Taskiya Reporters

Taskiya Reporters ingantattun labarai domin tunatarwa, fadakarwa da ilmantarwa

ZA'A GUDANAR DA JANA’IZAR KHALIFA SHEIKH GHALI SHEIKH YAHUZA ZARIAZa a gudanar da sallar jana’izar Khalifa Sheikh Ghali ...
20/08/2026

ZA'A GUDANAR DA JANA’IZAR KHALIFA SHEIKH GHALI SHEIKH YAHUZA ZARIA

Za a gudanar da sallar jana’izar Khalifa Sheikh Ghali Sheikh Yahuza Zaria, tare da wasu daga cikin iyalansa da Allah Ya yi wa rasuwa, gobe Juma’a, 20 ga Agusta, 2026.

Lokaci: Ƙarfe 3:00 na rana
Wuri: Masallacin Mai Martaba Sarkin Zazzau.

Ana kira ga ’yan uwa, almajirai, muridai da masoya da su halarci jana’izar domin raka marigayin zuwa makwancinsa na ƙarshe tare da yi masa addu’a.

Allah Ya gafarta musu, Ya jikansu da rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsu, Ya kuma bai wa iyalansu da ɗaukacin ’yan uwa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN 😭 😭 DUK SU HUƊU SUN RASU YAUCikin alhini da jimami muke sanar da rasuwar Mallam Suka...
20/08/2026

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN 😭 😭

DUK SU HUƊU SUN RASU YAU

Cikin alhini da jimami muke sanar da rasuwar Mallam Sukairaju Gahli, ɗaya daga cikin mutane huɗu da s**a rasa rayukansu a yau sakamakon mummunan haɗarin mota da ya faru a kan hanyar Gamagira.

Marigayin ya yi hatsarin ne tare da Sheikh Gahli, Khalifan Sheikh Yahuza Zariya, da wasu mutane biyu. Abin baƙin ciki, dukkan mutane huɗun sun rasu sakamakon wannan mummunan haɗari.

Za'ayi Jana'izarsu Gobe Juma'a da Misalin Ƙarfe 03:00pm Na Rana A Fadar Sarkin Zazzau.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta musu baki ɗaya, Ya jiƙansu da rahama, Ya haskaka kaburburansu, Ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsu.

Allah Ya ba iyalansu, ’yan uwa, abokan arziki, almajirai da ɗaukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN 😭 😭YANZU_YANZU: Cikin Alhini da Jimami Muke Sanar da Jama'a Rasuwar Khalifan Sheikh ...
20/08/2026

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN 😭 😭

YANZU_YANZU: Cikin Alhini da Jimami Muke Sanar da Jama'a Rasuwar Khalifan Sheikh Yahuza Zaria, Sheikh Malam Ghali S.Yahuza

Malam Ghali Ya Rasu ne Sakamakon Wani Hatsarin Da Ya Rutsa Dasu a Hanyar Soba.

Za'a Sanar da Lokacin da Za'a Gudanar da Jana’izarshi Nan Gaba Kaɗan insha Allahu

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljanna ce makomarsa, Ya kuma ba iyalansa da ’yan uwa da abokan arziki haƙurin jure wannan babban rashi.

~ Daga Muhammad Bello Agaji
Director Fityanul Islam Zaria Local Govt.

SAƘON GAGGAWA.Majalisar Shura ta Ɗarikar Tijjaniyya tana kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sakin Khalifa Sheikh S...
01/08/2026

SAƘON GAGGAWA.

Majalisar Shura ta Ɗarikar Tijjaniyya tana kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sakin Khalifa Sheikh Sani Abdulƙadir Zaria ba tare da wani ƙarin ɓata lokaci ba. Idan kuwa ba a sake shi ba, to mu zamu sake ku.

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI'ŪN😭Babban Malamin Addinin Musulunci, Mallam Gwani Rigasa Kaduna, Allah Ya Yi Masa Rasuw...
25/07/2026

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI'ŪN😭

Babban Malamin Addinin Musulunci, Mallam Gwani Rigasa Kaduna, Allah Ya Yi Masa Rasuwa

An samu labarin rasuwar Babban Malamin Addinin Musulunci, Mallam Gwani Rigasa Kaduna, wanda ya kasance tsohon limamin Masallacin Makera Bus Stop da ke Rigasa, Jihar Kaduna.

Marigayin ya kasance daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci da s**a sadaukar da rayuwarsu wajen koyarwa, wa'azi da jagorantar al'umma a kan tafarkin addini.

🗓️ Jana'iza: Yau Asabar, 25/07/2026
🕘 Lokaci: Karfe 9:00 na safe
📍 Wuri: Naira Road, Dogon Layi, Rigasa, Kaduna.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa kabari, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya ba iyalansa, almajiransa da daukacin al'ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi. Āmīn.

Rahoto: Tijjaniyya Media Team, tare da taimakon AI.

Kuyi Following Tijjaniyya Media Team

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!Allah SWT ya karbi rayuwar Hafiza Bahijjah Adam, 'yar asalin Jihar Kaduna, lamarin ...
15/07/2026

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!

Allah SWT ya karbi rayuwar Hafiza Bahijjah Adam, 'yar asalin Jihar Kaduna, lamarin da ya jefa iyalanta, ɗalibanta, abokanta da al'ummar Musulmi cikin alhini.

Marigayiyar ta kasance daga cikin masu hidima ga Alƙur'ani Mai Girma, inda ta yi fice wajen haddacewa, karantawa da koyar da Alƙur'ani. Ta bar kyakkyawan tarihi na ilimi, tarbiyya da bautar Allah, wanda zai ci gaba da kasancewa abin tunawa.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya yalwata mata rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarta. Amiin Yaa ALLAH

12/07/2026

Ga Kyau, Ga Kyauta

MUHAMMADUR RASULULLAH
🥰ﷺ😘

YANZU-YANZU:Sarkin Argungu ya bukaci jama'a su mallaki makamai domin kare kansuMai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Muhamma...
06/06/2026

YANZU-YANZU:Sarkin Argungu ya bukaci jama'a su mallaki makamai domin kare kansu

Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Muhammadu Sama’ila Mera, ya bukaci al’ummar masarautarsa da su mallaki makamai bisa ka’ida domin kare kansu da yankunansu daga hare-haren ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Sarkin ya bayyana hakan ne yayin wani taro da hakimai, shugabannin ƙauyuka da na unguwanni da aka gudanar a fadarsa da ke Argungu.

Me za ku ce?

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskiya Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share