28/09/2025
APC Ta Ce Maganganun Atiku Kan Harin Boko Haram Cike Suke da Munafunci
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Hon. Mohammed Abdullahi, ya sa hannu, APC ta zargi Atiku da amfani da mummunan harin wajen neman maki na siyasa, maimakon nuna tausayin gaskiya ga mutanen da abin ya rutsa da su, kamar yadda Fombina Times ta ruwaito.
Sanarwar ta ce: “Maimakon Atiku ya tsaya a gefen al’umma, ya fitar da sakon ta’aziyya cike da ƙarya, wuce gona da iri da kuma jirkita gaskiya. Wannan hali ya nuna halin siyasa mai cike da son kai da munafunci.”
APC ta kuma danganta Atiku da gazawa wajen magance matsalar tsaro lokacin da yake a cikin gwamnatin PDP, tana mai cewa “tushen rashin tsaron da ake fama da shi a yau ya samo asali ne daga gazawar wannan gwamnati.”
Haka kuma jam’iyyar ta yi zargin cewa Atiku bai taba kawo muhimman ayyukan raya ƙasa ga jihar ba, illa gina harkokin kasuwancinsa, inda ta ce har ma da garinsa Jada ba ya da ingantaccen ruwa ko hanyoyi har sai lokacin da gwamnatin APC ta yi gyara.
Sanarwar ta ci gaba da tambaya: “Ina Atiku yake lokacin da Boko Haram ta mamaye Madagali, Michika da Mubi? Ina yake lokacin da sansanonin ‘yan gudun hijira s**a mamaye Bajabure, Malkohi da Fufore? Ina yake lokacin da ma’aikatar AUN tasa ta rufe saboda rashin tsaro? Shiru. Bai bayyana ba.”
Sai dai a ƙarshe, jam’iyyar APC ta miƙa ta’aziyya ga al’ummar Wagga Mongoro, ta yi addu’ar samun rahama ga waɗanda s**a mutu da kuma sauƙin jinya ga waɗanda s**a jikkata. Ta kuma tabbatar da aniyar gwamnati wajen kawar da ragowar Boko Haram gaba ɗaya.
Shin Atiku ya yi kuskure wajen yin wannan magana a irin wannan lokaci?