
21/07/2025
SHAHADAR IMAM ALIYU ZAINUL ABIDIN A.S
Yau 25 ga watan Muharram ya yi dai-dai da ranar shahadar shugaban masu zuhudun duniya, sarkin masu bauta wa Allah ta'ala kuma shugaban masu kyauta Aliyu ɗan Imam Husaini Jikan Manzon Allah s.a.w.w.
Shi dai Imamu Zainul Abidin shi ne Aliyu ɗan Husaini ɗan Aliyu ɗan Abi Ɗalib kuma ɗan Fatima yar Muhammad Rasulullah s.a.w.w.
Mahaifiyarsa ita ce Shah Zanan ƴar Yazdajir wani sarkin Farisa a ƙarni na ɗaya bayan hijira.
Ya kasance mutum mai yawan ibada da gudun duniya, Shi'a da Sunna sun yi ittifaƙi cewa shi mutum ne abin koyi ta kowanne fanni, musamman zuhudu da bautar Allah da kyauta, idan Allah ya yi mana muwafaka lokacin haihuwarsa ya zagayo za mu kawo misalan hakan kasantuwar wannan lokacin juyayi ne.
Shi ne namiji daga ƴaƴan Imam Husaini a.s da ya yi saura a Karbala, wanda yake da shahararren zancensa dinnan "Da kun ga me na gano a Karbala da idanuna, da ba ɗayanku da za ya kara yin murmushi abada"!
Ya yi shahada a cikin garin kakansa Madina mai haske a shekara ta 95 bayan hijira yana ɗan shekara 57, sanadin guba da aka shayar da shi.
Allah ya la'anci makasanka, ya gaggauta bayyanar wanda zai dauki fansarku
أَيُّهَا النَّاسُ أَنَا ابْنُ مَنْ دَنا فَتَدَلَّى فَكانَ قابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنى، أَنَا ابْنُ مَنْ صَلَّى بِمَلَائِكَةِ السَّمَاءِ، أَنَا ابْنُ مَنْ أَوْحَى إِلَيْهِ الْجَلِيلُ مَا أَوْحَى،
عظم الله اجوركم باستشهاد رئيس البكائين و نور المؤمنين الإمام علي السجاد(عليه السلام)
https://t.me/SheikhAdamuT