09/03/2022
Hukumar tsaro ta DSS ta tsare wasu manyan na hannun-daman gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa DSS ta tsare mutanen ne ranar Laraba bisa zarginsu da hannu a dabar-siyasa.
Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar ta Kano, Murtala Sule Garo, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya ce yana cikin manyan jami'an gwamnatin jihar da s**a mika kansu ga DSS.
Sauran mutanen sun hada da Fa'izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano, Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo.
Murtala Garo ya ce an gayyaci mutumin da ke son jam'iyyar APC ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar ta Kano a zaben 2023, A.A Zaura, da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa, da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, da kuma wani mai bai wa Gwamna shawara.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikinsu da hannu a manyan-manyan hare-haren dabba, lamuran da s**a yi sanadin mutuwar wasu mutane.