11/06/2026
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ta zama cikakkiyar mamba ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ta karɓi katin shaidar zama mamba a jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin ya biyo bayan umarnin da Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayar ga manyan jami’an gwamnatinsa da su koma jam’iyyar APC ko kuma su fice daga mukamansu.
Majiyoyi sun ce gwamnan ya bai wa dukkan manyan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa wa’adin sa’o’i 48 domin su bayyana matsayinsu tare da bin sabon tsarin siyasar da ake aiwatarwa a jihar.
Komawar Mataimakiyar Gwamnan zuwa APC na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa a jihar Adamawa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da martani daga bangarori daban-daban.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga ofishin Mataimakiyar Gwamnan ko gwamnatin jihar da ke ƙarin bayani kan matakin da aka ɗauka.