
03/08/2025
BIKIN MURNAR CIKA SHEKARU BIYU NA MAI GIRMA SHUGABAN MAJALISAR WAKILAI TA TARAYYA DA KWAMITIN MEDIA TA ZARIA TA SHIRYA.
Wurare masu muhimmanci 3 da kwamitin New Media ta halarta;
-Gidan marayu
-Asibitoci
-Gidan gyaran hali
Alhamdulillah, cikin ikon Allah yau Asabar, 02/08/2025 aka shiga kwana na biyu da Kwamitin Media ta mai girma Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon Abbas Tajudeen PhD GCON (Teejay Media Centre) da Zaria s**a gudanar da ziyarce-ziyarce na musamman ga wurare kamar Gidan Marayu, Asibitoci da kuma Gidan Gyaran Hali da aka fi sani da Prison.
Nan gidan Marayu kenan dake Kofar Kibo Zaria idan cikin ikon Allah muka sami halarta a hukumance tare da kai masu tallafin ababe na musamman tun daga abinci, abin sha, kayan kwalama na yara da kayan wasannin, sabulai, dettol da dai ababen da ba'a rasa ba.
Tabbas, mun yi farin ciki yadda muka ga yaran cikin farin ciki da kuma kyakkyawar kula da suke samu da hadiman gidan karkashin jagorancin Malam Awai Sarki Mohammed Allah SWT ya saka masu da Alkhairi bisa da kokarin da suke yi.
Muna kuma rokon Allah SWT ya sakawa mai girma Speaker da Alkhairi wanda a sanadin shine muka amfana har muka yi tunanin amfanar da wasu cikin yardan Allah, Allahumma Ameen!
Lawal Shehu Aliyu
SLA New Media
02/08/2025