04/06/2023
WALITAKAR ALBANIY DA JA'AFAR TA BAYYANA
Zan fara da Baffa Hotoro wanda yake jingina kansa da da'awar Sunnah Salafiyyah
Lokacin da Baffa Hotoro ya bayyana, yana son a sanshi yayi suna, sai ya dauki hanyar zakulo maganganun Marigayi Sheikh Ja'afar da Sheikh Albaniy Zaria yana datsewa yana musu sharri da kage yana ciresu daga da'irar Sunnah yana alakanta musu ta'addanci da kungiyar Boko Haram
Ina tuna lokacin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi yake kafa hujja da maganar Baffa Hotoro akan batanci da sharrin da yayi wa Shahidanmu Malam Ja'afar da Albaniy, to wannan yana daga cikin munin barnan da Baffa Hotoro yayi wa da'awar Malam Ja'afar da Albaniy don neman a sanshi, saboda 'yan bidi'ah kan kafa hujja da maganganun batancin da ya yiwa su Malam Ja'afar
Da Allah Ya tashi k**a Baffa Hotoro, sai ya k**ashi ta hannun makiyan su Malam Ja'afar inda shi Baffa Hotoron ya tsallaka kan Sheikh Dahiru Bauchi yaci mutuncinsa, su kuma iyalan Sheikh Dahiru s**ayi karansa, DSS s**a masa damka mai karfi har da leg-chain a kafarsa, ya fito a bidiyo yana basu hakuri, to ba komai bane alhakkin su Malam Ja'afar ne da Albaniy ya k**ashi, watakila hakan ya zama sanadin shiriyarsa
Sai ga wani yaro a Bauchi daga bangaren sufaye Abulfathi Attijjaniy ya bayyana, yana ta zagi da cin mutuncin Malaman Sunnah, kai tsaye ya fito yace su Albaniy da Ja'afar 'yan ta'adda ne sun karantar da ta'addanci bayan ya kudunduma musu buhunan ashariya ana ta buga masa kabbara yana kwaba
Daliban Malam Albaniy s**a yi karansa gurin shugaban 'yan sandan Nigeria IGP, 'yan sanda sun k**ashi don gudanar da bincike kafin a tafi Kotu, shine yayi bidiyo babu riga dagashi sai singilet yana bada hakuri don ya san zai dauru igiya sai ya saura, to wannan bidiyon yayi a kansa ne, amma Kotu kam sai ya je, don ba'a hakura ba
Wannan duka alamace da take tabbatar mana da cewa su Malam Albaniy Zaria da Malam Ja'afar Waliyyai ne, Malaman Allah ne, basu karantar da ta'addanci ba, sun yaki ta'addanci ne, akan fada da ta'addanci da su