27/05/2025
Idan kana son ka zama dalibi mai tarbiya, da ladabi, ka lazimci majalisin wannan malamin.
Domin a gaskiya a nan Nigeria irin su kadan ne! Shehun malamin dan garin Maiduguri ne! Kuma shine ya maye gurbin Sheikh Ja'afar a inda yake tafsirin Alkur'ani mai girma.
Wannan malamin a halin yanzu malami ne a jami'ar Maiduguri, daya kai matakin Prof, kuma tun daga digiri na daya zuwa ta uku, duka yayisu a jami'ar musulunci dake Madinar Annabi Muhammad (Saw)...
Babu shakka ko baka maiduguri kana iya bibiyarsa domin ka amfana sosai, kuma ana sakashi a Sunna Tv, kamar yau talata, da kuma shafukansa...
Dan haka duk wanda yake zama a majalisin sa, zai karbi ruhin ilmi na gaske, hade da tarbiya, da lafiyayyiyar akida, ta tauhidi...
Domin tafiyar su daya, dasu Sheikh Dr. Abubakar birnin Kudu, da Sheikh Prof. Sani R. Lemu, dss
Shine dai Sheikh Prof. Muhammad Alh Abubakar, Hafizahullah. 😍🙏...