20/06/2025
Muhimman Wurare 10 da Iran Ta Lalata a Isra’ila Cikin Kwana Bakwai
A cikin makon da ya gabata, dangane da martanin Iran kan hare-haren Isra’ila, rahotanni sun nuna cewa Iran ta kai hari kan wasu mahimman cibiyoyi a faɗin Isra’ila, tana mai haddasa babbar asara ga tattalin arziki, tsaro da ababen more rayuwa. Ga jerin manyan wurare 10 da aka lalata:
1. Ma’aikatar Tsaro ta Isra’ila (Kirya) – Cibiyar tsare-tsaren soja mafi girma a Tel Aviv, wacce ke da matuƙar muhimmanci ga shirye-shiryen yaƙi da tsaron ƙasa.
2. Ofishin Hukumar Leken Asirin Isra’ila na MOSSAD a Herzliya – Wurin da ake zargin yana ɗaya daga cikin cibiyoyin tsara dabarun sirri da ayyukan leƙen asiri na ƙasar.
3. Sansanin Sojin Sama na Nevatim (a Negev) – Muhimmin sansani da ke kula da dabarun sojin sama da ke kudu maso yammacin Isra’ila.
4. Sansanin Sojin Sama na Hatzerim – Daya daga cikin cibiyoyin horar da matukan jiragen yaƙi da sarrafa makaman zamani.
5. Asibitin Soroka da ke Beersheba – Asibitin da ke karɓar dubban mutane a yankin kudu, ya gamu da mummunan hari wanda ya haifar da rugujewar wasu sassa.
6. Matatar Mai ta Haifa – Wurin tace danyen mai wanda ke ciyar da ƙasar da makamashi, ya gamu da hari da ya janyo gobara mai girma.
7. Katafaren Rukunin Shaguna a Kiryat Ekron – Gidauniyar kasuwanci mai ɗauke da shaguna da dama, ta samu munanan lahani.
8. Cibiyar Binciken Kimiyya ta Weizmann – Wata sananniyar cibiyar bincike da kimiyya, musamman a ɓangaren fasaha da makamashi.
9. Ofishin Hada-hadar Hannayen Jari a Ramat Gan – Wurin da ake gudanar da kasuwancin hannayen jari, wanda ya shafe daruruwan kamfanoni da masu zuba jari.
10. Tashar Motocin Sufuri ta Tel Aviv da Tashar Lantarki ta Haifa – Hanyoyin sadarwar cikin gari da samar da wutar lantarki sun gamu da mummunan hari, lamarin da ya janyo tsaiko a harkokin yau da kullum.