Ahbabu sheikh Nuruddeen Almisry yana

Ahbabu sheikh Nuruddeen Almisry yana Tafsir live video and orders matter

A jiya 27 Ramadan,1446 A.H 27th March,2025 maulanu Assheikh Nuruddeen Dahuwa Almisry Yana yayi Katmar karatun da yakeyi ...
28/03/2025

A jiya 27 Ramadan,1446 A.H 27th March,2025 maulanu Assheikh Nuruddeen Dahuwa Almisry Yana yayi Katmar karatun da yakeyi na littafin Asshifa na alqady iyyad A babban masallacin juma'a na garin Yana.
Manyan malamai da dama sun halarci wannan taron kuma sun muna addu'o'i da dama.
Jimkadan bayan 1hour shehi yasake yin katmar karatun alqur'ani wanda yake gudanarwa a Masallacin Alh. Haladu Bangire bakin kasuwa,bayan anyi addu'a Alh Haladu bangire yayi jawabin godiya da jinjinawa shehi bisa jajaircewar da shehi yayi,ya kara da muna fatan Allah ya amsamuna ibadunmu.

13/03/2025

Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da Allah (amsasshiyace).

Ita ni'ima tana bukatar godiyaJarrabawa Tana bukatar hakuriZunubi yana bukatar tuba   Allah kayafemana zunubanmu Albarka...
09/03/2025

Ita ni'ima tana bukatar godiya
Jarrabawa Tana bukatar hakuri
Zunubi yana bukatar tuba
Allah kayafemana zunubanmu Albarkacin wannan wata Mai Albarka

Assalamualaikum.Muna masu baku haƙuri dangane da sanarwar da mukayi na karatun Asshifa a central mosque Yana sai gobe in...
09/03/2025

Assalamualaikum.
Muna masu baku haƙuri dangane da sanarwar da mukayi na karatun Asshifa a central mosque Yana sai gobe in Allah ya yarda.
Daku iya bibiyarmu gobe da misalin 2:30pm a live video insha Allah

02/10/2023

JAULA NA MAULID NA ZAWIYYAR SHEIKH SHARIF IBRAHIM SALEH ALHUSAINI DAKE GARIN SHIRA.
KARKASHIN JAGORANCIN MAULANA IMAM NASIR SHIRA.
17/03/1445 A. H. 02 OCTO, 2023.

01/10/2023
AlhamdulillahWannan itace wasikar da maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh rta ya rubuta sannan ya aikota ga zawiyyarsa da...
01/10/2023

Alhamdulillah
Wannan itace wasikar da maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh rta ya rubuta sannan ya aikota ga zawiyyarsa dake Maiduguri wadda aka karantata a wajen taron maulidin.
Daga bakin MAL. Abba Saleh.
Allah ya kara masa lapiya da tsawon rai.
Ameen.

11/07/2023

[Fahimtata ce]

A Najeriya, daga cikin manyan dalilan da yasa Sufanci yake samu raguwar tasiri da kuma zaizayar mabiya, shine kafewa a matafiya ta gargajiya da kuma ƙin karɓar canji.

Duk wata fikira, ɗariƙah, ko mazhabi da baya karɓar canji ya kuma waiwayi ginin shi da tafiyar shi a zamanance, yana samun ƙalubale da ke iya jawo masa raguwar mabiya da kuma rashin tasiri. Wannan shine babban sirrin da yasa musulunci har yanzu yake samun karɓuwa, duk da matsalar mulhidanci da ake fama da ita, wanda ke alaƙa da wofintar da illimin falsafa da wasu sashin musulmi sukayi kamar Wahabiyawa da sauransu.

Duk da cewa akwai wasu dalilai dake jawo koma baya a wasu sassanni na ƙasarnan, kamar Siyasa, ƙarancin ilimi na mabiya Sufanci da kuma rashin yaɗa shi Sufancin ta hanyar koyarwa, amma dai matsalar gargajiyanci tayi matuƙar tasiri wajen sauƙaƙa yaƙar Sufaye daga abokan hamayyar su, wannan ne ma yasa da yawan ƴan boko ke yiwa shi Sufanci wani gani-gani.

Nazari zai tabbatar da hakan ne ga duk wanda ya kalli guraren da ake rage ƙarfin Sufanci a duniya, da kuma guraren da yake ta ƙara haɓaka. Misali ka ɗauki ƙasar Morocco, Egypt, Tunisia, Algeria, Sudan, Senegal, da ma Gambia a Afirka, ba komai yasa Sufanci har yau ya gagara ba, sai saurin karɓar canji na wayewa da sauye-sauyen manufofi da zasu dace da zamani ba tare da kaucewa asalin manufar Sufancin ba, wato gyara ko wankin zuciya.

Amma a ƙasashe irin Najeria, Ghana, Niger, Kamaru da sauransu, zaka samu sufancin bai cika dacewa da zamanin ba, hasali ma wanda yayi yunƙurin nusar da haka, na iya zama abin tuhuma, ko ma ƴan bani na iya su kore shi daga cikin Ɗariƙar.

Daga cikin alamomin rashin karɓar sauyi da ake fama da shi akwai takaita Zawiyoyi a matsayin wajen Wazifa da Zikiri kawai, akwai taƙaita fahimtar ilimi a matsayin karatun Addini kaɗai, akwai ƙin zamanantar da shi kanshi ilimin Addinin, akwai rashin zamanantar da tsarin shugabanci na halarori da zawiyoyi da ma dai sauran abubuwa da ƴan uwa zasu iya halartowa.

رُجُوعِي مِنَ الْمَوْلَى الْجَلِيلِ جَلاَلُهُإِلَيْهِ بِحُبِّ الْـهَاشِمِــيِّ وَلاَ غَرْوَا____________________________...
26/05/2023

رُجُوعِي مِنَ الْمَوْلَى الْجَلِيلِ جَلاَلُهُ
إِلَيْهِ بِحُبِّ الْـهَاشِمِــيِّ وَلاَ غَرْوَا
________________________________________

رَحِيمُ أَيَا مَنَّانُ مَنْ جَــــلَّ ذِكْـــــرُهُ
فَصَلِّ عَلَيْهِ وَارْفَعِ الضِّيقَ وَالشَّكْـوَى

21/05/2023

Address

زاوية الشيخ نوردين غلاديمة(المصري) يان
Yana

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahbabu sheikh Nuruddeen Almisry yana posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ahbabu sheikh Nuruddeen Almisry yana:

Share

Category