HNN Hausa

HNN Hausa Ku Kasance Tare Damu Domin Samun Ingantattun Labaran Cikin Gida Nigeria Dama Wasu Sassa Na Duniya

PHOTONEWS:Katsina Exco Holds Valedictory Session as Head of Service Bawale, Others Bows OutKatsina State Executive Counc...
12/08/2026

PHOTONEWS:

Katsina Exco Holds Valedictory Session as Head of Service Bawale, Others Bows Out

Katsina State Executive Council has held a valedictory session in honour of the Head of the Katsina State Civil Service, Alhaji Falalu Bawale, following the completion of his 35 years of service. His tenure as Head of Service ends this August.

The valedictory session was held today shortly after the commencement of the 13th State Executive Council meeting at the Upper Chamber of Muhammadu Buhari House, Government House, Katsina, chaired by Governor Dikko Umaru Radda.

Other Council members honoured during the session included Hon. Ya’u Ahmed Nowa, Funtua/Dandume Federal Constituency; Hon. Mustapha Kanti Bello, Kankia/Kusada/Ingawa Federal Constituency; Hon. Jamila Abdu Maigoyo, Mani/Bindawa Federal Constituency; and Hon. Hamza Suleiman Faskari, Kankara/Faskari/Sabuwa Federal Constituency.

Also honoured was Hon. Aminu Lawal Maye Jibia, who contested for the Katsina State House of Assembly.

The farewell session provided an opportunity for members of the Council to appreciate the contributions of the outgoing members to the administration and wish them success in their future endeavours.

Following the valedictory session, the Council continued with its 13th State Executive Council meeting to deliberate on key matters concerning the development and progress of Katsina State.

NYCN Ta Zagaya Kananan Hukumomi 30 Na Jihar Katsina Don Tabbatar Da Shugabanninta Wanda Zasu Wakilci Matasan a Yankunan ...
05/08/2026

NYCN Ta Zagaya Kananan Hukumomi 30 Na Jihar Katsina Don Tabbatar Da Shugabanninta Wanda Zasu Wakilci Matasan a Yankunan Nasu

Majalisar Matasa ta Kasa (NYCN) Reshen Jihar Katsina ta samu nasarar gudanar da bikin tabbatar da shugabannin kananan hukumomi 30 cikin 34 na jihar karkashin jagorancin Hon. Yusuf Abubakar papa.

An gudanar da wannan shiri tare da cikakken goyon baya daga Gwamnatin Jihar Katsina, wanda ya taimaka wajen tabbatar da sahihanci da ingancin tsarin.

Shugabannin NYCN na jihar sun bayyana cewa shirin na da nufin ƙarfafa shugabancin matasa a matakin ƙananan hukumomi, inganta haɗin kai, da kuma samar da ingantaccen tsarin gudanar da harkokin majalisar domin ci gaban matasan jihar.

Sun yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa irin goyon bayan da gwamnatin sa ta bayar wajen tabbatar da nasarar wannan shiri.

Sun kuma gode wa hukumomin tsaro, masu ruwa da tsaki, da dukkan matasan da s**a ba da haɗin kai wajen gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali.

NYCN ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar da sauran abokan hulɗa domin inganta rayuwar matasa tare da ƙarfafa su su taka rawar gani wajen ci gaban Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.

NYCN Ta Sanar Da Lokacin Tantance Masu Neman Takarar Zaɓen Ƙananan Hukumomi na 2026Kwamitin Zaɓe Mai Zaman Kansa na Ƙung...
29/07/2026

NYCN Ta Sanar Da Lokacin Tantance Masu Neman Takarar Zaɓen Ƙananan Hukumomi na 2026

Kwamitin Zaɓe Mai Zaman Kansa na Ƙungiyar Matasan Najeriya (NYCN) ya sanar da cewa za a gudanar da tantance masu neman takarar shugabancin ƙananan hukumomi na shekarar 2026 a ranakun Laraba 29 da Alhamis 30 ga Yuli, 2026.

Kwamitin ya buƙaci dukkan masu neman takara da su halarci tantancewar tare da kwafi uku (3) na takardun da ake buƙata domin tabbatar da cancantarsu.

Takardun sun haɗa da:

1. Highest Level Qualification
2. O Level Certificate
3. Indigene Certificate
4. NIN
5. Primary Certificate
6. Birth Certificate
7. Receipt of Nomination Form
8. 1 passport

KWAMITIN ZAƁEN ƘANANAN HUKUMOMI NA NYCN KATSINA YA ƘARA WA’ADIN SAYAR DA FOM DA VALIDATION ZUWA 27 GA YULIKwamitin Gudan...
20/07/2026

KWAMITIN ZAƁEN ƘANANAN HUKUMOMI NA NYCN KATSINA YA ƘARA WA’ADIN SAYAR DA FOM DA VALIDATION ZUWA 27 GA YULI

Kwamitin Gudanar da Zaɓen Ƙananan Hukumomi na Ƙungiyar National Youth Council of Nigeria (NYCN) reshen Jihar Katsina ya sanar da ƙarin wa’adin sayen fom na takara tare da aikin Validation/Revalidation na ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin majalisar.

A cewar kwamitin, an tsawaita wa’adin ne zuwa ranar Litinin, 27 ga Yuli, 2026, domin bai wa duk masu sha’awar tsayawa takara da kuma ƙungiyoyin da ba su kammala rajista ko sabunta rajistarsu ba damar cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata.

Kwamitin ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatun da aka samu daga masu ruwa da tsaki, tare da manufar tabbatar da cewa kowa ya samu damar shiga wannan tsari cikin adalci da gaskiya.

Haka kuma, kwamitin ya miƙa saƙon godiya ga matasan Jihar Katsina bisa irin yadda s**a nuna himma, jajircewa da haɗin kai tun farkon fara gudanar da wannan tsari, yana mai bayyana fatan cewa za a ci gaba da gudanar da zaɓen cikin lumana, gaskiya da adalci.

NYCN Reshen Jihar Katsina Ta Ƙaddamar da Sayar da Fom ɗin Tsayawa Takarar Zaɓen Ƙananan Hukumomi na 2026Majalisar Matasa...
07/07/2026

NYCN Reshen Jihar Katsina Ta Ƙaddamar da Sayar da Fom ɗin Tsayawa Takarar Zaɓen Ƙananan Hukumomi na 2026

Majalisar Matasan Nijeriya (NYCN) reshen Jihar Katsina ta ƙaddamar da sayar da fom ɗin tsayawa takarar zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi na shekarar 2026.

An gudanar da ƙaddamarwar a Babban Dakin Taro na Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Jihar Katsina, wanda kuma aka ayyana a matsayin cibiyar hukuma ta sayar da fom ɗin ga masu sha’awar tsayawa takara.

Majalisar ta buƙaci duk masu sha’awar shiga zaɓen da su bi ƙa’idoji da jadawalin da Kwamitin Zaɓe (IELECO 2026) ya fitar, tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da sanar da jama’a duk wasu ƙarin bayanai a kan lokaci.

23/06/2026

Wannan na a Matsayin katin Gayyata ga duk wanda Kati be iso Gareshi ba.

Hawan Angunchi za'ayi shi a Ranar Lahadi 28 ga watan yuni 2026, Allah ya bada ikon zuwa Ameen Summa Ameen..

22/06/2026

Yan uwa na al’ummar Jihar Katsina,

Bamu da wanda yafi cancanta ya jagorance mu yanzu kamar *Senator Ahmad Babba Kaita*.
Shi ne zabin talakawa. Shi ne muriyar marar murya.

Ba ya magana da manyan kalamai kawai. Yana aiki da adalci da gaskiya.
Yana ganin rayuwar talaka ne don ta inganta.

Ahmad Babba Kaita ya san ciwonmu.
Ya san yunwa, ya san rashin tsaro, ya san yadda makaranta da asibiti s**a zama abin wahala ga talaka.

Saboda haka zabinsa ba na siyasa ba ne kawai. Zabi ne na rayuwa.
Zabi ne na cewa: “Ya isa cin amanar talakawa da yaudara da munafunci. Lokaci ya yi da za a yi adalci.”

Katsina ta cancanci shugaba mai jin tausayi.
Katsina ta cancanci wanda zai tsaya da gaskiya ko da duka duniya ta tsaya masa.
Wannan shugaban shine *Senator Ahmad Babba Kaita*.

Muna nan tare da shi, ba don komai ba sai don gobe ta fi yau kyau.

✍️ *Hon.Engr Musa Abdulmumini*
_(Garkuwan Talakawa)_
_Chairman, Katsina Local Government Council In Sha Allah_

02/06/2026

Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un

Allah yayi ma Abdul'aziz Mustapha [Abba] rasuwa sakamakon harbin bindiga da akai mai, ɗan shekaru 21.

Ya haɗu da ajalin shi ne bayan fitowa daga gida dai dai lolacin da akai harbin.

Abba mazaunin Kano a cikin Ƙaramar Hukumar Dala a Titin Goburawa-Ɗan Dishe dai dai Sinima kusa da Masallacin Juma'a na Ƴan Izala.

Ana zargin Ƴan Sanda dake a yankinne s**ai harbin sakamakon wani samame da s**a kai a yankin.

Anyi Jana'izar shi kamar yadda Addinin Islama ya tanada.

Bayan haka, mazauna yankin sun tabbatar cewa, mutum biyu ne wannan iftila'in ya rutsa da su, a inda tuni sun riga mu gidan gaskiya.

Muna addu'ar Allah SWA yaji kan su da rahma, in tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani, ameeen.

Duk ƙoƙarin da mukai na jin ta bakin Mai Magana da Yawun Ƴan Sanda na Jihar Kano abun yaci tura, dudda kira da saƙon karta kwana da muka tura mai.

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr) Abdulmumin Kabir Usman CFR Ya Taya Tasi’u Sanusi Saulawa Murnar Samun Sabon Mats...
04/05/2026

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr) Abdulmumin Kabir Usman CFR Ya Taya Tasi’u Sanusi Saulawa Murnar Samun Sabon Matsayin Mukaddashin Provost Marshal na Hukumar Kwastam ta Najeriya

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji (Dr) Abdulmumin Kabir Usman CFR ya aike da saƙon taya murna ga Tasi’u Sanusi Saulawa bisa naɗinsa a matsayin Mukaddashin Provost Marshal na Hukumar Kwastam ta Najeriya.

A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Mayu, 2026, Sarkin ya bayyana cewa naɗin Saulawa ya zo ne bisa cancanta da ƙwarewa, tare da nuna jin daɗinsa da alfahari ga wannan matsayi da ɗan asalin Jihar Katsina ya samu.

Mai Martaba ya ƙara da cewa wannan naɗi babban nauyi ne da ke buƙatar jajircewa, riƙon amana da kuma aiki tukuru domin tabbatar da an cika amanar da aka ɗora masa.

Sarkin Katsina ya yi addu’ar Allah Ya ba Saulawa lafiya, hikima da nasara wajen gudanar da wannan sabon aiki, tare da fatan zai ci gaba da kawo ci gaba ga ƙasa da al’umma baki ɗaya.

Haka kuma, ya bayyana cewa wannan nasara abin alfahari ne ga masarautar Katsina da ma Jihar baki ɗaya, yana mai fatan za ta ƙara inganta suna da martabar jihar a matakin ƙasa.

A ƙarshe, Mai Martaba ya yi fatan Allah Ya ƙara masa ɗaukaka tare da ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata.

Address

No 036 Umar Faruq Plaza Opp Post Office PZ
Zaria
8100031

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HNN Hausa:

Shortcuts

Share