Labarai DAGA MUBI

Labarai DAGA MUBI Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Labarai DAGA MUBI, Radio Station, SHAGARI PHASE 2, Yola.

Idan nace Bilkisu Aliyu Bala toh ina nufin wannan yarinyar Allah ya barmu tare ƴar uwa
02/06/2025

Idan nace Bilkisu Aliyu Bala toh ina nufin wannan yarinyar
Allah ya barmu tare ƴar uwa

Kotu Ta Tura Matasa Biyar Gidan Yari Kan Zargin Kashe Mutum a Wurin Biki a MubiWata babbar kotun majistare ta biyu da ke...
17/05/2025

Kotu Ta Tura Matasa Biyar Gidan Yari Kan Zargin Kashe Mutum a Wurin Biki a Mubi

Wata babbar kotun majistare ta biyu da ke zaune a Yola, jihar Adamawa, ta tura wasu matasa biyar zuwa gidan yari a ranar Juma’a bisa zargin dukan wani mutum har lahira da sanduna a wajen wani biki da aka gudanar a karamar hukumar Mubi ta Kudu.

Alkalin kotun, M. A. Adamu, ne ya bada umarnin a tsare su, kuma ya daga sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Yuni, 2025.

Wadanda ake zargin su ne:

Timothy Hassan (25)

Iliya Kwada (28)

Markus Ezra (38)

Joel Michael (32)

Lukman Shuaibu (27)

An gurfanar da su bisa zargin hadin baki don aikata laifi, raunata mutane da makami, mallakar muggan mak**ai, barna da kuma kisan kai — laifukan da s**a saba wa sashe na 60, 218, 69, 318 da 191 na dokar laifuka ta Jihar Adamawa na 2018 da aka gyara.

Lauyan gwamnati, Insp. Hamza Abdullahi, ya shaida wa kotu cewa a ranar 4 ga Mayu, 2025, wadannan matasa sun tare wurin wani biki da ake yi a Wuro Barka, Mubi South, dauke da muggan mak**ai.

An zargi su da dukan wasu mutane biyu — Bamanga Yakubu da Okacha Adamu — da adduna da sanduna, tare da lalata babur dinsu. Sak**akon dukan da s**a yi musu, aka garzaya da su asibitin Mubi, inda likita ya tabbatar da mutuwar Bamanga Yakubu.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta k**a su da mak**ai irin su bindiga mai bututun gida, adda, sanduna da kuma karafunan rodi.

A kotu kuwa, yayin da Timothy, Markus da Lukman s**a musanta laifin, Iliya da Joel sun amsa cewa sun aikata laifukan.

Rahoton labarai daga mubi

Paparoma ya yi kyakkawan karshe - Tinubu Da zuciya mai nauyi, na shiga cikin Kiristoci na Katolika da sauran mabiya addi...
21/04/2025

Paparoma ya yi kyakkawan karshe - Tinubu

Da zuciya mai nauyi, na shiga cikin Kiristoci na Katolika da sauran mabiya addinin Kirista a duniya wajen jimamin rasuwar Paparoma Francis — bawan Allah mai tawali’u, mai himma wajen kare talakawa, kuma fitila ga miliyoyin mutane in ji shugaban Nijeriya Bola Tinubu

A cewar Tinubu, rasuwar Paparoma wadda ta biyo bayan bikin Ista, wata alama ce ta da ke nuna cewa ya koma ga Mahaliccinsa a wani lokaci da Kiristoci ke cike da sabuwar fata da bege.

Yaron da jami'in tsaro ya harba bisa kuskure a lokacin da rikici ya tashi a kasuwar shopping complex na mubi yana asibit...
06/04/2025

Yaron da jami'in tsaro ya harba bisa kuskure a lokacin da rikici ya tashi a kasuwar shopping complex na mubi yana asibiti
A sanadiyyar wannan rikicin, anyi asarar rai na mutum guda
Allah ya kiyaye nagaba
Kasance da wannan shafin domin samun sabbin labarai

Ga wani dan keke napep wanda ya saukar da farashinsa na daukan mutane daga Naira 200 zuwa Naira 100 domin watan Azumi Ra...
01/03/2025

Ga wani dan keke napep wanda ya saukar da farashinsa na daukan mutane daga Naira 200 zuwa Naira 100 domin watan Azumi Ramadan khareem

Wane fata kuke wa mai wannan adedeta sahun?

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fito ya yi bayani daga ɓangarensa kan zargin ya nemi lalata da Sanata Na...
01/03/2025

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya fito ya yi bayani daga ɓangarensa kan zargin ya nemi lalata da Sanata Natasha - Duba a sashen sharhi.

21/01/2025

barka da zuwa shafin labarai da yashafi jihar mu adamawa musamman yankin mu mubi ta arewa da mubi ta kudu
maraba da zuwa

Address

SHAGARI PHASE 2
Yola
112233

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labarai DAGA MUBI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category