07/10/2025
JAN HANKALI DANGANE DA HAƊIN KAN MUSULMI
— Daga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
“Saboda haka, mutum ya k**ata ya yi nazarin wa yake ma aiki? Mun sha fada mukan nanata ba daya ba biyu ba, duk wanda ka ji ya na kira ga rarrabar kawukan Musulmi, ya yarda ko bai yarda ba, ya sani ko bai sani ba, yana ma makiya aiki ne—ko ya yarda ko kar ya yarda, ko ya sani ko kar ya sani yana ma makiya aiki ne. Domin aikin makiya ne, shirinsu ne na rarraba din. Yanzu al'ummar Musulmi ya zama abinda ya dame su shi ne; me ya raba su ba meya hada su ba.
“Na'am ba muce ba abinda ya raba su ba, Manzon nan (S) ya zo da sako, kuma ya isar da sako ɗin. Allah Ta'ala Ya saukar masa da Alƙur'ani kammalalle cikakke, babu abinda ya kara shi babu abinda ya rage shi. Kuma ya bayyana ma'anar Alƙur'anin, kuma bai bar duniyar nan ba sai da ya kafa al'umma akan Addini.
“To amma al'ummar ita ta bamu gadon waɗansu abubuwan. An samu sabani akan shugabanci—wannan sabani ne aka samu. Ba a samu sabani akan matsayin Allah Ta'ala a matsayin Shi ne kadai Abin bauta ba. Ba a samu sabani akan shi Manzon Allah ne, kuma bawan Allah Manzon Allah, ba wani wanda ya ke kiranshi Ubangiji ko ɗan Ubangiji, ko daya daga cikin wadanda s**a taru s**a yi Ubangiji. Har ma a tashahud (zaman tahiya) dinmu sai mun ambaci; shi bawa ne kafin mu ce shi Manzo ne. A kullum sai mun ce; “Wa Ashhadu Anna Muhammadan Abduhu wa Rasuluhu”.
“Saboda haka bamu da sabani akan matsayin Manzon Allah, ba wani wanda yake ce mishi Ubangiji ko ɗan ubangiji ko abinda ya yi k**a da haka. Bamu da sabani akan Alƙur'ani. Na'am za ku ji zancen wawayen gari suna ce muku akwai wani Alƙur'ani daban, amman dai ‘Fi'ilan' dai Alƙur'ani guda daya ne, bashi da ƙari ba ragi shi ne Wannan.
“To amma al'umma ta saba akan fassara da ruwayoyi, don haka aka samu abinda ake ce ma ‘Firƙa' an samu ‘Firƙoƙi’ an samu Mazahib— Mazhabobi, an samu ‘Ɗuraƙat’ an samu Ɗariƙoƙi, wannan a cikin addinin suke. Lokacin da muke magana kan Mazhaba ko Firƙa, ko Ɗarika, muna magana ne kan ‘Juz'i’ bangare muke magana akai. Amma in muka zo muna magana akan Musulunci muna magana ne akan abinda ya doru ne akan dukkan wadannan, shi ne a sama, Musulunci ne a sama. Su wadannan karkashin Musuluncin suke. Duk wanda ka ji yana rigima akan Firƙa to yana rigima akan bangare ne, ya bar tushe, ya bar asali, yana magana akan reshe ne.
“Duk wanda ka ji yana magana akan Mazhaba shi ma ya bar tushe ne ya koma yana rigama akan reshe ne. Duk wanda ka ji yana rigama akan Ɗarika shi ma ya bar tushe ne ya koma reshe, don wadannan rassa ne. Firƙoƙi, Mazhabobi, Ɗariƙoƙi, da ma yanzu da ake yayin ƙungiyoyi, duk waɗannan ƙungiyoyi juz'iyai ne.
“Na'am da manufofi daban-daban, ba su (manufofin) ne asasi ba, ba su ne kuma asali ba. Muna magana kan asali ne; sunanmu Musulmi, ba sunanmu wadannan rarrabe-rarraben ba. Sunan al'ummarmu Musulmi shi ne ainihin Allah Ta'ala Yake cewa: “Huwallazi Sammakumul Muslimin min Kab, Wafihazalik” Ainihin shi ne tun farko mun ambace ku addinin Babanmu Ibrahim shi ne ya ambace ku, ma'ana Allah Ta'ala shi ne Ya ambace ku Musulmi tun farko da kuma a wannan lokacin da wannan Manzon ya zo, domin ku zama shaida ga sauran al'ummu, kuma Manzo ya zama shaida akan ku.
“Yanzu kiraye-kirayen sunannaki da daukan kowwane suna a matsayin shi ne ma addinin ayi ta rigima akai. Da kuma katangar karfen da aka sa a kwakwalwa, babu katangar sam, ba ta da wujudi sam-sam! Amma sai a kirkireta a raba tsakanin al'umma, har mutum ya riƙa ganin cewa wancan tsakaninsa da shi akwai shamaki, ra'ayinsu daban ne, fahimtarsu daban ne, har ma in tayi k**ari ma sai ya ce addininsu daban ne, alhali katanga aka sa masa a kwakwalwarsa—ta fi katangar karfe karfi. Saboda ainihin ta raba shi da ɗan'uwansa Musulmi alhali addininsu guda.
“To wannan lokaci namu da ainihin bamu son ya zama sai maƙiya ne zasu ingiza mu izuwa hadin kai, don shi hadin kan nan a cikin addinin namu ne yake, umarni ne na Allah Ta'ala: “Wa Atasimu Bi Hablillahi Jami'an Wala Ta Farraƙu” ku yi riko da igiyar Allah gabadayanku kar ku rarraba, aka nuna illar rarraba tun a na farko, sannan kuma
harwalayau shi wannan Manzo ya k**anta al'ummar Musulmi da misalin jiki guda, wanda idan wani ɓangare nasa ya yi ciwo, duk sauran bangarorin za su amsa da rashin bacci da kuma zazzabi. Saboda haka idan aka taba wani bangare duk gabadaya jikin ne yake amsawa, to haka al'ummar Musulmi suke, tamkar jiki Guda ne”
— Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin jawabinsa na Khatamar Makon Hadin kai na shekarar 1447/2025.
06/10/2025