Simas Academy

Simas Academy Internet School For Digital Marketing & Computer Skills In English & Hausa. FREE Courses And Programs To Build Your Career & Business.
(4)

Ta Wacce Hanya Kake Amfani Da AI Wajen Taimakawa Kanka?Bari Kuji, Har Yanzu Da Akwai Waɗanda Suke Adawa Da AI Suke Tunan...
17/10/2025

Ta Wacce Hanya Kake Amfani Da AI Wajen Taimakawa Kanka?

Bari Kuji, Har Yanzu Da Akwai Waɗanda Suke Adawa Da AI Suke Tunanin Ba Zai Iya Yi Musu Komai Ba.

Da Akwai Waɗanda Kuma Sun Tabbatar AI Cigaba Ne, Amma Kuma Ko Kaɗan Basu Amfani Dashi Wajen Bunƙasa Harkokinsu.

A Gurguje, Maganar Gaskiya Idan Kana Daga Cikin Waɗanda Suke Son Gina Career Ɗinsu Ko Kasuwancinsu Kayi Ƙoƙari Ka Koyi AI. Kuma Ka Ringa Amfani Dashi A Al'amuranka Na Kasuwanci.

AI Itace Sabuwar Duniyar Da Muka Jima Muna Jira!
AI Itace Sabuwar Rayuwar Da Muke Mafarkin!

Ya Rage Naka Ka Rungumi Zamani Ka Huta Ko Kuma Dai Akasin Haka.

Daga Simas Academy Makarantarku Ta Zamani 😊

12/10/2025

Kullu Nafsin Za'ikatul Maut, Allah Yayiwa Bilkisu Ahmad Rasuwa, Ɗaya Cikin Jagororinmu Ɓangaren Crypto, Sa'annan Malama A Makarantar Bitkova.

Muna Miƙa Gaisuwar Ta'aziyya Ga Iyalanta, Ƴan Uwanta, Bitkova Digital Hub, Da Kuma Mahmoud Muh'd Sardauna. [Allah Ya Ƙara Haƙuri]

Tabbas Munyi Tashi Babba, Amma Ubangiji Yafi Sonta A Kanmu Baki Ɗaya.

Muna Addu'ar Ubangiji Allah Ya Jikanta Da Rahama, Yasa Aljannah Ce Makomar Ta Tare Da Mu Baki Ɗaya. امين

Simas Academy Daga Bakin ChatGPT 😁 Me Ya Nuna Maka Da Ka Tambaya?
09/10/2025

Simas Academy Daga Bakin ChatGPT 😁 Me Ya Nuna Maka Da Ka Tambaya?

06/10/2025

Video Content Creation Program In Hausa Is Coming Up Next

Who Is In? ☺️

A Kowane Ƙarni Ka Tsinci Kanka, A Kowane Yanayi, A Kowane Environment, Ka Koyi Lissafi Da Ƙirƙira Ta Hanyar Nazari Da Tu...
04/10/2025

A Kowane Ƙarni Ka Tsinci Kanka, A Kowane Yanayi, A Kowane Environment, Ka Koyi Lissafi Da Ƙirƙira Ta Hanyar Nazari Da Tunanin Mutane.

Ilimin Psychology Yana Da Matukar Muhimmanci, Koda Kaɗan Ne Ka Kwashe Ka Zuba A Aljihunka Zai Taimaka Maka Sosai 😊

Dashi Yau Ake Gudanar Da Kasuwanci, Dashi Ake Gudanar Da Siyasar Duniya Dashi Kuma Ake Rainawa Mutane Hankali 🙂

Inda Lissafi Da Tunaninka Ya Ƙare, A Dai-Dai Nan Na Wani Yake Farawa 😅Dalilin Da Yasa Duk Wani Mai Ɓukatar Cigaba A Wann...
04/10/2025

Inda Lissafi Da Tunaninka Ya Ƙare, A Dai-Dai Nan Na Wani Yake Farawa 😅

Dalilin Da Yasa Duk Wani Mai Ɓukatar Cigaba A Wannan Ƙarnin Yake Buƙatar Ya Koyi Ilimin Collaboration 😊

Ilimin Collaboration Zai Baka Damar Yin Haɗaka Da Mutane Kayi Aiki Dasu, Har Ka Cimma Abinda Kake So. Kowa Zai Kawo Idea Ɗinsa, Kowa Zai Baje Kolin Fasaharsa, Kuma Kowa Zai Kawo Baiwarsa Wanda Ba Kowa Yake Dashi Ba.

Ka San Me Sirrin? Kamfanoni Manya-Manya Da Sukayi Nasara A Duniya Suna Da Wannan Culture Ɗin (Al'ada) Ta Collaboration Tsakanin Kowa Da Kowa.

Barkanmu Da Yau Daga Makarantarku Ta Zamani 😊

Saura Watanni 2 Ayi Launching Na Simas Academy ☺️ Inda Kowa Zai Iya Samun Damar Shiga Yayi Karatu.Kafin Ayi Launching Da...
04/10/2025

Saura Watanni 2 Ayi Launching Na Simas Academy ☺️ Inda Kowa Zai Iya Samun Damar Shiga Yayi Karatu.

Kafin Ayi Launching Da Akwai Waɗanda Zasu Samu Kyautar Scholarship, Da Akwai Ɗaliban Farko Da Zasu Samu Kyaututtuka Na Musamman (Kamar Gurbin Aiki Bayan Kammala Karatu Da Sauransu).

👉 Share

04/10/2025

Idan Zamu Zaɓi Hausa Influencers Masu Samar Da Ilimi Mu Basu Award Wanene Kake Ganin Yakamata Ya Kasance A Ciki?

Wannan Shine Mayowa Adeyanju, Yana Murnar Cika Shekaru 21 A Duniya. Labarinsa Abin Ƙarfafa Gwiwa Ne Ga Duk Wanda Yake Tu...
04/10/2025

Wannan Shine Mayowa Adeyanju, Yana Murnar Cika Shekaru 21 A Duniya. Labarinsa Abin Ƙarfafa Gwiwa Ne Ga Duk Wanda Yake Tunanin Ba Zai Iya Ba A Duniyar Internet!

Yana Fama Da Harkar Blogging Kafin Zuwan AI Automation (YouTube). A Can Yake Samun Na Biyan Bukata. Zuwan AI Daga 2024 Ɗin Nan Mayowa Ya Rungumi Harkar Automation Na YouTube.

A Halin Yanzu Dai A Dai-Dai Wannan Lokacin Yaron Nan Ba Iya Kuɗi Ya Tara Ba... Har Mota Ya Sayawa Kansa (Kar Kuma Kayi Tunanin Yahoo Ne) 😅 Shima Ya Shiga Jerin Waɗanda Suke Printing Na Kuɗi Daga YouTube Ta Hanyar Amfani Da AI. Har Ya Kasance Yanzu Haka Mutane Ya Ɗauka Aiki Kuma Yake Investing Na Kuɗaɗen Da Yake Samu Kowane Wata.

Ba Mun Kawo Muku Wannan Labarin Bane Saboda Ku Ji Cewa Lallai Abinda Wane Yayi Dole Sai Kunyi Ba Ko Makamancin Haka! Tunatarwa Ne Cewa 'Internet Ta Kawo Mana Damar Da Babu Babba Babu Yaro, Ko Mace Ko Namiji, Kuma Babu Abinda Zai Iya Dakatar Da Kai Sai Tunaninka!'

Abinda Kake Buƙata Kawai Shine Ka Nemi Ilimin Abin, Ka Sanya Haƙuri Sa'annan Ka Cigaba Da Addu'a Tare Da Jiran Lokacinka ✍️

Allah Ya Taimake Mu Baki Ɗaya. Barka Da Safiya ✍️

Mata Ne Yakamata Ace Sun Fi Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Koyi Ilimin Computer Da Internet. Domin Tabbas Sunfi Buƙata...
03/10/2025

Mata Ne Yakamata Ace Sun Fi Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Koyi Ilimin Computer Da Internet. Domin Tabbas Sunfi Buƙatar Ilimin, Kuma Zai Iya Taimaka Musu Koda A Gidajen Mazajensu Ne!

Muna Ƙira Gareku Mata, Da Ku Dukufa Sosai Wajen Koyon Digital Skills In Sha Allahu Rayuwarku Zata Samu Kyakkyawar Sauyi!

Daga 😊

Ka Koyi Sani A Ɓangarori Daban-Daban Na Fasahar Zamani, Amma Ka Tabbatar Kana Da Ƙwarewa A Ɓangare Guda Wanda Kake Da Ya...
03/10/2025

Ka Koyi Sani A Ɓangarori Daban-Daban Na Fasahar Zamani, Amma Ka Tabbatar Kana Da Ƙwarewa A Ɓangare Guda Wanda Kake Da Yaƙini Watarana Zai Zama Silar Nasarar Ka.

Watarana Sai Labari In Sha Allahu, Allah Yasa Mu Dace 😊

Lokaci Zai Kawo Mu Da Duk Wani Matashin Da Bai Koyi Wani Digital Skill Ba Zaiyi Da-Na-Sani. Domin Za'a Barshi A Baya Kot...
01/10/2025

Lokaci Zai Kawo Mu Da Duk Wani Matashin Da Bai Koyi Wani Digital Skill Ba Zaiyi Da-Na-Sani. Domin Za'a Barshi A Baya Kota Ina ✍️

Address

Jimeta
Yola

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Simas Academy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Simas Academy:

Share