Media Forum Yola

Media Forum  Yola MEDIA FORUM YOLA ๐ŸŽฅ๐ŸŽฅ๐ŸŽฅ

ZIYARA TA MUSAMMAN GA  HAJIYA AISHATU (AJUJI) UWAR GIDAN MARIGAYI  MALAM DANLADI DAKE UNGUWAR NEPA JIMETA YOLA ADAMAWAA ...
22/07/2025

ZIYARA TA MUSAMMAN GA HAJIYA AISHATU (AJUJI) UWAR GIDAN MARIGAYI MALAM DANLADI DAKE UNGUWAR NEPA JIMETA YOLA ADAMAWA

A kwanakin bayane Sheikh Muhammad Adamu Abbare wakilin yanuwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na da'irar Gombe tare da rakiyar yan'uwa na da'irar Yola zuwa ziraya ga dottijiya masoyyar Manzon Allah da Ahlubaiti (as) Hajiya Ajuji wacce ita uwar gidace ga marigayi dattijon arziki cikin dattawan garin jimeta Malam DANLADI Wanda kuma Allah taala ya bashi yawan zuriya na yaya da jikoki da yayan jikoki masu kimanin wajen 300+

MUNA ROKON ALLAH TAALA YAYIWA ZURIYA ALBARKA ALFARMAR SHUGABA DA IYALANSA TSARKAKA

Muna rokon Allah taala ya kara haskaka makwancin Malam ฦŠanladi ita kuma Hajiya Ajuji da take raye Allah ya kara mata lafiya da nisan kwana kuma yasa tayi kyakyawar karshe Alfarmar shugaba da iyalansa tsarkaka

22-7-2025
Media Forum Yola

Muyi Salatin Annabi (saww) ga ruhin Mama Saliha (Hari Jamo) mahaifiyar Jagora Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) albarka...
21/07/2025

Muyi Salatin Annabi (saww) ga ruhin Mama Saliha (Hari Jamo) mahaifiyar Jagora Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) albarkacin Imam Ali Bin Husain Zainul Abideen (as) Allah ya jaddada Rahma ga ruhin ta.



25/Muharram/1447
21/July/2025

ูฑู„ุณูŽู‘ู„ูŽุงู…ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ูƒูŽ ูŠูŽุง ุฃูŽุจูŽุง ุนูŽุจู’ุฏูุงู„ู„ูŽู‘ู‡ูุŒ ุฏูŽู…ูู†ูŽุง ูˆูŽู…ูŽุงู„ูู†ูŽุง ููุฏูŽุงุกูŒ ู„ูŽูƒูŽ ูŠูŽุง ู…ูŽูˆู’ู„ูŽุงูŠูŽ.CIKI TARUKAN ASHURA AN BADA K...
21/07/2025

ูฑู„ุณูŽู‘ู„ูŽุงู…ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ูƒูŽ ูŠูŽุง ุฃูŽุจูŽุง ุนูŽุจู’ุฏูุงู„ู„ูŽู‘ู‡ูุŒ ุฏูŽู…ูู†ูŽุง ูˆูŽู…ูŽุงู„ูู†ูŽุง ููุฏูŽุงุกูŒ ู„ูŽูƒูŽ ูŠูŽุง ู…ูŽูˆู’ู„ูŽุงูŠูŽ.

CIKI TARUKAN ASHURA AN BADA KYAUTAR JINI GA MABUฦ˜ATA A DA'IRAR IBEJU LEKKI LAGOS STATE

Da yammacin jiya Lahadi Yan'uwa musulmai almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na garin Lagos s**a bada kyautar jini ga mabuฦ™ata albarkacin Imam Hussain (As).

Yayin bada jini ma'aikatan asibitin sun nuna farin cikinsu sossai tare da godiya ga yan'uwa kan wannan aikin alkhairi.

25 Muharram 1447 - 21July 2025
Media Forum Yola

19/07/2025

ู†ูู‚ูŽุฏู‘ูู…ู ุชูŽุนูŽุงุฒููŠู†ูŽุง ุฅูู„ูŽูŠู’ูƒูŽ ูŠูŽุง ู…ูŽูˆู’ู„ูŽุงู†ูŽุง ูŠูŽุง ุตูŽุงุญูุจูŽ ุงู„ู’ุนูŽุตู’ุฑู ูˆูŽุงู„ุฒู‘ูŽู…ูŽุงู†ู

WANI YANKI NA JAWABIN SHEIKH SIDI ABDULLAHI ASHURA WANDA YAYI A WAJEN ZAMAN JUYAYIN ASHURA SHURAFA'U S**A GABATAR YAU ASABAR A DA'IRAR YOLA.

Media Forum Yola

19/07/2025

Yadda Yan'uwa dake muhallin zaman juyayin Ashura s**a rude da kuka yayin Sayyid Abdullahi Ashura yake gabatar da jawabi kan al'amarin ashura a Da'irar Yola, wanda Sharifai na harkar musulunci s**a shirya.

Media Forum Yola

RAHOTO| YADDA AKA GABATAR DA MAJLISIN JUYAYIN ASHURA WANDA SHURAFA'U S**A SHIRYA A DA'IRAR Cikin alhini da juyayi aka ga...
19/07/2025

RAHOTO| YADDA AKA GABATAR DA MAJLISIN JUYAYIN ASHURA WANDA SHURAFA'U S**A SHIRYA A DA'IRAR

Cikin alhini da juyayi aka gabatar da zaman juyayin Ashura wanda sharifai s**a shirya a babban ษ—akin taro na Univasal Basic Of Education (U.B.E) dake garin jimeta babban fadar jihar Adamawa

An fara da bude taro da addu'a wanda sidi Nuhu Loko ya gabatar sai karatun Alkur'ani daga Sayyida Ruฦ™ayya Umar Hamza, sannan Ziyarar Aba Abdullah Hussain (as) Ya Biyo Baya, Daga nan aka baiwa Sha'irul Hussain Shamsu Fudiyyah Tare da Malam Abdullahi Lushi S**a gabatar da waken juyayi tare da ma'atam.

Sidi Umar Hamza Hussainiyya shine ya gabatar da Babban Baฦ™o Sheikh Sidi Abdullahi Ashura (Bauchi) domin ya gabatar da jawabi kan al'amarin ashura, yayin gabatar da jawabin nashi Sidi Abdullahi yayi jawabai masu sosai rai da sanya zubar kwalla (Hawaye).

Kuna iya kallo cikin hotuna yadda yan'uwa s**a ruษ—e da koke-koke suna kiran "YA HUSSAIN" yayin da Sidi Abdullahi yake gabatar da jawabi, Sannan Malam Nasiru (Mai Shayi) ya gabatar da nashi waken juyayin Sidi Umar Hamza ya rufe taron da addu'a.

ูฑู„ุณู‘ูŽู„ูŽุงู…ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ูƒูŽ ูŠูŽุง ุฃูŽุจูŽุง ุนูŽุจู’ุฏู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูฑู„ู’ุญูุณูŽูŠู’ู†ูุŒ ู‚ูŽุฏู’ ุฎูŽู„ูŽุนู’ู†ูŽุง ู‚ูู„ููˆุจูŽู†ูŽุง ุนูŽู„ูŽู‰ ู‚ูŽุงุชูู„ููŠูƒูŽ ูŠูŽุง ุฃูŽุจูŽุง ุนูŽุจู’ุฏู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูฑู„ู’ุญูุณูŽูŠู’ู†ู

20 MUHARRAM 1447 - 19 July 2025
Media Forum Yola

YADDA MUHALLIN ZAMAN JUYAYIN ASHURA YA KASANCE YAYIN DA SAYYID ABDULLAHI ASHURA YAKE GABATAR DA JAWABI A DA'IRAR YOLA Ya...
19/07/2025

YADDA MUHALLIN ZAMAN JUYAYIN ASHURA YA KASANCE YAYIN DA SAYYID ABDULLAHI ASHURA YAKE GABATAR DA JAWABI A DA'IRAR YOLA

Yan'uwa sun fashe da kuka yayin da Sayyid Abdullahi Ashura yake gabatar jawabi a wajen zaman juyayin Ashura wanda yan'uwa sharifai s**a shirya, taron na cigaba da gudana ne a babban dakin taro na UBE dake garin jimeta.

Media Forum Yola

19/07/2025

KAITSAYE

KAI TSAYE DAGA WAJEN ZAMAN JUYAYIN ASHURA WANDA SHARIFAI S**A SHIRYA A DA'IRARAn fara gabatar da zaman juyayin Ashura wa...
19/07/2025

KAI TSAYE DAGA WAJEN ZAMAN JUYAYIN ASHURA WANDA SHARIFAI S**A SHIRYA A DA'IRAR

An fara gabatar da zaman juyayin Ashura wanda yan'uwa sharifai s**a shirya a da'irar Yola, taron na cigaba da gudana ne babban dakin taro na UBE dake garin jimeta.

Media Forum Yola

HALMIN-NASIRIN YANSURUNA!!!LABBAIKA YA HUSSAIN!!!Sharifai Na Harkar Musulunci, Karkashin Jagorancin Sayyid Ibrahim Zakza...
18/07/2025

HALMIN-NASIRIN YANSURUNA!!!

LABBAIKA YA HUSSAIN!!!

Sharifai Na Harkar Musulunci, Karkashin Jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) Da'irar Yola. Na Gayyatar al'umma zuwa gagarumin zaman juyayin ASHURA a Yola, wanda Sharifai s**a shirya.

Zaman zai kasance kamar haka:-
- Ranar: Asabar 19 Yuli, 2025
- Lokaci: 10:00am na safe
- Muhalli: U.B.E HALL Jimeta-Yola

Akwai Mashahuran Malamai da Mawaka da zasu hakarci wannan zama I/Allah.

BABBAN BAKO ME JAWABI: Shaikh Sidi Abdullah Ashura Bauchi.
BABBAN BAKO MAWAKI: Shamsuddin Fudiyyah Kano (Sha'irul Hussain)

SANARWA: Sidi Umar A. Hamza Husainiyya Yola, a Madadin Shurafa Forum Yankin Adamawa.

Allah ya bada ikon halarta, Ameen.

Media Forum Yola

Address

Yirol

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Media Forum Yola posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share