
24/08/2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Jihar Katsina ta sayo sabbin motocin yaƙi guda takwas masu sulke don ƙarfafa tsaro da yaƙi da ‘yan bindiga a faɗin jihar.
Matakin na zuwa ne bayan wani hari da ‘yan bindiga s**a kai lokacin sallar Asuba a garin Mantau, ƙaramar hukumar Malumfashi. Wannan ƙoƙari na nuna niyyar gwamnatin jihar wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga barazanar ta’addanci.
Ya kuke ganin yunkurin Dikko Radda na yaki da matsalar tsaro a jiharsa?