Shuhada Foundation

Shuhada Foundation The Official Page For Mu'assasatu Shuhada, Under The Islamic Movement In Nigeria.
(1)

TUNATARWA:Yayin da watan Mauludi mai albarka ya k**a (Rabi'ul Auwal) wato watan haihuwar Fiyayyen Halitta Gatan Marayu d...
14/08/2026

TUNATARWA:

Yayin da watan Mauludi mai albarka ya k**a (Rabi'ul Auwal) wato watan haihuwar Fiyayyen Halitta Gatan Marayu da masu uba, muna tunatar da 'yan uwa kan biyan haƙƙin Shuhada na wannan wata — ₦500 zaku iya sauke na shekara ma 6K ne kacal.

Shahidai sun sadaukar da rayuwarsu, amma sun bar mana iyalai da alhakin kula da su. Saboda haka, wannan gudunmawar ba kawai kuɗi ba ce; hanya ce ta nuna cewa ba mu manta da sadaukarwarsu ba, kuma ba mu manta da iyalansu ba.

Mu'assasatu Shuhada tana tunatar da yan'uwa, duk wanda bai biya na wannan watan ba, ko wattannin baya, muna ƙara tunatar da shi da ya sauke haƙƙinsa. Wanda kuma ya riga ya sauke, zai iya ƙara Ihsani gwargwadon ikonsa.

Mu tuna Shuhada, mu tallafi iyalansu, mu cika haƙƙinsu.

Allah Ya karɓi sadaukarwar Shuhadammu, Ya albarkaci duk mai bayarwa, Ya sanya wannan a cikin ayyukan alheri. 🤲🏽

Zaku iya turawa kai tsaye zuwa asusun Shuhada Foundation:

Acc: 1004801776
Bank N; UBA Shuhada Foundation

Acc: 1011864432
Bank N: Zenith Shuhada Foundation

Allah yabamu ikon saukewa!


.

TUNATARWA!"Idan Ansamu Shahidai to Akwai Hakkokin iyalan Shahidai akanmu, tun daga Karatunsu, Sutura". Sannan mu riƙa yi...
11/08/2026

TUNATARWA!

"Idan Ansamu Shahidai to Akwai Hakkokin iyalan Shahidai akanmu, tun daga Karatunsu, Sutura". Sannan mu riƙa yi yimusu addua a cikin Salolinmu na wuturi, kuma a karkare addu'ar da neman Allah ya dauki fansa.

—Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)

Don Haka ana tunatar da yan'uwa suyi kokarin sauke hakkin Shuhada, Idan mutum ya sauke yana da Hali to yayi Ihsani.

Akan kokarin da Yan uwa suke harwalayau yana da kyau su rika kokarin isar da Asusun Shuhada Foundation lungu da sako inda yan'uwa suke!

Sanarwa Daga Shuhada Foundation
SHAHIDANMU GWARAZANMU!

ABS Channel Tv
Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
Fa'eez Media
Media Forum of the Islamic movement
Harkar Musulunci
Hurras Media


TUNATARWA - TUNATARWA! Yayin da muke kusantar Arba'in na Imam Hussain (AS), yana da kyau mu tuna cewa ƙaunar Imam Hussai...
30/07/2026

TUNATARWA - TUNATARWA!

Yayin da muke kusantar Arba'in na Imam Hussain (AS), yana da kyau mu tuna cewa ƙaunar Imam Hussain da sauran shahidai ba ta tsaya ga hawaye da alhini kawai ba. Daya daga cikin hanyoyin nuna godiya ga sadaukarwarsu ita ce kula da iyalansu da kuma bayar da gudunmawar da aka ware domin sauke haƙƙinsu.

Kamar yanda muka sani akwai haƙƙin shuhada da ake biya Naira 500 a kowane wata wata, hakan hanya ce ta nuna cewa ba mu manta da waɗanda s**a sadaukar da rayuwarsu saboda gaskiya ba, kuma ba mu manta da iyalansu da s**a rage ba. Ko da gudunmawar ta yi ƙanƙanta, idan aka yi ta da ikhlasi tana da daraja a wurin Allah.

Idan ka riga ka sauke haƙƙinka na wannan wata ko Shekara, kada ka tsaya nan. Ka ƙara da ihsani, domin Allah Maɗaukakin Sarki yana son masu kyautatawa. Wataƙila wannan ƙarin alherin naka zai zama sanadin farin ciki ga iyalin wani shahidi, kuma ya zama abin da za ka tarar a ranar da dukiya da 'ya'ya ba za su amfana ba, sai wanda ya zo wa Allah da zuciya mai tsarki.

Kada mu bari iyalan shahidai su ji cewa al'umma ta manta da su. Mu kasance masu cika alƙawari ga jinin da aka zubar saboda kare gaskiya.

Allah Ya karɓi sadaukarwar shahidanmu, Ya albarkaci masu tallafa wa iyalansu, Ya sanya mu cikin masu cika haƙƙinsu da ikhlasi.

Zaku iya saukewa Ko Ihsani, ta hanyar Asusun Shuhada foundation kai tsaye!

Acc: 1004801776
Bank: UBA. Shuhada foundation..

Ko kuma;

Acc: 1011864432
Bank: Zenith. Shuhada foundation.





-Shuhada Foundation
30/July/2026

WAƘI'AR 25 JULY, 2014: SHAHADAR MUTUM 34 RANAR DA TA BAR TARIHI CIKIN HAWAYE A HARKAR MUSULUNCI.A ranar Juma'a, 25 ga Yu...
25/07/2026

WAƘI'AR 25 JULY, 2014: SHAHADAR MUTUM 34 RANAR DA TA BAR TARIHI CIKIN HAWAYE A HARKAR MUSULUNCI.

A ranar Juma'a, 25 ga Yuli, 2014, wacce ta zo daidai da Juma'ar ƙarshe ta watan Ramadan, wani al'amari mai matuƙar raɗaɗi ya faru a birnin Zariya. Bayan kammala Muzaharar Ranar Ƙudus, jami'an soji sun buɗe wuta kan yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

A wannan hari, mutane 34 ne s**a rasa rayukansu. Daga cikinsu akwai Ahmad, Hamid da Mahmud, uku daga cikin 'ya'yan Shaikh Zakzaky (H). Bisa ga haka a lokacin, an k**a su da ransu, aka kai su Barikin Bassawa, inda daga bisani aka kashe su bayan azabtarwa mafi muni da sojojin s**a yi masu. Haka kuma kaninsu Ali (Haidar) ya ji munanan raunuka, da harbi a kafarsa. A tare da shi Akwai wasu yan uwa Mujaheed da Imamu. Wanda daga baya shi ma Ali (Haidar) ya kasance cikin waɗanda s**a rasa rayukansu a harin da aka kai ranar 12 ga Disamba, 2015 har gidan su a gaban mahaifinsu sojojin s**a kashesa tare da wasu yan uwansa Hammad da Humaid.

Wani abin da ya ƙara girgiza zukatan mutane da zalunci shi ne kashe wani dattijon Kirista mai suna Mr. Julius Anyanwu, mai shekaru 60 da sojojin s**a yi. Saboda ya kusanci jami'an sojin ne yana tambayarsu dalilin amfani da ƙarfi a kan mutanen da ba su ɗauke da makami, sai shi ma aka harbe shi. Wannan lamari ya nuna cewa bala'in wannan rana bai tsaya kan bambancin addini ko ƙabila ba.

A ranar 13 ga Oktoba, 2014, aka gudanar da jana'izarsa a jiharsa ta Imo, inda Shaikh Zakzaky (H) ya aika da Pasto. Yohana Y.D Buri da wakilai domin su halarta tare da miƙa ta'aziyya ga iyalansa.

Jagorancin wannan Kisan ya samu ne ga wani babban jami'in soja mai suna Birgediya S. O. Oku, wanda ya taka muhimmiyar rawa a abin da ya faru a wannan rana.

Washegari, Asabar, jami'an sojin sun sake komawa gaban Husainiyyah Baqiyyatullah da ke Zariya. Duk da harbe-harben da aka yi kisa da jikkata almajiran Sheikh Zakzaky a gaban Husainiyya, amma ba su cimma manufar ta rushe Husainiyyar ba a wannan lokaci.

Daga baya; Sarkin Zazzau na lokacin, Alhaji Shehu Idris ya basu kyautar doya cikin mota guda, tare da yi musu jinjina s**a tafi.

Wannan kisan na Shahidan Qudus a Zariya, wani al’amari ne da ya dauki hankalin al’ummar Duniya baki-daya, musamman a Nijeriya

Abin da ya biyo bayan wannan lamari shi ne yadda jama'a daga sassa daban-daban na Nijeriya s**a nuna alhini da tausayawa. Malamai, shugabannin addinai, 'yan siyasa, ƙungiyoyi masu zaman kansu, Kiristoci da Musulmi, tare da mutane daga ƙabilu da mabambantan fahimtu, sun riƙa tururuwa zuwa gidan Shaikh Zakzaky (H) a Gyallesu na tsawon watanni domin yin ta'aziyya.

Tarihi ba ya mantawa da irin waɗannan ranaku. Rayukan waɗanda s**a rasa rayukansu suna ci gaba da tunatar da duniya muhimmancin kare haƙƙin ɗan Adam, mutunta rayuwar bil'adama, da tabbatar da adalci. Duk lokacin da aka yi shiru a gaban zalunci, ana ba shi damar maimaita kansa.

Allah Ya girmama ladan shahidanmu, Ya jiƙansu da rahama, Ya ba iyalansu da sauran al'ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi. 🥀🤲

ABS Channel Tv
Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
Fa'eez Media
Harkar Musulunci
Media Forum of the Islamic movement


WAKI’AR SOKOTO TA ALU WAMMAKO 2007. 20th July, 2007 (6 Rajab, 1428H)A irin wannan wata ranar Juma'a 20th July aka yi Wak...
20/07/2026

WAKI’AR SOKOTO TA ALU WAMMAKO 2007. 20th July, 2007 (6 Rajab, 1428H)

A irin wannan wata ranar Juma'a 20th July aka yi Waki'ar Sokoto, wacce ta fara da harbe wani Malamin Wahabiyya da wasu da ba a san ko su wa s**a yi ba, ‘yan iskan gari dajami’an tsaro s**a fake da wannan s**a dira a kan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky, s**a shahadantar da ‘yan uwa kusan 10, tare da jikkata da dama, da kona gidajen ‘yan uwa da shagunan sana’arsu fiye da 300.

Sannan kuma hukumar jihar bisa umurnin gwamna Aliyu Magatakarda Wammako s**a k**a wakilin ‘yan uwa na garin, Shaikh Kasimu Umar tare da ‘yan uwa kusan 120. Sai da ‘yan uwan nan s**a shafe shekaru shida a tsare kafin Allah ya kaddara fitowarsu.

Ga sunayen Shahidan Waki'ar!

1) shahid Hussaini Aliyu mana
2) shahid Aminu System hungumwa
3) shahid Nasiru Aliyu jimi
4) shahid aliyu abubakar tabako
5) shahid Nura abubakar guiwa
6) shahid Hussaini bello Gidadawa

Allah (T) ya karbi Shahadar Shahidan mu! Amin.

Domin Sauke Hakkin Shuhada Ko Ihsani, kuna iya turawa ta asusun Shuhada Foundation kai tsaye:

Acc: 1004801776
Bank NM: UBA
Acc NM: Shuhada Foundation

Acc: 1011864432
Bank NM: Zenith
Acc NM: Shuhada Foundation




Barkan mu da Ranar Juma'a Mai Albarka! 🕋Tunatarwa; "Muyi kokari mu sauke Haƙƙin Shuhada, kuma muyi ihsani, Kada mu zama ...
17/07/2026

Barkan mu da Ranar Juma'a Mai Albarka! 🕋

Tunatarwa; "Muyi kokari mu sauke Haƙƙin Shuhada, kuma muyi ihsani, Kada mu zama masu yawan yabon shahidai da harshe kawai; mu zama masu raya manufarsu da ayyuka. Domin su, ayyukansu ne s**a rinjayi maganganunsu."🌹

Mu bayar da kaɗan Allah ya nunka mana.

Acc: 1004801776
Bank NM: UBA
Acc NM: Shuhada Foundation

Acc: 1011864432
Bank NM: Zenith
Acc NM: Shuhada Foundation



.

SAKON GODIYA!Mu'assasatush-Shuhada tana miƙa saƙon godiya da jinjina ga ɗaukacin 'yan'uwa Musulmi da s**a amsa kiran gid...
10/07/2026

SAKON GODIYA!

Mu'assasatush-Shuhada tana miƙa saƙon godiya da jinjina ga ɗaukacin 'yan'uwa Musulmi da s**a amsa kiran gidauniyar bankwana da Shaheed Imam Khamna'i (QS).

Alhamdulillah, an samu transactions masu dimbin yawan da Allah (SWT) kaɗai Ya san adadinsu. Haka nan, tun daga fitar sanarwar gidauniyar yan uwa suke ta turo da receipts har zuwa yau duk saboda nuna kauna ga Shaheed Imam Khamna'i (QS).

Wannan ya ƙara tabbatar da cewa ƙaunar Shahidi Imam Khamna'i (QS) ta zauna a zukatan mutane, kuma ba za ta taɓa gushewa ba. Muna da yaƙinin cewa idan aka sake yin irin wannan kira a gaba, za a ga sadaukarwa mafi girma fiye da wannan.

Har zuwa yanzu, kofa a bude take ga wanda basu saka nasu ba, da kuma wanda zasuyi ƙara Ihsani domin faranta Ruhin Shahid Khamene'i ta hanyar farantawa iyalan Shahuda!

Allah (SWT) Ya karɓi ibadun mu, Ya sakawa kowa da alkhairi, Ya kuma sanya ladan wannan aiki ya isa ga Shaheed Imam Khamna'i (QS). Ilahee, Ameen.






10/July/2026

Ga dama ta samu ga masu neman falala!Gidauniyar Bankwana da Imam Khamna'i (QS).Muna sanar da gayyatar yan uwa Musulmi ga...
09/07/2026

Ga dama ta samu ga masu neman falala!

Gidauniyar Bankwana da Imam Khamna'i (QS).

Muna sanar da gayyatar yan uwa Musulmi gabatar da wata kwarya-kwaryar gidauniya ta sadaukarwa ga Shaheed Imam Khamna'i (QS), domin mika ladan gare shi albarkacin Iyalan Shuhada.

Ka sadaukar da N500 ka tura cikin asusun bankin Mu'assasatu Shuhada k**ar:

Acc: 1004801776
Bank NM: UBA
Acc NM: Shuhada Foundation

Acc: 1011864432
Bank NM: Zenith
Acc NM: Shuhada Foundation

Muna sa ran ganin receipt daga yan uwa cikin gidauniyar da za a gabatar hadiya ga Shaheed Imam Khamna'i (QS).



09/07/2026

Mu'assasatush-Shuhada Foundation na kiran muminai domin gabatar da wata ƙwarya-ƙwaryar gidauniya hadiyya zuwa ga Shaheed Sayyid Ali Khamna'ei (DZ).

Maza garzaya ayi dakai kada wannan garaɓasa ta wuce ka.🌹




09 July, 2026.

TUNATARWA KAN BIYAN HAKKIN SHUHADADarasi daga watan Muharram Watan Sadaukarwa da Shahadaبِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمٰنِ الرَّ...
28/06/2026

TUNATARWA KAN BIYAN HAKKIN SHUHADA

Darasi daga watan Muharram Watan Sadaukarwa da Shahada

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيمِ

Lalle Ashura ba kawai labari ba ce, alƙawari ne. Ba kawai tarihin shahada ba ne, makaranta ce ta sadaukarwa, da kuma cika alqawari.

Ya ku 'yan uwa Almajiran Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Muna cikin watan Muharram; watan da yake raya zukata da tunawa da irin sadaukarwar da Imam Husaini (AS) da iyalansa da sahabbansa s**a yi domin kare addinin Allah. Amma akwai tambaya da ya k**ata kowannenmu ya yi wa kansa:

Shin me muka koya daga Karbala?

Karbala ta koya mana cewa sadaukarwa ba ta ƙare da zubar da jini ba. Bayan shahada, akwai wata amanar da ta rage a wuyan al'umma: kula da iyalan shahidai da waɗanda s**a bari a baya.

Bayan shahadar Imam Husaini (AS), iyalansa sun shiga cikin ƙunci, yunwa, ƙuncin tafiya da zaman juyayi. Sai dai Allah Ya sanya waɗanda s**a kasance masu aminci s**a tsaya wajen kare mutuncinsu da ɗaukar nauyinsu. Wannan ya zama darasi ga kowace al'umma mai neman bin tafarkin Karbala.

A yau ma muna da iyalan Shuhada waɗanda mazansu, 'ya'yansu ko iyayensu s**a sadaukar da rayuwarsu saboda bin tafarkin Imam Husaini. Waɗannan iyalai ba su rasa komai saboda son duniya ba; sun rasa masoyansu ne saboda kare addini da tsayawa kan gaskiya.

Saboda haka, biyan Haƙƙin Shuhada ba sadaka ba ce kawai; wata amana ce da ke wuyanmu. Wannan shi ne ɗaya daga cikin hanyoyin tabbatar da cewa jinin shahidai bai zube a banza ba.

Allah Madaukakin Sarki Ya ce:

"Kuma kada ku yi zaton waɗanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne. A'a, rayayyu ne a wurin Ubangijinsu, ana azurta su."
(Suratu Ali Imran: 169)

Idan shahidai suna da wannan matsayi a wurin Allah, to ya dace mu girmama abin da s**a bari a bayan su. Daya daga cikin mafi kyawun hanyoyin nuna wannan girmamawa ita ce tsayawa tare da iyalansu da tallafa musu.

Ya kai ɗan uwa / Y'ar uwa,

Bayan sauke Hakkin wata N500 toh Ko da gudummawarka kaɗan ce, kada ka raina ta. Wataƙila abin da kai ka ba da sauƙi ne a gare ka, amma shi ne zai zama farin ciki ga marayu.

Muharram wata ne na sabunta alƙawari. Kamar yadda muke sabunta baƙin cikin Karbala, mu kuma sabunta alƙawarinmu na kula da waɗanda s**a sadaukar da komai saboda wannan tafarki.

Don haka Mu'assasatu Shuhada tana kara kira da karfafa dukkan muminai da su ba da gudummawarsu kai tsaye ta asusun Shuhada Foundation, domin cika wannan haƙƙi da Allah Ya ɗora mana.

Kada mu bari iyalan Shuhada su ji cewa sun yi sadaukarwa su kaɗai. Mu nuna musu cewa al'ummar da shahidai s**a mutu saboda ita ba ta manta da su ba.

Allah Ya karɓi sadaukarwar Shuhada, Ya ba iyalansu haƙuri da lada, Ya kuma sanya mu cikin masu cika amanar da aka ɗora mana.

وَالسَّلَامُ عَلَى الْحُسَيْنِ، وَعَلَى عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ، وَعَلَى أَوْلَادِ الْحُسَيْنِ، وَعَلَى أَصْحَابِ الْحُسَيْنِ.

Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
ABS Channel Tv
Fa'eez Media
Media Forum of the Islamic movement
Harkar Musulunci
Hurras Media
Shuhada Foundation


Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shuhada Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share