28/09/2025
Baba Joda Smart Agric ta Horar da Manoma Kan Noman Ganyayyakin Tafarnuwa, Citta da Tallafin Shirin ADAS
Kungiyar Baba Joda Smart Agric Multi-Purpose ta gudanar da horo na aikace ga manoma kan noman ganyayyakin tafarnuwa, citta ta hanyar amfani da dabarun noma na zamani, bayan samun tallafi da tabbacin siye daga Shirin (ADAS-P).
Horon na kwanaki biyu da aka gudanar a ƙarƙashin shirin ƙungiyar don bunƙasa noma na zamani, ya samu mahalarta da ke son rungumar hanyoyin noma masu dorewa da ke ƙara yawan amfanin gona tare da tabbatar da samun kasuwa.
Wannan aikin ya biyo bayan babban shirin ADAS-P na noma wanda Mataimakiyar Gwamnan Jihar Adamawa ta kaddamar a Benue Valley Farms, Fufore.
Jami’an ADAS-P tare da tawagar sashi na daya sun halarci horon, wanda hakan ya ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirin da ƙungiyoyin manoma na cikin gida.
A cewar masu shirya taron, mayar da hankali kan tafarnuwa, citta da kurkum ya samo asali ne daga ƙarfin tattalin arzikinsu da kuma ƙaruwa bukatarsu a kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.