28/11/2022
DA DUMI DUMI ||
Daga shafin Adamawa Press Team
kotu ta mayarwa Binani tikitin takarar gwamna na APC a Adamawa
babban kotun daukaka Kara Wanda ke birnin Yola fadar jihar Adamawa ta maidawa da 'yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyar APC sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani tikitin takarar ta a matsayin gwamnan jihar Adamawa
Bayan sauraron kowani bangare, a karshe dai Kotun tayi watsi da karar da Mallam Nuhu Ribadu yashigar sanan ta maidawa senata Aisha Binani tikitin takarar ta kuma ta umarci hukumar Zabe da ta gaggauta maida Sunan Aisha Binani cikin 'yan takarkarun gwamna a Adamawa.