GABAS MEDIA

GABAS MEDIA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from GABAS MEDIA, TV Channel, Yola.

08/08/2026

Takai Tattun Labaran GABAs MEDIA Tareda Muhammad Aminu Ganye.

Ayi Sauraro Lafiya.

Wani jami'in Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), Bashir Umar, ɗan asalin Jihar Adamawa, ya yabu bayan ya mayar da kuɗi ...
06/08/2026

Wani jami'in Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), Bashir Umar, ɗan asalin Jihar Adamawa, ya yabu bayan ya mayar da kuɗi har Yuro €37,000 da ya tsinta ga mamallakinsu.

Rahotanni sun ce Bashir Umar ya tsinci kuɗin ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano a ranar Lahadi, inda ya miƙa su ga mamallakinsu ba tare da ɓata lokaci ba.

Lamarin ya samu yabo daga jama'a, inda da dama s**a bayyana abin a matsayin babban abin koyi na riƙon amana da gaskiya.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

Kungiyar Adamawa Media Political Program Presenters' Forum (AMPPF) ta gudanar da babban zaɓenta na shugabanci, inda ta z...
06/08/2026

Kungiyar Adamawa Media Political Program Presenters' Forum (AMPPF) ta gudanar da babban zaɓenta na shugabanci, inda ta zaɓi Abdulwahab Aliyu na Pulaaku FM, Yola a matsayin sabon Shugaban ƙungiyar na wa'adin shekaru biyu.

An gudanar da zaɓen ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Amintattu (BOT), Alhaji Musa Sheleng, tare da halartar sauran mambobin kwamitin, ciki har da tsohon Shugaban ƙungiyar, Alhaji Yusuf Modibbo Zubairu.

Bayan kammala zaɓen, an tabbatar da Abdulwahab Aliyu a matsayin sabon shugaban AMPPF, wanda zai jagoranci ƙungiyar bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta.

Ƙungiyar ta yaba da irin gudunmawar da tsohon shugaba, Alhaji Yusuf Modibbo Zubairu, ya bayar wajen ci gaban ƙungiyar, tare da yi masa fatan alheri a ci gaba da ayyukansa.

Hakazalika, ƙungiyar ta yi kira ga dukkan mambobinta da su bai wa sabon shugaban cikakken haɗin kai da goyon baya domin cimma manufofin ƙungiyar da bunƙasa aikin gabatar da shirye-shiryen siyasa da aikin jarida a Jihar Adamawa.

An fitar da wannan sanarwa ne domin sanar da manema labarai da sauran al'umma.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

Ana zargin wani jami'in soja da harbe wani matashi a garin Mubi da ke Jihar Adamawa.'Yan uwan matashin sun bayyana cewa ...
06/08/2026

Ana zargin wani jami'in soja da harbe wani matashi a garin Mubi da ke Jihar Adamawa.

'Yan uwan matashin sun bayyana cewa jami'in sojan ya bi matashin har cikin gida kafin ya harbe shi, inda s**a ce ba su san wani laifin da ya aikata da zai jawo hakan ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya jawo fargaba da alhini a tsakanin mazauna yankin, yayin da ake sa ran hukumomin da abin ya shafa za su gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

Sabbin shugabannin Nigeria Union of Journalists (NUJ), NAS FM Chapel, sun kai ziyarar sada zumunci ga mahukuntan NAS FM ...
06/08/2026

Sabbin shugabannin Nigeria Union of Journalists (NUJ), NAS FM Chapel, sun kai ziyarar sada zumunci ga mahukuntan NAS FM Yola domin gabatar da kansu a hukumance tare da ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙungiyar da mahukuntan gidan rediyon.

Babban Manajan NAS FM Yola, Hajiya Victoria Yakubu, tare da sauran jami'an gudanarwa ne s**a tarbi tawagar.

Da yake jawabi, Shugaban NUJ NAS FM Chapel, Kwamared Dominic Yohanna, ya bayyana godiyarsa ga wanda ya kafa NAS FM, Dr. Mahmood Halilu Ahmed, MNI, bisa samar da damar kafa reshen ƙungiyar a gidan rediyon.

Ya kuma yaba wa Hukumar Gudanarwar NAS FM ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ya'u Umar Babayi da Babbar Manaja, Hajiya Victoria Yakubu, saboda irin goyon bayan da s**a bayar wajen tabbatar da NAS FM ta zama cikakkiyar mamba ta Majalisar NUJ ta Jihar Adamawa.

Kwamared Dominic Yohanna ya tabbatar da cewa sabbin shugabannin za su ba da fifiko ga bunƙasa NAS FM tare da kare muradun mambobin ƙungiyar. Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙungiyar da mahukuntan gidan rediyon bisa mutunta juna, haɗin kai da ƙwarewa.

A nata jawabin, Babbar Manajan NAS FM Yola, Hajiya Victoria Yakubu, ta tabbatar wa sabbin shugabannin NUJ cikakken goyon bayan mahukuntan gidan rediyon domin samun nasarar gudanar da ayyukansu.

Haka kuma, a saƙonnin fatan alheri daban-daban, Mubarak Alihu Saboyaro, Bello Abdullahi, da Modibbo Zubairu sun taya sabbin shugabannin murna tare da yi musu alƙawarin ba su cikakken goyon baya.

An bayyana ziyarar a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sabbin shugabannin NUJ da mahukuntan NAS FM Yola domin ci gaban gidan rediyon.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

Hamshaƙin attajirin Najeriya kuma mamallakin kamfanin mai na Oriental Energy Resources, Muhammadu Indimi, ya bayyana ani...
06/08/2026

Hamshaƙin attajirin Najeriya kuma mamallakin kamfanin mai na Oriental Energy Resources, Muhammadu Indimi, ya bayyana aniyarsa ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin wata kotu da ta umarce shi da ya biya tagwayen 'ya'yansa mata dala miliyan 43.51, sakamakon takaddamar rabon ribar hannun jari.

Rikicin ya samo asali ne daga saɓanin da ya kunno kai kan haƙƙin rabon ribar kamfanin, inda tagwayen 'ya'yan attajirin s**a shigar da ƙara suna neman a biya su ribar da suke ganin ta dace da su.

Rahotanni sun nuna cewa Indimi na shirin kalubalantar hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara, domin kare muradunsa tare da neman sake duba hukuncin da kotun ta yanke.

Ana sa ran ci gaba da shari'ar zai ƙara fito da cikakkun bayanai kan takaddamar da ke tsakanin attajirin da 'ya'yansa.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

Rahotanni sun ce Sojojin Saman Najeriya, ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, sun kai wani hari kan wata mafakar da ake zargin...
06/08/2026

Rahotanni sun ce Sojojin Saman Najeriya, ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, sun kai wani hari kan wata mafakar da ake zargin 'yan ta'adda ke amfani da ita a kusa da Chiralia da ke Jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama, harin ya gudana ne a ranar Talata bayan samun bayanan sirri da s**a nuna cewa mayakan sun sake komawa yankin domin ci gaba da ayyukansu.

Rahoton ya bayyana cewa yankin Chiralia na cikin dazuzzuka masu wahalar shiga, kuma 'yan ta'adda sun daɗe suna amfani da shi a matsayin mafaka saboda yanayinsa da ke ba su damar ɓoyewa.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin sojin Najeriya ba su fitar da cikakken bayani kan sakamakon harin ba.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa tun bayan hawansa mulki bai taɓa tsoma baki cikin ayyukan Hukumar Yaƙi...
06/08/2026

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewa tun bayan hawansa mulki bai taɓa tsoma baki cikin ayyukan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da sauran hukumomin bincike ba, domin ba su damar gudanar da aikinsu cikin cikakken 'yanci.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya bayyana cewa wani mataki da EFCC ta ɗauka ya ba shi kunya, ba wai saboda matakin kansa ba, sai dai saboda lokacin da aka ɗauki matakin.

Shugaban ya ce duk wani mataki da hukumomin gwamnatin tarayya s**a ɗauka, al'umma kan danganta shi da shugaban ƙasa, ko da kuwa ba shi da masaniya ko sa hannu a aiwatar da shi.

Majiyar: GABAs MEDIA
Kabir Usman Gograjatau

06/08/2026
01/08/2026

Hubbirde Fulfulde Media Presenters Nde Nigeria lisal Adamawa Less Ardugal Comrade Yusuf Ishaq Buba Yahri Gilla Ema Samdinore Ha komishinaajo hukuma pamari diwal Adamawa Alh Ibrahim yayaji mijin yawa.

Komicinajo on mani Yetti nden sarwi hubbirde Fulfulde media presenters association lisal Adamawa, ha dow tidal ema kautal h**e hakkude bibbe hubbirde den waddan jahal yeso bosugal fake ummatore nofoti.
👇👇👇

Address

Yola

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GABAS MEDIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category