18/10/2025
'DUK WANDA YAKE WULAKANTA SALLAH BA ZAI SAMU (SHAFA'A) CETONMU BA..'
_Nasihar Malama Zeenah Ibraheem Zakzaky
“Wa yace jinkirta Sallah shi ne abin da yafi kyau? A Hadisan Manzon Allah (S) da A’imma (A.s) duk sun yi bayani akan cewa yin Sallah a farkon lokacin sa‚ shi ne abin da yafi kyau. Kuma sun kwaɗaitar ta hanyar ta hanyar Hadisai da dama. Akwai Hadisin da ke cewa.“
“Duk wanda ke walaƙanta Sallah ba zai samu (Shafa’a) cetonmu ba. Walaƙanta Sallah shi ne ya zama ba ka ba Sallah muhimmanci. Lokacin Sallah ya yi‚ ka tsaya kana wasu harkoki baka mayar da Sallah ya zama shi ne muhimmin a rayuwar ka ba.”
“Duk abin da za kayi sai kayi ka gama gajiya sannan kazo kayi Sallah. Akwai shekarun baya akwai ƴan uwan dasu kawo magana wurin Malam (H) cewa; Wasu ƴan’uwa su na yin sakaci da Sallah. Kaman ace ƴar uwa in su na gida irin ‘United nation’ ɗin nan‚ su na girkin su a tsakar gida‚ in lokacin Sallah ya yi.”
“Sai su wanda ba ƴan gwagwarmaya ba‚ (Ƴan uwa na addini) sai su tashi suje suyi Sallah.Ita ko wanda tace ita ƴar gwagwarmaya ne‚ sai ta zauna ta rinƙa girki‚ ta ɓata lokaci sai ta gama duk abin da za tayi sannan za taje tayi Sallah.”
“Lokacin Sallah ze yi‚ tace se ta gama tuƙa tuwo. Mutane na Sallah ita bata damu ba. Kaga mutane zasu fahimci bata Sallah. Kuma wa yace girki na gaba da Sallah? Sallah shi ne kan gaba.”
—Nasihar Malama Zeenah Ibraheem Zakzaky Ga Ƴan’uwa Akan Kiyaye Lokacin sallah. -Cikin Karatun Fikira Saleema.
Ja'afar Muhammad Jr.