
12/01/2025
Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya baiyana abinda aka tattauna a ganawar sa da El-Rufai
Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya bayyana sakamakon ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu manyan shugabannin siy
A yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, Gabam ya ce sun yi ganawar ne don tattauna halin da kasar ta tsinci kanta a 2024.
Ya kuma ce jam’iyyar ba ta yi wani laifi ba wajen tattaunawa da El-Rufai, wanda dan jam’iyyar APC ne.
Ya ce: “Mun yi ganawar domin duba ga halin da Nijeriya ta tsinci kan ta a 2024 a matsayin jam’iyya. Mu jam’iyyar adawa ce mai zababbun ‘yan majalisa, majalisun jihohi, da kananan hukumomi.
"Me ya sa hakan zai tada kura akan Malam Nasir El-Rufai? Sun ce ba shi da mahimmanci, ba kome ba ne. Me yasa El-Rufai ya dame su? Me yasa ake damuwa da Segun Sowunmi? Idan suna da mahimmanci, me ya sa gwamnati ba za ta ba su muƙamai da s**a dace da su don inganta aikin gwamnati ba?, ”in ji shi.
~ Daily Nigerian Hausa