barna, shi ya sa za ka samu barayi da 'yan ta'adda babu aikin alfasha da munkari da ba sa aikatawa. Sun lalata musu zukata sai s**a zama 'yan ta'adda, mabarnata a bayan kasa.

Haka idan ka dawo bangaren Siyasa, Shari'a ta zo da hukunce-hukunce a babin ne don samar da Maslaha da gyara, da kawar da Mafsada da barna. An hana shugabanni zalunci don kada su su lalace, kuma su yi sanadi talakawa ma su lalace. Haka Shari'a ta yi umurni da hakuri a kan zaluncin shugabanni don talakawan su gyaru, kada su lalace. Haka an hana tawaye wa shugabanni don kada su lalace, a samu barna da ta'addanci, na asarar dukiyoyi da rayuka, a samu tashin hankali, a rasa zaman lafiya.

A takaice, Shari'a ta ba ka ma'auni a komai na rayuwarka. Duk abin da za ka yi ka auna Maslaha da gyara da ke cikinsa, da kuma Mafsada da barna da ke cikinsa.

Kuma a lura, ba a aiki da mujarradin zato a wannan babi, dole sai an samu yakinin samuwar Maslaha da rashin barna ko zato mai rinjaye kafin a aikata. Haka duk abin kake da zato mai rinjaye a kan zai haifar da barna to wajibi ne ka nisance shi, b***e idan yakini kake da shi.

Saboda haka ka tsaya ka kalli zanga-zangar da ake kira a yi bisa wannan ma'auni, ka tabbatar ka yi aiki da abin da shi ne Maslaha, shi ne gyara. Ka nisanci duk abin da kake ganin zai kai ga Mafsada da barna.

Allah ya shiryi shugabannin Nigeria, su zama masu adalci, ya ba su tausayin talakawa.

28/06/2024

إن جأني سائل قلت مرحبا
و أفضل الأيام للفتی حين يسأل

08/06/2024

Address

Masjid Aba Huraira, Ungwan Sarkin Fada
Wamba

Opening Hours

Monday 18:25 - 20:00
Wednesday 18:25 - 20:00
Friday 18:25 - 20:00
Sunday 18:25 - 20:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Markazu Abee Huraira Littaalim Wal Irshad Wamba posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share