
25/07/2025
Saudiyya ta bayyana matakin da Faransa ta dauka na amincewa da kasar Palastinu a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi da ke kara tabbatar da matsayar da al’ummar duniya s**a cimma game da ’yancin Palasdinawa na kafa ’yantacciyar kasa bisa iyakokin da aka tsara tun shekarar 1967, tare da Gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce wannan mataki yana da matukar muhimmanci wajen ci gaba da kokarin tabbatar da doka da oda na kasa da kasa da kuma aiwatar da kudurorin da s**a dace. Haka kuma, Saudiyya ta bukaci sauran kasashen da har yanzu ba su amince da kasar Palasdinu ba da su dauki irin wannan mataki mai kyau domin tallafa wa zaman lafiya da kare hakkokin Palasdinawa.