HNN Hausa

HNN Hausa HNN News Muryar Al'umma, Ku kasance damu domin Samun Ingantattun Labarai da Rahotanni a fadin duniya

Wasu da ake zargin ‘yan fa-shi da ma-kami ne s**a ka-she wani jami’in ‘yan sandan Najeriya mai suna Insfekta Sunday Baba...
25/04/2024

Wasu da ake zargin ‘yan fa-shi da ma-kami ne s**a ka-she wani jami’in ‘yan sandan Najeriya mai suna Insfekta Sunday Baba a yayin wani fa-shi da ma-kami a Rumuolumeni da ke jihar Ribas a daren Laraba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ce ta tabbatar da wannan bayanin ta shafin ta na dandalin sada zumunta.

Buni ya mayar da martani ga kazamin fada da ya faru tsakanin sojoji da mahaya KekeGwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya y...
15/04/2024

Buni ya mayar da martani ga kazamin fada da ya faru tsakanin sojoji da mahaya Keke

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi kira da a kara samun daidaito tsakanin sojoji da fararen hula a Gashu’a.

Buni ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake mayar da martani kan wata arangama tsakanin sojoji da mahaya Keke NAPEP a ranar Lahadi a garin Gashu’a wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, tare da jikkata da dama.

Ya bayyana da cewa abin takaici ne yadda irin wannan lamari ke faruwa a daidai lokacin da jihar ke samun zaman lafiya a fadin jihar.

"Abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne yadda ake asarar rayuka a cikin wani yanayi da za a iya kaucewa," in ji shi.

Yanzu-yanzu: FG ta amince da ranar Alhamis a matsayin karin hutu don bikin Eid-El-Fitr Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ay...
09/04/2024

Yanzu-yanzu: FG ta amince da ranar Alhamis a matsayin karin hutu don bikin Eid-El-Fitr

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Alhamis 11 ga Afrilu, 2024 a matsayin karin hutu a hukumance domin gudanar da bikin Eid-El-Fitr na bana.

08/04/2024

BAYANI AKAN ZAKKAR FIDDA KAI (ZAKÃTUL FITR)

Tare da: Dr. Jabir Sani Maihula (Hapizahullah)

Kungiyar SERAP, ta kaddamar da shari’a a kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan rashin kiran da aka yi wa...
07/04/2024

Kungiyar SERAP, ta kaddamar da shari’a a kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan rashin kiran da aka yi wa Sanatan Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi.

SERAP ta kuma kai karar Akpabio bisa gazawarsa wajen mika takardar kasafin kudin ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, domin gurfanar da shi gaban kuliya.

Ningi ya kara da cewa ba a iya gano Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.

'Yan sanda sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina
06/04/2024

'Yan sanda sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Jamiyyar NNPP ta sauya tambarin ta (Logo) daga kayan Marmari zuwa hoton littafi da hula, tare kuma da sauya Taken Jamiyy...
05/04/2024

Jamiyyar NNPP ta sauya tambarin ta (Logo) daga kayan Marmari zuwa hoton littafi da hula, tare kuma da sauya Taken Jamiyyar zuwa Education for All.

Hakan na zuwa ne bayan wani taro da Jamiyyar ta gudanar na yan majalisar zartarwa na Ƙasa a dakin taro na A-Class dake Maitama babban birnin tarayya Abuja.

A gobe ne ake saka ran Jamiyyar zata gudanar da taro na kaddamar da shugabancin jam'iyyar na Ƙasa, kamar yadda wakilinmu Jabir Ali Danabba ya rawaito mana.

An bukaci shugabannin Afirka da su yi koyi da Faye, yayin da shugaban Senegal ke bayyana kadarorinsa a bainar jama'aAn b...
03/04/2024

An bukaci shugabannin Afirka da su yi koyi da Faye, yayin da shugaban Senegal ke bayyana kadarorinsa a bainar jama'a

An bukaci shugabannin Afirka da su yi koyi da sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ta hanyar bayyana kadarorinsu a bainar jama'a.

Wata kungiyar farar hula, The Resource Center for Human Rights and Civic Education, CHRICED, ce ta yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata domin bikin rantsar da Faye a matsayin shugaban kasa.

Nasarawa za ta ba da gudummawa ga asusun tarayya ta hanyar Noma, Ma'adinai - Gov Sule Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nas...
01/04/2024

Nasarawa za ta ba da gudummawa ga asusun tarayya ta hanyar Noma, Ma'adinai - Gov Sule

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce dabarun gwamnatinsa shi ne karfafa gudummawar da jihar ke bayarwa ga asusun tarayya ta hanyar bunkasa harkar noma da ma’adinai.

HOTO MAI SOSA ZUCIYA: 'Ya Ce Ga Daya Daga Cikin Sojojin Nijeriya Da Aka Ķàśhe A Jihar Delta
30/03/2024

HOTO MAI SOSA ZUCIYA: 'Ya Ce Ga Daya Daga Cikin Sojojin Nijeriya Da Aka Ķàśhe A Jihar Delta

Duk manufofin gwamnati Tinubu alama ce na raba Najeriya ne, ba hada kan Najeriya ba, wannan dalilin yasa Tinubu ya ɗako ...
28/03/2024

Duk manufofin gwamnati Tinubu alama ce na raba Najeriya ne, ba hada kan Najeriya ba, wannan dalilin yasa Tinubu ya ɗako na uku a kasa daga yankin inyamurai don tabbatar da manufarsa ta Raba kasa. Kowa ya sani cewa, Akpabio yana da zarge-zarge da ake masa na cin hanci da rashawa amma duk da haka ya dako shi ya bashi mukamin shugaban majalisar Dattawan Najeriya.

Kowa yaga yadda ake kwashe wasu muhimman ma'aikatu daga Arewacin Najeriya ana kaisu kudancin kasa, kamar wasu sashi na babban Bankin kasa, da wasu sashi na zirga-zirgar jirgin saman Najeriya.

Idan ba haka ba taya zai zama ana cikin zaman lafiya zai kwashe muhimman wurare ya mayar da su yankinsa duk da cewa, ba kaunarsa akeyi ba a kudancin kasar. Inji Shu'aibu Mungadi.

Ya bayyana haka ne a wani shirin talabijin na farin wata da ake gabatarwa a gidajen Rediyo Vision FM kwanakin baya.

Tsadar Rayuwa: Ƴan Najeriya na cikin ɓacin rai yayin da yawancin mutane  ke mutuwa don neman abin da za su ci'Yan Najeri...
27/03/2024

Tsadar Rayuwa: Ƴan Najeriya na cikin ɓacin rai yayin da yawancin mutane ke mutuwa don neman abin da za su ci

'Yan Najeriya da dama ne s**a rasa rayu-kansu a cikin 'yan kwanakin da s**a gabata yayin da suke fafutukar cin gajiyar kayan abinci da gwamnati ke rabawa a yayin da ake fama da yunwa a kasar.

Address

Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share