
06/05/2025
Geckos, Tsaka dangin kadangare ne dake rayuwa a nahiyoyin duniya. Ana samun su a wajaje daban daban. Wannan dangin na kadangaru shine mafi girma mai jinsi sama da dubu daya da dari takwas. Akwai abubuwa masu abin mamaki game da wannan dangin kadangarun.
Ba k**ar sauran jinsin kadangaru ba da basu iya magana ko sauti, Tsaka na fitar da sauti wanda suke magana dashi. Idan watakila ka taba kwana a gandun dajin da suke da tsaka sosai zaka iya jin yadda suke wannan sautin.
Tsaka na cikin dabbobin da suke iya tafiya a bai bai ajikin bango ko gilasi saboda yanayin halittar kafar su k**ar yadda yake acikin hoto. Haka nan, ba k**ar sauran kadangaru ba da suke da tantanin ido, wato eyelids, Tsaka basu dashi shi yasa suke lashe idon su domin gani da kyau (duba idon acikin hoto). Bugu da kari, shi yasa basu iya ƙifta ido. Karfin ganin tsaka yafi na dan adam sau dari uku da hamsin. Lallai shi yasa baka iya buge ta cikin sauki.
Idan abokan gaba wato predator yai kokarin k**a Tsaka, tana iya gutsure jelarta ta gudu wanda zaka iya fahimtar haka idan kai kokarin kashe ta a gida. Idan ta samu ta gudu, tana iya sake sabuwar jela.
A wasu kasashe na duniya k**ar k**ar Amerika da Turai ana kiwon Tsaka a gida, ma'ana house pet. Duk da cewa yawan jinsin Tsaka suna rayuwa a daji, akwai jinsin da sun fi rayuwa acikin gida. Tsaka tafi yawo da daddare amma akwai wadanda suke rayuwar su da rana.
Duk da binciken masana kimiyya ya nuna cewa Tsaka bata dauke da dafi ko guba, binciken ya nuna cewa jikin Tsaka na dauke da kwayoyin cuta masu yawa wanda idan s**a taba abinci za'a iya kamuwa da cuta. Hakan yasa shari'ar musulunci tai umarnin kashe su.
Acikin hoto jinsin Tsaka ne da ake kira da Tropical House Gecko wadda ke yawan rayuwa acikin gida.
Idan kasan wani abu game da wannan dabba sa mana a koment.