
24/08/2025
YAU LAHADI - 24th August,2025
Ranar Lahadi tana ƙarƙashin tauraron Shams (الشَّمْس), wanda shi ne jagoran fitila da haske a cikin sararin samaniya. Ana ɗaukarsa a matsayin tauraro mai kyau (سَعِيد), wato mai kawo albarka da alheri a cikin ayyuka da al'amuran Ɗan'adam.
A wannan rana, ana ganin dacewa da yin ayyukan addu'ar da s**a shafi ɗaukaka (رِفْعَة), neman mulki ko shugabanci (الحُكْم), da kuma samun iko a cikin al’umma. Wannan yasa malamai s**a ce idan mutum ya nemi matsayi ko ɗaukaka a wannan rana, akwai yiwuwar ya samu nasara idan ya haɗa da addu’ar data dace da ranar tare da yin sadaqa.
Haka kuma ranar Lahadi tana da alaƙa da neman karɓuwa wajen shugabanni (قَبول عند الزعماء) da manya, ko kuma neman cigaba a wurin aiki da mu’amaloli na yau da kullum. Idan mutum ya tsara ayyukansa a wannan rana, zai iya samun buɗewar ƙofa wajen ci gaban rayuwar sa bi'izinillah.
Saboda haka, dukkan mai neman sa’a a wannan rana da ya fara aikinsa da bismillah (بِسْمِ اللهِ) tare da addu’o’in neman taimako daga Allah (تعالى). Domin ko da yake Shams tana ɗauke da ƙarfin haske da sa’a, kariya ta gaskiya da ɗaukaka ba ta samuwa sai daga Allah Maɗaukaki.
m~inuwa Zaria 08060679875