09/06/2025
K|SAN RAI AKAN WAYA
Wannan Officer ne a rundinar Sojin ruwa Nigeria, sunansa Lieutenant Commander Muhammad Buba, wani dan daba a jihar Kaduna ya masa ki$an gilla a yunkurin da yayi na kwace wayarsa
Abinda ya faru shine Sojan ya zo course ne a Armed Forces and Command Staff College (AFCSC) dake Jaji a jihar Kaduna, yana tafiya a mota sai tayar motarsa tayi faci, ya tsaya yana gyarawa sai barawon yazo, ya bukaci karban wayansa ya hana, shine sai barawon ya zaro wuka ya burma masa a saitin kahon zuciyarsa
Amma kafin barawon ya gudu an kawo dauki shima aka masa mummunan ki$an gi||a, ba'a barshi ya gudu ba ya hadu da sakamako tun anan duniya
Hoto na farko Sojan ne lokacin yana raye, hoto na biyu bayan an masa ki$an gi||a akan wayarsa, hoto na uku barawon wayar ne shima aka dagargaza kansa da dutse, na rufe saboda Facebook basa bari a saka irin hoton
Wannan Matashin Ofisan Soji ya mutu akan kokarin kare dukiyarsa, muna kyautata zato ya dace da mutuwar shahada Insha Allah
Jama'a masifu sun yi ywa a wannan zamanin namu, a cigaba da yin addu'ah na neman tsarin Allah a duk lokacin da za'a fita, bamu da wata garkuwa imba addu'ah ba
Allah Ya karemu daga sharrin macuta azzalumai