NI IMAR ALLAH

NI IMAR ALLAH Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from NI IMAR ALLAH, Digital creator, Ikara, Zaria.

02/09/2025

Akwai wata jumlar wacce ta taɓani wacce take cewa : Ahli ba maganar jini bace amma magana waye wanda ya ɗaga maka hannu a lokacin da kake cikin bukatar shi
_Akwai Abokai🫂
_Akwai Ahli👥
_Akwai abokai dake zama Ahli👥👥

Abokai na kirki sunada wahalar samu
Akwai wahalar a ƙaurace musu
Akwai wahalar a manta dasu
Idan wasu Abokai s**a ƙaurace maka kada kayi ƙoƙarin maido su gareka kabarsu su tafi domin ka nemo sababbi

Abota bawai Abokai dari hudu ne ba (400) da kake dasu a cikin kafafen sadarwa📲 Abota ƴa'ƴan bishiyoyi ne dake tsayawa a tare dakai a lokacin da kake cikin ƙunci💔

Rayuwa bata ce mana komai
Amma da sannu sannu tana Fahimtar damu komai

A cikin Rayuwa yanada muhimmanci ka samu aboki Wanda yake wani lokaci madubi◻️ wani lokaci inuwa⬛

Madubi baya ƙarya
Inuwa bata gushewa har abada

Abokan ƙarya kamar inuwa suke suna tare dakai a lokacin da kake cikin haske⚪

Amma suna kaurace maka a lokacin da ka faɗi cikin duhu⚫

" Ko wani mutum da ka gani a duniyar wannan to ya gamu da jarabawa , wani Allah ya jarebe sa akan imaninsa wani akan duk...
01/09/2025

" Ko wani mutum da ka gani a duniyar wannan to ya gamu da jarabawa , wani Allah ya jarebe sa akan imaninsa wani akan dukiyarsa wani kuma akan iyalansa , to idan ka ji jarabawar wani kai taka ƙarama ce , ka zamo mai godiya ga Allah."

Alhmdulillah

abdoul Idris 🖊️

01/09/2025

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Shaiɗan ya kan ɓoye idan ya ji an ambaci sunan Allah (ﷻ), domin haka aka yi masa suna mai ɓoyewa, wato ba ya zama wurin da ake karatu da wa'azi kamar yadda ba ya zama cikin zuciyar mai ibada da gaskiya.

Ibada ta gaskiya ita ce wadda aka yi ta kamar yadda Allah (ﷻ) yace a yi ta, banda ibadar bidi'a, ba ta korar shaiɗan, Kuma da sharaɗin a yi ibadar da kyakkyawar niyya, domin aikin da babu niyya mai kyawu game da shi ɓatacce ne.

Abdulfatahu Idris
🖊
08 Rabi'ul Awwal 1447A.H
01 September 2025

Address

Ikara
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when NI IMAR ALLAH posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share