
22/07/2025
📰 Sanata Natasha: "Dakatar da ni tun daga farko ya kasance na bogi ne"
A ranar Talata, 22 ga Yuli 2025, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi mata na watanni shida ba bisa ka’ida aka yi ba, kuma za ta garzaya Kotun Daukaka Kara domin neman fassarar hukuncin da Kotun Tarayya ta bayar a baya.
Sanata Natasha ta bayyana cewa an hana ta shiga Majalisar Tarayya da karfi, inda jami’an tsaro s**a tsare ta a ƙofa duk da cewa ta je a kafa.
Ta ce hukuncin Kotun Tarayya na ranar 4 ga Yuli ya nuna cewa dakatarwar da aka yi mata tayi tsanani kuma ta tauye 'yancin wakiltar jama’arta.
Sai dai har yanzu Majalisar Dattawa ta ki aiwatar da wannan hukunci, tana cewa har yanzu bata karɓi kwafen hukuncin da aka tabbatar da shi (Certified True Copy) ba.
Natasha ta ce wasu daga cikin takardun da aka yi amfani da su wajen dakatar da ita 'yan fotokofi ne na rajistar halarta, ba takardun doka ba, don haka lamarin ya kasance na bogi tun daga farko.