DOKIN KARFE News

DOKIN KARFE News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from DOKIN KARFE News, Media/News Company, Sobon gari LG Zaria, Zaria.

06/10/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abdullahi Sani, Faisal Haruna Zuntu, Kim Yoon, Dan Hajiya Jikan Alhaji, Aminu Ibrahim Roni

12/06/2024

Big shout-out to my newest top fans! Abdullahi Sani

03/06/2024

Gwamnatin Najeriya ta ce yajin aikin da ƴan kwadago ke yi ya saɓa wa doka

Yajin aiki: Ƴan ƙwadago sun katse wutar lantarki

Ƴan ƙwadago sun rufe ma'aikatu da bankuna a Kano

Ƴan ƙwadago sun rufe hanyar shiga kamfanin man fetur na Najeriya

An samu tsaikon zirga-zirgar jiragen sama a Legas saboda yajin aikin ma'aikata

Babban Bankin Najeriya ya soke lasisin bankin Heritage.

'Tattalin arziƙin Najeriya na bunƙasa'

Ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya ta bi sahun yajin aikin ƙwadago

Wani mutum da aka yi wa duka saboda zargin wulakanta Ƙur'ani a Pakistan ya rasu

Kwamitin albashi mafi ƙanƙanta na Najeriya zai gana da ƴan ƙwadago

Jam'iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai

Najeriya ta sauya taken ƙasaSa'o'i 3 da s**a wuceShugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da am...
29/05/2024

Najeriya ta sauya taken ƙasa
Sa'o'i 3 da s**a wuce

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da amfani da tsohon taken ƙasar mai suna "Nigeria: We Hail Thee".

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a yau, wanda tuni aka yi amfani da shi lokacin da Tinubu ya yi wa taron majalisar na haɗin gwiwa jawabi a yau Laraba.

Shi ne karon farko da majalisar ta rera taken tun bayan daina amfani da shi shekara 46 da s**a wuce.

Shugaba Tinubu ya ce taken na nuna bambancin al'adu, da kuma wakiltar kowane ɓangare tare da zimmar taka rawa wajen ƙulla 'yan'uwantaka.

Yayin bikin cikarsa shekara ɗaya a kan mulki da kuma murnar cika shekara 25 da komawa mulkin dimokuraɗiyya, shugaban ya taya 'yan ƙasa murna kuma ya nemi 'yan majalisa "su ci gaba da aiki tare don gina ƙasar da na gaba za su yi alfahari da ita".

WATA SABUWAHalin Da Ake Ciki Game da Sarautar KanoBabbar kotun Jihar Kano ta umarci jami’an tsaro da kada su tsige Sarki...
29/05/2024

WATA SABUWA

Halin Da Ake Ciki Game da Sarautar Kano

Babbar kotun Jihar Kano ta umarci jami’an tsaro da kada su tsige Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, Sannan kuma su fitar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadarsa da yake zaune Ta Nasarawa.

A halin da ake ciki, babbar kotun Tarayya ta bayar da umarnin haramtawa jami’an tsaro cafke Sarkin Kano na 15, Aminu ado Bayaro tare da fitar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II daga fadarsa Dake Kofar Kudu.

RIKICIN SARAUTAR KANO: An ji ƙarar rugugin harbe-harben bindiga daga fadar Sarkin Kano a cikin dare zuwa asuban TalataMa...
28/05/2024

RIKICIN SARAUTAR KANO: An ji ƙarar rugugin harbe-harben bindiga daga fadar Sarkin Kano a cikin dare zuwa asuban Talata

May 28, 2024

A daren ranar Litinin ne aka ji karar harbe-harbe a karamar fadar da tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ke zaune a Nasarawa GRA na babban birnin jihar.

Fadar tana da nisan kimanin mita 300 daga gidan gwamnatin Kano inda aka takaita zirga-zirgar ababen hawa zuwa wani bangare na hanyar da zai kai ka Tarauni.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu mafarauta dauke da muggan mak**ai a fadar Sarkin da aka dawo da Sarki Lamido Sanusi, s**a yi yunkurin kai farmaki kan wasu masu zanga-zangar neman gwamnan ya bi umurnin kotu da ya hana ta tsige Ado-Bayero.

Wasu mazauna yankin da masu wucewa sun yi zargin cewa an yi harbin ne don hana duk wani yunkurin k**a Ado-Bayero bayan wata babbar kotun jihar ta bayar da umarnin a kore shi daga fadar a ranar Litinin.

Har yanzu ba a iya tabbatarwa ko harbe harben daga jami’an tsaro ne ko kuma dogaran fadan sarki.

Babbar kotun jihar kano ta umarci sarkin Kano na 15, Mai martaba Aminu Ado bayero da ya daina kira ko gabatar da kansa a...
27/05/2024

Babbar kotun jihar kano ta umarci sarkin Kano na 15, Mai martaba Aminu Ado bayero da ya daina kira ko gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kano.

Haka kuma kotun ta bayar da umarni ga ƴansanda da su fitar da shi daga fadar Sarkin Kano da ke unguwar Nassarawa a cikin jihar.

A umarnin da kotun ta bayar bayan da ta karanta bukatar da lauyan gwamnatin jihar Kanon Ibrahim Isa Wangida ya gabatar mata, kotun ta zartar da umarnin na wucin-gadi.

Bayan Alhaji Aminu Ado Bayero, kotun ta kuma umarci sauran sarakuna hudu da aka rushe da su daina ayyana kansu a matsayin sarakunan masarautun.

Masarautun da aka rushe dai su ne wadda tsohuwar gwamnatin jihar kanon ta APC karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro wato Kano da Bichi da Gaya da Rano da kuma Karaye.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Sarkin na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gabatar da zaman fada a yau Litinin.

Babbar kotun ta dage zaman sauraren karar wadda aka shigar a gabanta ranar 24 ga watan nan na Mayu 2024, zuwa ranar 11 ga watan Yuni shekara ta 2024 domin saurare

26/05/2024
Kotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano Babbar kotun tarayyar mai zama a Kano ta bayar da umurnin dakatar da gwamnatin ...
24/05/2024

Kotu ta Dakatar da Rushe Masarautun Kano

Babbar kotun tarayyar mai zama a Kano ta bayar da umurnin dakatar da gwamnatin Kano daga aiwatar da matakin rushe masarautun jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan karar da guda daga cikin manyan hakiman da matakin ya shafa Alh Aminu Babba Dan Agundi Sarkin Dawaki Babba ya shigar a gaban kotu domin kalubalantar matakin rusa masarautu da majalisar dokokin Kano ta yi, wanda gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu na amincewa da kudurin.

Kotun Karkashin Justice AM Liman ta sanya ranar 3 ga watan Yuni domin sauraran karar.

Mene ne ra’ayin ku kan wannan turka-turka?

23/05/2024

YANZU YANZU TIJJANI GANDU ya saki wakar Barka da zuwa Sanusi

Ga wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, wadda ta rushe dukkanin masarautun jih...
23/05/2024

Ga wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, wadda ta rushe dukkanin masarautun jihar biyar.

Majalisar Kano ta rushe masarautu biyar na jiharASALIN HOTON,KANO STATE GOVERNMENTSa'o'i 5 da s**a wuceMajalisar dokoki ...
23/05/2024

Majalisar Kano ta rushe masarautu biyar na jihar

ASALIN HOTON,KANO STATE GOVERNMENT

Sa'o'i 5 da s**a wuce

Majalisar dokoki ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu a 2019.

Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Alhamis.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ya nuna cewar sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano duk sun rasa kujerunsu.

Address

Sobon Gari LG Zaria
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DOKIN KARFE News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DOKIN KARFE News:

Share