Ashuk Media Services

Ashuk Media Services Domin Neman Karin Bayani; 08100840878/08082047790. Mun gode

Shafin ASHUK MEDIA SERVICES, an Bude Shi Ne domin kawo ma al'umma Labaran Al'amuran Yau da Kullum, Shirye-Shirye daban-daban, Ko Hira da Mutane, da kuma Tallace-Tallace Na duk abunda kuke bukata.

13/05/2026

DA DUMI-DUMI: Jarumi Musa Mai Sana'a ya sake yin zazzafana Martani ga Mawaki/Jarumi Ali Isah Jita. SHIN MENE NE RA'AYIN KU? Ashuk Media Services Ashuk Media Services 𝑭𝒐𝒍𝒍𝒐𝒘𝒆𝒓𝒔.

Hotunan Yadda Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa Ya Sabunta Tare Da Zamanantar Da Zauren Majalisar Zartaswar D...
13/05/2026

Hotunan Yadda Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa Ya Sabunta Tare Da Zamanantar Da Zauren Majalisar Zartaswar Dake Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Wadda Aka Maidata Ta Zamani Da Aka Ƙaddamar a ranar Laraba 13-05-2026.

Me Za Ku Ce?

13/05/2026

SPONSORED: Shiri na Musamman agame da yadda sana'ar Noma take tare da Masani, wato Alh. Nuhu Lawal Umar, Kaigaman Zazzaua, Shugaban Kungiyar Noma Dan Riba Na Jihar Kaduna da Jihohin Arewa Maso Yamma, kuma Mamallakin Kamfanin ''Tukunyar Gwari Seed Nig. Ltd''. Ga kashi na farko Ashuk Media Services The Reel

'Akwai babban ƙalubale a gaban wasu gwamnonin APC biyar da ke neman takarar wa’adi na biyu'Rahotanni sun nuna cewa aƙall...
13/05/2026

'Akwai babban ƙalubale a gaban wasu gwamnonin APC biyar da ke neman takarar wa’adi na biyu'

Rahotanni sun nuna cewa aƙalla gwamnoni biyar na jam’iyyar APC na fuskantar gagarumin ƙalubale a ƙoƙarinsu na samun tikitin takarar wa’adi na biyu gabanin zaɓen 2027.

Duk da cewa jam’iyyar APC na son amfani da tsarin sulhu wajen zaɓen ƴan takararta, alamu sun nuna cewa wasu gwamnoni da masu neman gadonsu na fuskantar turjiya daga cikin jam’iyyar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa galibin rikice-rikicen na shafar gwamnoni masu neman wa’adi na biyu, yayin da wasu gwamnoni masu shirin barin mulki ke kuma fuskantar matsala wajen tabbatar da waɗanda suke son su gaje su Ashuk Media Services The Reel

13/05/2026

TIRKASHI TACE TINUBU SHINE DAI DAI DA NIGERIA SHIN HAKANE?
Ashuk Media Services The Reel 𝑭𝒐𝒍𝒍𝒐𝒘𝒆𝒓𝒔.

AURE NE BURINA: A Shirye Nake Da Na Auri Abun Hon Al'ajabin Zazzau, Cewar Fatima Hassan...Wata Matashiya a garin Zaria F...
13/05/2026

AURE NE BURINA: A Shirye Nake Da Na Auri Abun Hon Al'ajabin Zazzau, Cewar Fatima Hassan...

Wata Matashiya a garin Zaria Fatima Hassan, ta bayyana cewa a shirye take ko ta wane hali ta auri Hon Mahmud Sadis Buba (Abun Al'ajabin Zazzau) saboda soyayyar da take yi masa.

Matashiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na sadarwa, inda ta ce ta dade tana son fitar da mijin aure, amma sai yanzu lokaci ya zo, inda ta bayyana yadda jama'a s**a matsa mata da maganar ta je ta yi aure.

Ta kara da cewa, lokaci ya yi insha Allah ga masoyina Abun Al’Ajabi nan na tsayar da shi a matsayin mijin aurena, ta kara da cewa aure ba dole sai jibgegen mutum ba, za ta iya hakuri da kadan da ta samu. Ashuk Media Services The Reel Abubakar Hussaini Kidandan

Wai shin Wane fata za ku yi mata?

DA DUMI-DUMI: Kwamitin Tantance ’Yan Takara na jam’iyyar APC  da dama wanda hakan ya hana wasu ’yan takara sama da 150 s...
13/05/2026

DA DUMI-DUMI: Kwamitin Tantance ’Yan Takara na jam’iyyar APC da dama wanda hakan ya hana wasu ’yan takara sama da 150 shiga zaɓen fidda-gwani gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce a wasu jihohin Najeriya, inda wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa s**a fara zanga-zanga tare da barazanar garzayawa kotu domin neman adalci. Yayin da wasu s**a fara ficewa daga jam'iyyar. Ashuk Media Services The Reel

Shin mene ne ra'ayin ku?

Hon. Abdullahi Tijjani Gwarzo ya janye takarar sa ta Kano ta Arewa — bayan zaman sulhu da jiga-jigan jam’iyyar APC da gw...
13/05/2026

Hon. Abdullahi Tijjani Gwarzo ya janye takarar sa ta Kano ta Arewa — bayan zaman sulhu da jiga-jigan jam’iyyar APC da gwamna Abba K. Yusuf su ka yi masu jiya a gidan gwamnatin Kano. Ashuk Media Services The Reel

CIKIN HOTUNA: Yadda mataimakin gwamnan jihar Kano, HE Murtala Sule Garo, ya wakilci gwamnan Kano Abba K. Yusuf a yau Tal...
12/05/2026

CIKIN HOTUNA: Yadda mataimakin gwamnan jihar Kano, HE Murtala Sule Garo, ya wakilci gwamnan Kano Abba K. Yusuf a yau Talata don karɓar baƙuncin tawagar babban kwamitin ƙasar Burtaniya a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Ms. Cynthia Rowe, don ziyarar girmamawa da nufin ƙara ƙarfafa dangantakar cigaba da kuma haɗin-guiwa tsakanin ƙasar Burtaniya da jihar Kano.

A jawabin ta, Ms. Cynthia Rowe ta miƙa saƙon godiya gwamnatin Burtaniya ga gwamnatin Kano da al'ummar jihar Kano bisa kyakkyawar tarba da tawagar ƙasar Burtaniya ta samu. Ms. Rowe ta kuma sake jaddada ƙudurin ƙasar Birtaniya na haɗin-guiwa da Najeriya da jihar Kano. Ashuk Media Services The Reel

SPONSORED: Ina kuke ne Manoma, to ga Sanarwa ta Musamman a madadin Maigirma Kaigaman Zazzau, Alh. Nuhu Lawal Umar, Hakim...
12/05/2026

SPONSORED: Ina kuke ne Manoma, to ga Sanarwa ta Musamman a madadin Maigirma Kaigaman Zazzau, Alh. Nuhu Lawal Umar, Hakimin Fatika da kewaye, Mamallakin Kamfanin Tukunyar Gwari Nig. Ltd, kuma shugaban Kungiyar Noma dan Riba na Jihar Kaduna da Arewa Maso YammaHInsha Allahu. Shirin zai fara zuwa daga Ranar Laraba 13-05-2026 a dukkanin shafukan Sada ZUmunta Na Zamani, domin neman karin kuna iya bayyana mana a comments section ko ta private ko ku kira number wayar dake kai. Ashuk Media Services The Reel 𝑭𝒐𝒍𝒍𝒐𝒘𝒆𝒓𝒔.

Address

Tudun Jukun
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ashuk Media Services posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share