
03/04/2024
RAMADAN (23)
-
"Ka sarayar da dukkanin ƙoƙarinka a cikin wannan goman ƙarshen ramadanan ta hanyar daɗa neman kusanci da Allah ta'ala, ka zage damtse, ka kyautata niyya, ka yafe ma waɗanda s**a saɓa maka, ka yawaita aiyukan alkhairi a cikinsu. Manzon Allah ﷺ ya kasance idan goman ƙarshen ramadana tazo, yakan yi iyakar ƙoƙarisa wajen ganin ya dace da rahamar Allah maɗaukakin sarki wacce yake saukarwa a cikin watan mai albarka"
-
"Kada ka shagaltu da ababen duniya, kada ka bari shaiɗan yayi galaba a kanka game da waɗannan kwanuka masu tarin albarka na ƙarshen ramadana, domin haƙiƙa suna da matuƙar falala fiye da na bayansu"
-
"Ka ninka aiyukan alkhairanka a cikinsu, ka nemi taimakon Allah, ka nemi kusanci gareshi a cikinsu, domin haƙiƙa amsa kiran mai kira cikin dare, yana gafartawa waɗanda s**a roƙeshi kuma s**a ƙasƙantar da kansu gareshi"
-
Allah Yasa mudace 💯