11/02/2025
"Jan hankali akan zaman Lafiya da Yancin Addini a Cikin Makarantu ko Hukumomin Gwamnati" - Rubutun babban lauyan Najeriya, Sunusi Musa (Senior Advocate of Nigeria)
Alhamdulillah, ance shugabbanin darikar Tijjaniya sun zauna da hukumar jami’ar Tarayya dake Dutsinma a Jihar Katsina. Ance kuma an cimma matsaya an Kuma baiwa daliabai damar ci gaba da yin wazifarsu kullum.
Ya dace kowane mutane sun rinka gane iyakarsu a komai. Idan mutum yana aiki a wata ma’aikata ta gwamnati, ya tsaya iya aikin da aka ba shi. Ko da wasu suna wani abu da mutum yake ganin ya sabawa fahimtarsa, bai dace yayi amfani da ofishinsa don hana abinda dokar da ta kafa ofishin nasa ko ma’aikatar bata hana ba.
Ita Jami’ar nan daga sunanta ma zaka ga ance ta tarayya, kaga daga nan kasan kenan hadin gambizane. A hadin gambiza kuma zaman hakuri akeyi.
Irin wanan ya taba faruwa muna Law School, wata asabar yan NASFAT sunzo gudanar da wani zikiri a masallaci, wasu masu zafin ra’ayi a cikin shugabannin MSS s**aje s**ace zasu koresu har akayi hatsaniya. A lokacin bana manta yadda Daraktan Mulki kuma Sakataren Council of Legal Education na loakcin, Yusuf Shehu Usman ya gargademu akan cewa Masallaci bana MSS bane na makaratane, kuma bamu da hurumin hana yin wani zikiri a ciki. Haka aka kashe wutar. Na yabawa Darakta mulki yadda yayi amfani da wisdom aka bar maganar ba tare da an hukunta wani dalibi a cikin wadanda s**a yi kokarin tada hatsaniya ba.
Jama’a don Allah mu gane cewa Gwamnati fa ta kowace. Yadda idan kana da dan musulmi dan darika kake da hakkin Gwamnati ta baka damar gudanar da addininka iya fahimtarka matukar bai shiga hakkin wasu ba, haka ma Musulmi dan Izala ko kirista yake da wanan damar. Idan mutum yana son kada ya bari a yi wani zikiri na daban da ya saba fahimtarsa, abinda ya dace shine kawai ya gina tasa ma’aikatar ko makaranta ya kuma kafa sharadinsa na cewa shi ga tsarinsa. Wanan babu wanda ya isa ya ce masa don me. Idan ma wani yayi magana sai muce a bar masa kayassa, hakk