14/09/2025
YAU LAHADI _ 14/09/2025
DA DUMI-DUMIN TA: Wani mamakon ruwan sama da aka tafka tsakanin Alhamis da Juma’a a Zariya, a jihar Kaduna, ya yi sanadin ɗaiɗaita yara sama da 470 tare da lalata gidaje aƙalla 270.
Shugaban ƙaramar hukumar Zariya, Ahmad Muhammad Jaga, ya jagoranci tawagar haɗin-gwiwa da ta ƙunshi jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), da Ƙungiyar Red Cross, domin duba yankunan da ambaliyar ta rutsa da su.
Unguwannin da s**a fi fuskantar barna sun haɗa da: Ƙofar Kuyanbana, Gangaren Mobil, Bayan-Cinema a Tudun Wada, Magume, Baƙo Zuntu, da Kamacha a Tukur-Tukur.
Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta shafe gidaje, ta lalata kayan abinci, da na’urorin lantarki. Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce sun shiga halin firgici lokacin da ruwan ya mamaye gidajensu, abin da ya tilasta musu ficewa a tsakiyar dare.
Tuni jami’an Red Cross, reshen Zariya, s**a fara raba kayayyakin tallafi ga waɗanda abin ya shafa. Tallafin ya haɗa da abinci, barguna da ɗaukin gaggawa ga iyalai da s**a rasa matsuguni.
Ashuk Media Servicess
Abubakar Hussaini Kidandan
Highlights
100M Followers