Gaskiya Jari

Gaskiya Jari Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gaskiya Jari, Media, Gyallesu T/dawa zaria, Zaria.

Ana kiyasin wutar data afkawa birnin Los Angeles dake jihar California ta kasar Amurka Kona dukiyar data zarce Dala bili...
11/01/2025

Ana kiyasin wutar data afkawa birnin Los Angeles dake jihar California ta kasar Amurka Kona dukiyar data zarce Dala biliyan 57,000,000,000 kimanin Naira trillion 94,000,000,000,000 a kuɗin Nigeria, cikin Awanni 48 da farawar ta.

Tawagar ƴan sintiri a jihar Sokoto ta ce ta kuɓutar da mutum 63 daga hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fa...
10/01/2025

Tawagar ƴan sintiri a jihar Sokoto ta ce ta kuɓutar da mutum 63 daga hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, a jihar mai fama da matsalar ayyukan ƴan bindiga.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun Garba Mohammed, mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar ta ce tawagar ta ƙunshi jami'an ƴansanda da jami'an tsaro ƙarƙashin gwamnatin jihar Sokoto.

Bayanin ya bayyana cewa an kuɓutar da mutanen ne a tsawon kwana huɗu, daga ranar Lahadin da ta gabata.

Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Haka nan a baya-bayan nan an samu ɓullar wata ƙungiyar ƴan bindiga da ake kira Lakurawa.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta tsananta ayyukan yaƙar ƴan bindiga tun bayan ɓullar ƙungiyar ta Lakurawa a ƙarshen shekarar da ta gabata.

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!Abokina Barr. Hamza Nuhu Dantani ✍️Wato Labarin Yarinyar nan da  wani mara imani yayi mata...
09/01/2025

HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!

Abokina Barr. Hamza Nuhu Dantani ✍️

Wato Labarin Yarinyar nan da wani mara imani yayi mata Fyade na da matukar tayar da Hankali duk cewa yanzu haka case din yana Gaban Kotu!

Wato a Zantawar da mukayi da iyayen yarinyar da kuma Shafa’atu wacca itace ta fara yiwa yarinyar video ta fada min abinda ya tayar min da hankalina matuka.

Ashe Wanda Ake Zargi ya dade da yiwa yarinyar Lalata, kuma tun tana Shekara 8 yake mata mummunar aika aika da farji da kuma ta dubura ( wa'iyazubillah), da kuma zubar da kazantarsa a bakinta da tilasata mata hadiyewa.

Ashe ya jima yana yi mata barazana idan har ta sake ta fadawa iyayenta zai kashe ta tare da gana mata azaba.

Ashe Makwabta ne da yarinyar Kuma iyayen basu da karfi, akan case din nema har Allah Ya yiwa mahaifinta rasuwa, har ya saka Mahaifiyar yarinyar zuwa Asibitin murtala dake Kano

Yarinyar Har yanzu ko kwanciya bata iyayi saboda zafin ciwon, sai dai ta dan ajiye kanta a kafadar uwarta ta samu ta dan huta, kullun suna cikin zullumi basu da wanda zai taimake su.

Sai da Allah ya kawo Baiwar Allah Shafa’atu Muhammad Adam ta Dauki video ta saka a shafinta har aka dinga taggin namu ni da Abba Hikima da wasu masu Fafutuka.

Likitocin da s**a dubu yarinyar s**a ce, tunda suke basu taba ganin lalata da illa irin yadda aka yiwa wannan baiwar Allah ba. S**a ce ko da ma ta samu Sauki zaiyyi wuya ta samu haihuwa ko juna biyu saboda abun ya taba mata Mahaifa da hanjinta.

A Yanzu dai Mai Girma Gwaman Jahar Jigawa tare da mai Dakinsa sun aika da tawaga zuwa Asibitin murtala har ma an turata zuwa Mal Aminu Kano Kano Teaching Hospital don yi mata aiki tare da Jagoranci Dr Hauwa Babura wanda muka magantu da ita sosai

Insha Allah Zamu bibiyi wannan case din nida Abokina Abba Hikim, Insha Allah sai mun tabbatar da anyi mata adalci

Nigeria’s Secret Police DSS Reportedly Arrests Traditional Worshipper In Oyo For Alleged Qur'an Burning | Sahara Reporte...
08/01/2025

Nigeria’s Secret Police DSS Reportedly Arrests Traditional Worshipper In Oyo For Alleged Qur'an Burning | Sahara Reporters

Jami'an tsaron farin kaya na DSS sun tabbatar da k**a wani mutun mai bautar addinin gargajiya (traditionalist) a bisa zargin sa da kona Alqur'ani mai girma, shi dai wanda a ke zargi dan jahar Oyo ne

Sahara reporters ne ta riwaito

Shugaban Amurka, Joe biden ya ayyana dokar ta ɓaci a birnin na Los Angeles da ke jihar California bayan da aka faɗa ciki...
08/01/2025

Shugaban Amurka, Joe biden ya ayyana dokar ta ɓaci a birnin na Los Angeles da ke jihar California bayan da aka faɗa cikin yanayi na tashin hankali sak**akon mummunar gobarar daji.

Gobarar ta cinye kusan fili, eka 3,000 yayin da lantarki ta katse sannan aka fara rufe makarantu.

A yanzu hukumomi na ci gaba da aikin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Zagin shugaban mulkin sojan kasar Guinea Conakry Janar Mamady Doumbouya ya janyo wa dan adawa Aliou Bah daurin shekaru b...
07/01/2025

Zagin shugaban mulkin sojan kasar Guinea Conakry Janar Mamady Doumbouya ya janyo wa dan adawa Aliou Bah daurin shekaru biyu

DCL Hausa

ISWAP Terrorists Raid Civilian Joint Task Force Office In Borno, Hours After Attack On Nigerian Army BaseJanuary 7, 202...
07/01/2025

ISWAP Terrorists Raid Civilian Joint Task Force Office In Borno, Hours After Attack On Nigerian Army Base



January 7, 2025

News

The sources added that the terrorists razed many buildings and military operational vehicles during the attack that lasted over two hours.

The Islamic State West Africa Province (ISWAP) militant group has claimed responsibility for a recent attack on a Civilian Joint Task Force base in Borno State.

According to a statement released by the group, they seized various weapons, including 7.62x39mm AK magazines and ammunition, during the raid. The statement also included photos showing ISWAP members firing indiscriminately at the base.

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, wadda tsohuwar matar Sani Musa Danja ce, ta bayyana hakan cikin wani bidiyo d...
07/01/2025

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, wadda tsohuwar matar Sani Musa Danja ce, ta bayyana hakan cikin wani bidiyo da ta wallafa.

A cikin bidiyon ta bayyana yadda mata ke shiga mawuyacin hali bayan mutuwar aurensu. Ta shawarci mata da su kasance masu haƙuri a gidajensu na aure tare da gujewa duk wani abu da ka iya kawo musu ɓaraka da mazajensu.

Ta yi gargaɗin cewa babu komai a rayuwar zawarci sai tarin baƙin ciki da da-na-sani.

Idon mikiya ce ta riwaito

MASHA ALLAHGaskiya ban taba ganin Gwamnan da ya san darajar mutane wanda bashi da girman kai da wulakanta mutanen k**ar ...
07/01/2025

MASHA ALLAH

Gaskiya ban taba ganin Gwamnan da ya san darajar mutane wanda bashi da girman kai da wulakanta mutanen k**ar Maigirma Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ba

Akwai wasu da na sani da suke tare da shi cikin mukarrabansa halinsu sam ba irin nasa bane, sun sa girman kai da nuna isa maimakon suyi koyi da Maigidansu

Abba yana ta fuskantar cin kafa da dunduniya daga wasu miyagun 'yan siyasar Abuja, amma hakan bai sanyaya masa gwiwa wajen kokarin sauke nauyin shugabancin al'ummar Kano da ya rataya a wuyansa ba

Kanawa ku rike Abban ku da kyau, ba zakayi nadamar zamansa Gwamna Insha Allah

Allah Ka kara wa rayuwarsa da namu albarka

Daga Datti Assalaffy

Hasbunallahu Wa Ni'mal Wakeel 😭😭😭😭😭 Inna ilaihim Wa Inna ilaihim Raji'una Allahu Akbar 😭😭  Yesterday, during the isha'i ...
07/01/2025

Hasbunallahu Wa Ni'mal Wakeel 😭😭😭😭😭 Inna ilaihim Wa Inna ilaihim Raji'una Allahu Akbar 😭😭


Yesterday, during the isha'i He is prayer, kidnappers Attack There location Camp in Kaita Village Tsafe Zamfara

Very Well i know this My friend A lover of people, a patient, a religious person, a fearing Almighty the person, who does not play with prayer. Day and Night

May Almighty Allah have Mercy On Him
May Almighty Allah Accept your Shadat

Your little child that you Live May He Bless His life Amen ya Allah Very Sad 😭😭😭😭😭😭

DAARUL HADEETH SALAFIYYAH Marigayi Sheikh Albaniy Zaria ya dauki dukiyarsa mai yawa ya gina wannan cibiya ta ilimi don h...
07/01/2025

DAARUL HADEETH SALAFIYYAH

Marigayi Sheikh Albaniy Zaria ya dauki dukiyarsa mai yawa ya gina wannan cibiya ta ilimi don hidima wa addinin Allah a lokacin da shi da iyalansa suna gidan haya

Yau Malam baya raye, wannan cibiya ta fada hannun wadanda manufarsu ba iri daya bane da Malam

Ubangiji Allah Ka jikan Sheikh Albaniy, Ka kare masa makarantarsa daga sharrin 'yan duniya

Address

Gyallesu T/dawa Zaria
Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiya Jari posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category