02/06/2022
Zuwa ga Gwamnan Bauchi: Shawara da gargadi
Assalamu Alaikum. Bayan gaisuwa mai tarin yawa, da fatan Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad da sauran mutanen Bauchi suna lafiya.
Bayan haka ni dan siyasa ne, kuma mai kishin Jihar Bauchi da mutanenta k**ar yadda mutanen s**a sani. Duk abin da zai kawo cikas ga mutanen Bauchi da cigabansu, bana kaunarsa, kuma zan yi duk abin da zan iya domin kare shi.
Na yi takarar sanata Bauchi ta Kudu kuma Allah bai bada nasara ba amma ganin abinda yafaru yaban tsoro da takaichi game da irin siyasan da ake guda narwa ajiharmu da ma nigeria baki daya.
Ganin irin yadda lamura s**a lalace ne ya sa nake rubuta wannan shawara ga Gwamnan Bauchi domin kaunar jihar da nake yi kuma domin a kawo gyara.
Bai k**ata a ce ta yanan gizon ne na turo maka wannan wasika ba, amma kasancewar na yi kusan wata shida ke nan ina neman zama da kai, amma abin bai samu ba. Mun hadu a wani taro na ce ina so in ganka, ka ce zaka ban lokaci amma bai yi ba. Na bi ta hannun shugaban jam’iyya har k**an sau biyu shima bai dawo min da amsa ba. Wannan ya sa na ga babu wata hanya da zan fidda hakkin mutanen Bauchi, su san na isar da sakonsu face ta wannan hanya.
Akwai lokacin da gwamna ya kira mu taron shan ruwa, sai na yi tunanin wannan lokaci ne mai kyau da zan isar da sakon talakawa domin mu ne muke zama da su, kuma muka san kokansu da abubuwan da suke damunsu. Amma a nan ma sai aka hana mu magana, sai aka saurari wasu kalilan da aka san suna kusa da gwamna da ba za su fada masa gaskiya ba saboda dan abin da suke samu.
Ina jan hankalin gwamna da ya tuna abin da tsohon Gwamnan Bauchi MA Abubakar ya yi muka cire shi, to fa kai ma gwamna kusan ka k**a irin wannan hanya. Don duk alamomin abinda M A yakeyi kai ma yanzu kusan sun tabbata kanayinsu misali rashin sauraron shawari daga jamaa, raini da dai sauransu. Na tabbatar maka da kana shawari da mutanen kwarai sosai shari’an da ka yanke na hana wadansu yan siyasa tsayawa na yin takaran muk**ai da bam da bam chikin Jam'iyar mu na PDP, da baka dauki wannan matakin ba.
Sannan kuma bugu da kari takarar da ka shiga na neman Shugaban Kasa, tun farko mutanen Bauchi sun ce maka ka hakura tunda Allah ya baka gwamna wanda kana dama har na shekaru takwas amma wadannan tsirarun mutanen da ba su gaya maka gaskiya s**a shawarche ka da kaje kanema toh hakan bai haifar da komai ba illa asaran kudin jama’an Bauchi.
Don haka ina kira gare ka mai girma gobna da cewa mutanen Bauchi sun san abin da suke yi. Lallai abin da ya faru da wancan gwamnan, zai iya faruwa da kai matukar ba a gyara ba. Muna fuskantar zabe, muna kuma so jam’iyyarmu ta PDP ta yi tasiri kuma ta samu nasara ne a duk zabukan da za mu shiga. Don haka dole achanza yadda ake gudanar da abubuwa in har munason jam’iyar mu ta PDP ta lashe duk zaben da za ayi mai zuwa.
A karshe kuma lallai idan muka fadi zabe, to fa gwamna da shugaban jam’iyya ne suke da laifi,
Sako daga Ahmed Shuaibu (Raba Gardama)