15/09/2026
Mafitarmu:
“Mu yanzu da muke zaune a wannan al'ummar, an jefa mana wadansu abubuwa da s**a zama sun hana mu ma mu fahimci gaskiya, sai muna ta fada akan abubuwa daban-daban, ana ta kunno mana da su, mu yi ta fada da su.
“An kawo mana rashin tsaro, saboda ya dauke hankalinmu ne. An kawo mana talauci, saboda ya dauke hankalinmu ne. An kawo mana fadan kabilanci da bangaranci da sauransu, duk don haka ne. Duk wadannan su s**a dauke hankalin al'umma, kullum suna rigima ne. Saboda mene? Sun kasa gane mene ne ya k**a su koma a kai.
“Kuma lallai abinda ya k**ata su fahimci cewa, ita al'umma wannan rigimar ba zai taba kai ta ga gaci ba. Rigingimun nan da suke yi, la'alla tsakanin addini da addini ne, ko a cikin addinin ne, ko tsakanin gari da gari ne, ko bangaren ƙasa da wani ɓangare, ko ƙabila da ƙabila, (duk) wadannan rigingimun suna amfanan maƙiya ne. Maƙiya s**a shuka su domin su su amfana.
“Saboda haka idan mutane s**a gano cewa ba kan wannan ya k**ata mu sa hankalinmu ba, ya k**ata ba, ya k**ata ne mu sa hankalinmu akan cewa, ai duk cikanmu al'umma guda ce, kuma Allah Ta'ala ne ya halicce mu, ya dora mu a doron kasa, addininSa kuma 'Wadih' (a sarari yake), wanda ya yi imani ya yi, wanda bai yi ba kuma dai ruwansa, amma dai bai zo da addinin domin mu riƙa rigima muna fada da juna ba. In muka fahimci wannan, muka gane wannan, to insha Allahul Azeem abubuwa za su saukaka mana.
“Kuma dai karshen al'amari muna cewa, makoman wannan al'ummar, ko an ƙi, ko an so, komawa ga gaskiya ne. Gaskiyar magana kenan, lallai komai fada da gaskiyan da kake, watarana za a koma ga ita ne. Muna shekarun fata ne, ba muna shekarun da ba fata ba ne. Da muna shekarun da ba fata ne, sai mu ce ba fata, muna jiran hurin kaho ne kawai Kiyama ta tsaya. Amma yanzu abin da muke jira kenan? Muna jiran tabbatan addini ne. Alkawari ne na Allah, kuma. Allah ba Ya saɓa alkawari. Allah Ya gaggauta bayyanar wanda da bayyanarshi ne komai zai zamo daidai Insha Allahul Azeem.”
— Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) a Mauludin Resource Forum na Harka Islamiyya a Abuja, ranar Lahadi 1 Rabi'ul Thani 1448 (13/9/2026)
02/RabiuThani/1448
13/09/2026