
04/08/2024
Yaro karami akashe iyayensa Yana kallo idan antambayesa ina iyayenka yace ankashesu wai kuma duk Akan hakkinmu
Uwa Tana kallo Ana wulakanta yayanta mata bata da bakin magana akashe mata miji tana gani akona mahallinsu suna kallo
Iyaye suna zaune da yayansu kuna kadasu kamar dabbobi suda garinsu Amma haka zasu hakura subar muku
Anhana noma
Anhana kiwo
Kinrufe border talaka yayi hakuri da wannan yana biyayya baice komai ba yacigaba da lallaba rayuwarsa
Wutar lantaki ancire mata tallafi
Mai ancire masa tallafi
Naira ankarya darajarta
Tsaro akasa Bbu
Yunwa tana kashe kananan yara da iyayensu
Kauyuka kunje kunyi kane kane kuna sace mutane kuna karban kudin fansa talaka yana fita nema Amma kuna karbewa
Kuna sakawa bayin Allah boom suna mutuwa Amma talaka yadaure yayi hakuri
Abincin 1k yakoma 3k talaka yayi hakuri
Duk wani Jin dadin rayuwa akashi 100 talaka yahakura da kashi 80 yana lallaba ashirin ita ashirin anaso tadawo Bbu
Manyan azzalumai sunyi kane kane da dukiyar yan Nigeria talaka yayi hakuri da wannan ya yarda yafita Yanema Toh Wanda yake nemanma anabi ana karba why
Yafita neman hakkinsa gun shugabanni ance bai kyautaba
Ya Allah muna tawassali da wannan rana mai girma ranar jumaβa ya Allah ka kawo mana sauyin da mukeso Allah yadauramu Akan wannan azzalumar gwamnati ya Allah badan halinmuba ya Allah yajikanmu ya Allah kaji tausayinmu ya Allah dan sirrin dake cikin kalmar dake bakinmu kalmar shahada Allah ya wulakanta azzaluman nan Allah yakawo mana sauyi Allah yahana maison ganin Bayan talaka Jin dadin rayuwa Allah kaduba gabanmu kaduba bayan mu dan hakuri irin na manzon Allah ya Allah dan mutuncin manzon Allah ya Allah dan arzikin manzon Allah ka azurtamu da zaman lafiya da kwanciyar hankali Allah yanunawa duk wani azzalimi iyakarsa Allah yashirya mana zuriβar annabi
Gatan Mamanshi