
08/10/2025
Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya gargadi ’yan siyasa da sauran al’umma da su guji siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa yaki da rashin tsaro abu ne na haɗin kai da ya shafi kowa ba wai jam’iyya ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na Zauren Tuntuba na Dattijan Jihar Kebbi wanda na bana a ka yi kan Tattalin Arzikin Jihar a ranar Laraba, 8 ga Oktoba, 2025.
Ya bayyana cewa gwamnati tana ƙoƙari wajen magance matsalar tsaro musamman a yankin Kebbi ta Kudu, inda ta samar da kayan aiki, motocin sintiri da tallafin kuɗi ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
Gwamnan ya kuma yaba wa ƙungiyar dattawan jihar bisa shirya taron tattalin arziki da ke haɗa gwamnati da al’umma wajen inganta ci gaba.
Ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da mayar da hankali kan bangarorin noma, ilimi, lafiya, habakar matasa da ƙananan masana’antu, tare da jaddada cewa ci gaban jihar Kebbi abin haɗin kai ne da ke buƙatar gudunmawar kowa da kowa.