06/08/2024
TABBAS AKWAI MATSALA
A ganawar da Shugaban Kasa Tinubu yayi da Hafoshin tsaro dazu, Shugaban Sojojin Nigeria General Christopher Musa yayi bayanin abinda s**a cimma da matakin da zasu dauka
(1) Hankalin Shugaban Kasa Tinubu yayi mummunan tashi bayan ganin masu zanga-zanga suna daga Tutar Kasar Russia, don haka sun tabbatar da cewa daga Tutar wata Kasa a lokacin zanga-zanga laifi ne na cin amanar Kasa (Treason) wanda ba zasu lamunta ba
(2) Sun tabbatar da cewa batagari sun kwace iko da zanga-zanga, don haka yanzu babu eata sauran zanga-zangar lumana da ta rage, zasu hukunta duk wanda aka gani ya fito zanga-zanga a matsayin batagari
(3) Shugaban Sojoji Christopher ya gargadi masu kira ga Sojojin Nigeria su kifar da Gwamnatin Tinubu, Shugaban Sojojin yace ba za'a taba yun juyin mulki ba, abinda s**a sa gaba a yanzu shine bawa tsarin mulkin Demokaradiyya cikakken kariya
Wannan shine abubuwa uku wanda Shugaban Kasa Tinubu da Hafsoshin tsaro na Kasa s**a tattauna a kai, kuma s**a cimma matsaya
A shawarce duk wanda ka sani dan uwanka ne ko aboki to ka bashi shawara ya janye daga fita zanga-zanga, domin abinda tattaunawar Tinubu da Hafsoshin tsaronsa suke nufi shine zasu dakile duk wanda aka gani ya fito zanga-zanga, kun ga dai yadda aka harbe wasu bayin Allah
Don haka 'yan uwa ayi hakuri, mutanen nan babu Allah a lissafinsu, kuskure ne munyi tunda farko muka biye wa yaudaran wasu miyagun Malamai da s**a saka rigar Malaman Allah s**a yaudaremu da addini
Mafita shine mu kai karan azzaluman Nigeria da miyagun Malamansu zuwa gurin Allah Madaukakin Sarki, mu tashi cikin dare muyi Sallah da Karatun Qur'ani mu saka goshin mu a Kasa mu kai karan azzalumai gurin Allah, babu shakka Wallahi Allah zai mana maganinsu ba tare da bata lokaci ba tunda sun zaluncemu
Yaa Allah Ka isar mana, Ka mana maganin abinda yafi karfin mu 🙏
DDatti Assalafiy
Me za ku ce
IIndararo Hausa