Anku Tv News

Anku Tv News To getting More News

Da Dumi Dumin Sa.Tsohon Dan Takarar Majalisar Jaha Na Karamar Hukumar Hadejia Manu Vice Ya Fice Daga Jama iyar NNPP Zuwa...
15/04/2026

Da Dumi Dumin Sa.

Tsohon Dan Takarar Majalisar Jaha Na Karamar Hukumar Hadejia Manu Vice Ya Fice Daga Jama iyar NNPP Zuwa APC Mai Mulki.

A Yau Laraba A Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa In Da Ya Samu Kar Bah Daga Gwabnan Jigawa Mallam Umar Namadi Fca Da Kuma Shugaban Jama iyar Ta Apc Na Jahar Jigawa Wato Rt Hon Ahmed Garba Mk Da Sauran Masu Ruwa Da Tsaki Na Jahar.

Labaran Hausa.

Da Dumi Dumi Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birniwa Umar Baffa Ya Fita Daga Jama iyar A. p.c.An Hangi Hakan Ne A Safin ...
14/04/2026

Da Dumi Dumi

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birniwa Umar Baffa Ya Fita Daga Jama iyar A. p.c.

An Hangi Hakan Ne A Safin Sa Na Facebook In da Ya Wallafa Takarda Cewa Ya Fita Amma Bai Bayyana Inda Zai Koma Ba Sai Nan Da Wani Lokacin.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu beli daga Kotun Tarayya.A hukuncin da kotun ta yanke, an amince da ...
14/04/2026

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu beli daga Kotun Tarayya.

A hukuncin da kotun ta yanke, an amince da bayar da belin ga El-Rufai bayan sauraron bukatar da lauyoyinsa s**a gabatar, inda kotun ta ga ya dace a ba shi damar fita bisa wasu sharudda.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan sharuɗɗan belin ba, yayin da ake sa ran zai ci gaba da fuskantar shari’ar da ake yi a kansa a gaban kotun.

Ƙarin bayani...

Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Abba ya shiga rudani: a daidai lokacin da Sen Barau da Abdullahi Abbas s**a yi watsi da Murtala Gar...
13/04/2026

Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Abba ya shiga rudani: a daidai lokacin da Sen Barau da Abdullahi Abbas s**a yi watsi da Murtala Garo s**a nuna goyon bayansu ga Rabi'u suleiman Bichi kan kujerar Mataimakin Gwamnan Kano

Wani sabon salon rikici na siyasa ya ɓulla a Kano yayin da Sanata Barau Jibrin da tsohon shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, s**a fito karara s**a mara wa Engr. Rabiu Suleiman Bichi baya domin zama Mataimakin Gwamnan jihar a daidai lokacin da wasu jiga-jigan jam’iyyar da s**a hada da Abdullahi Umar Ganduje da sen kawu Sulaiman da alhassan ado da abba bichi da wasu yan majalisar s**a Goyi bayan Hon Murtala Sule Garo

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan matsaya ta fito ne daga cikin wata tattaunawa ta manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, inda aka nuna cewa Bichi ne zai iya haɗa kan ɓangarorin da ke rikici a cikin jam’iyyar.

Majiyoyi sun ce Bichi na da cikakkiyar gogewa a harkokin gwamnati, wanda ya haɗa da manyan muk**ai da ya riƙe a baya, lamarin da ya sa ake kallonsa a matsayin wanda ya dace da wannan kujera mai muhimmanci.

Ana yawan jefa martanin siyasa mai zafi tsakanin magoya bayan Sen Barau Jibrin da na Hon Murtala Garo

Tsohon Mataimakin karamar hukumar Dutse ya rubuta takarda shima.
08/04/2026

Tsohon Mataimakin karamar hukumar Dutse ya rubuta takarda shima.

Jiya Zakari Kafin Hausa yaje Hadejia meeting gidan Senator Ubali, amma akan hanya ta ta fita daga gari sai wani Masoyin ...
08/04/2026

Jiya Zakari Kafin Hausa yaje Hadejia meeting gidan Senator Ubali, amma akan hanya ta ta fita daga gari sai wani Masoyin sa ya gayyace ya tsaya yaga wajen sana'ar sa ko da 'minti biyar ne'. Minti biyar ɗin nan sai da ta zama sama da Awa 2 suna tattaunawa da shugabanni da kuma mambobin kasuwar kifi dake Hadejia.

Kasuwar kifin Hadejia ita ce babbar kasuwar kifi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya kuma ta na da ƴan kasuwa sama da 5000 dake neman abinci a jikin kasuwar, sa'annan kuma duk satin duniya ana cinikin kifin sama da naira miliyan 400.

Mun tattauna akan gwamnati, yadda ya k**ata muyi a kakar zaɓe me k**awa idan ƴan 'ci ka tsere' sun dawo neman goyon baya da kuma mahimmancin cigaba da wayar da hankulan juna akan ilar da akayiwa al'ummar mu cikin wannan shekaru. Munyi magana akan rashin cika alkawarin gyaran kasuwar da Gwamna ya musu lokacin zaɓe da kuma yadda Gwamna har yanzu yaƙi cika alkawarin daya dauka na buɗe Asibitin Kwararru na Hadejia ( da sauran batutuwan da s**a shafi al'ummar kasar Hadejia, Jigawa da kuma Nijeriya.).

DA DUMI-DUMI: Kotu ta ki amincewa da belin Malam Nasiru El-Rufai, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga wata...
01/04/2026

DA DUMI-DUMI: Kotu ta ki amincewa da belin Malam Nasiru El-Rufai, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu.

Babbar Kotun Birnin Tarayya ta soke umarnin k**a tsohon Minista kuma shugaban wani ɓangaren PDP, Kabiru Turaki, wanda ak...
01/04/2026

Babbar Kotun Birnin Tarayya ta soke umarnin k**a tsohon Minista kuma shugaban wani ɓangaren PDP, Kabiru Turaki, wanda aka bayar a ranar 26 ga Maris.

Alƙali, Mai Shari’a Peter Kekemeke, ya yanke hukuncin ne bayan Turaki ya gurfana a gaban kotu da kansa tare da lauyansa, Chris Uche (SAN).

Lauyan nasa ya ba kotu haƙuri kan rashin halartar da ya yi a zaman da ya gabata, yana mai cewa bai yi hakan da gangan ba, kuma yana girmama kotu sosai.

Shi ma ɓangaren gwamnati bai yi adawa da soke umarnin kamun ba, inda ya ce manufar umarnin ita ce tabbatar da halartar wanda ake tuhuma—kuma hakan ya cika.

Kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 22 ga Afrilu, 2026, domin fara sauraron tuhumar da ake masa, wadda ta shafi zargin ba da bayanan ƙarya ga ‘yan sanda.

Kotu ta tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin sataWata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hu...
01/04/2026

Kotu ta tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin sata

Wata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hukumar Fagge, jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu bisa zargin satar wayar matar sarkin, da kudade da wasu kayayyaki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda ake tuhuma sun hada da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, inda aka gurfanar da su kan tuhume-tuhume uku da s**a hada da hadin baki, sata da karbar kayan sata.

Mai gabatar da kara, Barista Abubakar Ibrahim, ya bayyana wa kotu cewa Sulaiman, wanda ke aiki a matsayin direban matar Sarkin, ya shiga dakinta ba bisa ka’ida ba, ya sace kayayyakin da aka kiyasta kudinsu ya kai naira miliyan 60, tare da wasu kudade da wayar salula.

A lokacin da aka karanta tuhume-tuhumen, Sulaiman ya amsa laifi, yayin da sauran biyun s**a musanta. Koda yake Lauyan wadanda ake tuhuma, Barista A.A. Abdullahi, ya gabatar da bukatar beli.

Alkalin kotun, Mai shari’a Halilu Abdurahman, ya amince da bayar da beli ga wadanda ake tuhuma tare kuma da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu, sai dai za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharuddan belin.

YANZU-YANZU: Kotu ta dage sauraron bukatar ba da belin tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i har zuwa ranar 31 ga watan ...
24/03/2026

YANZU-YANZU: Kotu ta dage sauraron bukatar ba da belin tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i har zuwa ranar 31 ga watan Maris 2026.

Court of Appeal ta sallami shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, ta ayyana Ali Hardworker matsayin Chairman na LG ɗin.
24/03/2026

Court of Appeal ta sallami shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, ta ayyana Ali Hardworker matsayin Chairman na LG ɗin.

Yanzu-Yanzu: Wata babbar mota ɗauke da yashi ta kutsa kai tare da buge sabuwar ƙofar gidan gwamnatin jihar Gombe bayan t...
24/03/2026

Yanzu-Yanzu: Wata babbar mota ɗauke da yashi ta kutsa kai tare da buge sabuwar ƙofar gidan gwamnatin jihar Gombe bayan ta kufce daga hannun direban da ke tuƙawa, lamarin da ya haifar da mummunar ɓarna ga mashigar gidan gwamnatin..

Rahotanni sun bayyana cewa direban motar ya samu ƴan raunuka sak**akon hatsarin

Address

Yayari

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Anku Tv News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Anku Tv News:

Share

Category