26/12/2025
AMURKA TA KADDAMAR DA GAGARUMIN HARI A NIGERIA
A daren jiya, Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kaddamar da wani gagarumin hari mai tsanani kan ‘yan ta’addan ISIS a Jihar Sokoto, da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
A cewar Trump, harin ya shafi mafakar ‘yan ta’addan ISIS ne a Sokoto, inda ya zarge su da kai hare-hare tare da kashe Kiristoci a Najeriya.
Ya gargade su cewa idan ba su dakatar da irin wadannan ayyukan ta’addanci ba, za su ci gaba da fuskantar mummunan sakamako kamar wanda s**a fara gani a wannan daren.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa wannan hari wani irin aiki ne da ƙasar Amurka kaɗai ke da ƙarfin aiwatarwa, yana mai jaddada cewa Amurka ba za ta bari tsattsauran ra’ayin ta’addancin Musulunci ya samu ƙarfi ko ya bazu a Najeriya ba.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta yi amfani da sansanin sojojin ruwanta na USS Paul Ignatius, da ke Rota a ƙasar Spain, inda ta harba wani ƙaƙƙarfan makami mai linzami mai saurin gaske, wato Tomahawk Missile, zuwa jihar Sokoto.