IBee Assalafiy

IBee Assalafiy أنا مؤمن بكل ما قاله النبي ﷺ الصادق المصدوق
(3)

21/10/2025

Tsarki ya tabbata ga Allaah
Lallai yanzu ansamu wasu

20/10/2025

Allaah Yajikan
ALBANI ZARIA 😓🙏

20/10/2025

Sheikh Albaniy Zaria RahimahulLaah

20/10/2025

Sheikh Albaniy Zaria: Duk wanda kaga munyi condemning karya ne ka dawo daga baya kaga ba haka bane

An kashe jiki, amma ba a kashe da'awar da koyarwar baNifa, in dai kai kana kaunar Malam Albaniy Zaria, wallahi nima ina ...
19/10/2025

An kashe jiki, amma ba a kashe da'awar da koyarwar ba

Nifa, in dai kai kana kaunar Malam Albaniy Zaria, wallahi nima ina kaunarka dari bisa dari. Domin Malam Albaniy ba mutum bane kawai alama ce ta gaskiya, tsantsar sadaukarwa da rayuwar ilimi. Ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen hidimar addinin Allaah, ya yada hadisan Manzon Allaah ﷺ, yana jawo mutane zuwa ga fahimtar sahihiyar sunnah.

Ya rayu cikin kankan da kai, yana tsoron Allaah fiye da komai. Ya hakura da jin daɗin duniya, ya bar tufafi masu tsada domin addinin Allaah ya ci gaba. Ya fi son ganin marayu da talakawa suna samun ilimi a bisa fahimtar mai gidansa Manzon Allaah ﷺ fiye da jin daɗin kansa.

Amma abin takaici, makiyan addini da masu ƙiyayya da gaskiya s**a yi masa kisan gilla. Amma kisan bai kashe tafarkinsa ba domin tafarkin gaskiya ba ya mutuwa. Ya mutu a matsayin shahidi In Shaa Allaah, cikin tafarkin Manzon Allaah ﷺ, kuma Daawar sa da koyarwarsa suna ci gaba da rayuwa cikin zukatan musulmai.

Albaniy Zaria ya kasance malamin da kalamansa ke taɓa rai, ba don neman suna ba, amma don yana faɗin gaskiya saboda Allaah. Duk wanda yake son gaskiya, yana son Albani. Domin kaunar Albani kaunar Manzon Allaah ce, kaunar hadisi ce, kaunar abin da Allaah yake so ce.

Allaah ya gafarta masa, ya ɗaukaka darajarsa, ya saka masa da mafificin matsayi a Aljannar Firdaus. Ya kuma tabbatar da tafarkin Sunnah.

28 Rabīʿ al-Thānī 1447
19 October 2025
IBee Assalafiy

19/10/2025

Sheikh Albaniy Zaria: Hamawiyyah (Muqaddima) 1/6

19/10/2025

Sheikh Albani Zaria: Haqqin Makwabta 2/2

Address

Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when IBee Assalafiy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to IBee Assalafiy:

Share