11/10/2025
Daya daga cikin hazikan ‘ya’yan garin Ngurore, Babangida Abdullahi, ɗalibi mai karatu a Department of Chemistry, Level 400 a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, ya samu babban mukami na Chief of Staff a ƙungiyar National Association of Science Students (NASS), ATBU Bauchi Chapter.
Wannan na ƙunshe ne a wata takardar da Shugaban ƙungiyar, Comr. Idris Musa Adam, ya sanya wa hannu a ranar 10 ga Oktoba, 2025, inda aka bayyana cewa nadin ya biyo bayan jajircewar Babangida a fannin shugabanci, kishin ɗalibai da kuma gudunmawarsa ga ci gaban ƙungiyar.
A cikin takardar, shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa:
“Wannan mukami alamar amincewa ne da jajircewa da nagartar Babangida Abdullahi, kuma muna sa ran zai ci gaba da wakiltar ƙungiyar da kwarewa da gaskiya.”
A matsayin sa na Chief of Staff, Babangida zai rika kulawa da ayyukan majalisar zartarwa ta ƙungiyar, ba da shawara ga shugaban ƙungiya, da wakiltar ƙungiyar a hukumance.
Al’ummar Ngurore sun bayyana farin cikinsu bisa wannan nasara, suna masu cewa wannan wata gagarumar dama ce da ke ƙara ɗaukaka sunan garin a tsakanin ɗaliban jami’o’i.
“Wannan nasara ce ba wai ta Babangida kaɗai ba, har da mu matasan Ngurore baki ɗaya,” in ji wani matashi da ke cikin garin.
Ngurore Community TV
📷Babangida Abdullahi