13/08/2023
Mata 200 ne s**a ci gajiyar tallafin kayayyakin masarufi da kungiyar Farfesa Gwarzo ta raba a Magama-Jibia da ke Katsina
Sak**akon tsadar rayuwa da ta mamaye al'ummomi da dama biyo bayan tashin farashin kayayyakin amfani na yau da kullum a Najeriya, kungiyar matasan Farfesa Abubakar Gwarzo da ke da himma wajen yiwa bil'adama hidima ta raba kayan masarufi a garin Magama-Jibia, dake a iyakar Jamhuriyar Nijar a jihar Katsina.
Babban sakataren kungiyar Kwamared Saifuddeen Ishaq ya bayyana cewa, tallafin na yau na daya daga cikin muhimman manufofi da ayyukan kungiyar na kyautata alaka da tunkarar mabukata domin tallafa musu da rage radadin wasu matsalolin da suke fuskanta.
“A halin yanzu muna da wasu tsare-tsare na shiga kusurwoyin kauyuka da karkara, don ci gaba da aiwatar da irin wannan tallafi wanda daya ne daga cikin tsare-tsaren wannan kungiya. Abin da ke gaban Farfesa Gwarzo ke nan, shi ya sa muke kokarin bin sawunsa domin bayar da gudunmawarmu don samun babban rabo a ranar kiyama.” In ji shi.
Ishaq ya kuma bayyana cewa tallafawa yara a fannin ilimi na daya daga cikin manufofin kungiyar, inda ya ce suna da tsarin da ke kokarin tura yara makarantu domin neman ilimin addini da na boko.
A nasa jawabin sakataren kudi na kungiyar Kwamared Aliyu Adamu Lamama ya ce sun yi la’akari da irin mawuyacin halin da al’ummar yankin ke ciki sak**akon barazanar rashin tsaro da s**a hada da fatara da yunwa, shi ya sa s**a mayar da hankali wajen tallafawa gajiyayyu da mabukata da sauran yara kanana don rage radadin damuwarsu sak**akon rufe iyakokin kasar biyo bayan juyin mulkin da sojoji s**a yi a Nijar, shi ya sa kungiyar ta samar da kayayyakin abinci don tallafa wa mutane.
Aliyu Lamama, ya kuma bukaci kungiyoyin farar hula da masu hannu da shuni da su jajirce wajen samar da irin wannan shiri na tallafawa gajiyayyu da mabukata da ma sauran makwabta domin kawar da jama’a daga mawuyacin halin da suke ciki.
Wasu daga cikin matan da s**a ci gajiyar tallafin, Fadimatu Zahra’u da Hajiya Halima, sun bayyana jin dadinsu bisa namijin kokarin da kungiyar matasa ta Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ke yi na yi musu hidima a halin da suke cikin mummunan yanayi, sun kuma mika godiya ta musamman ga shugabannin kungiyar da suke jajircewa ba dare ba rana, musamman Farfesa Gwarzo wanda ke taka muhimmiyar rawa ta fuskar yi wa al’umma hidima.