23/11/2025
Ba zan bar jini ya cigaba da zuba a Arewa ba, zan magance matsalar tsaro: Shugaban Tinibu
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta bar Arewa ta ci gaba da zubar da jini ba, tare da tabbatar da cewa za a kawo ƙarshen matsalolin tsaro da s**a haɗa da ta’addanci da ’yan fashi da makami a arewacin Najeriya.
Tinubu ya bayyana cewa babu wani bangare na ƙasar da za a bari “ya ci gaba da zubar da jini yayin da gwamnatin tarayya ke kallo kawai”.
An isar da sakon shugaban ne a ranar Asabar yayin bikin cika shekaru 25 da kafuwar Arewa Consultative Forum (ACF) da aka gudanar a Kaduna. Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya wakilci Shugaban Ƙasa a taron.
Shugaba Tinubu ya ce ya gaji matsalar tsaro mai “tsanani”, amma ya kuduri aniyar dawo da zaman lafiya a fadin ƙasa.
Haka kuma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta farfaɗo da tattalin arzikin yankin Arewa, yana mai jaddada fatan fara fitar da danyen mai daga gonakin Kolmani da kuma wasu sabbin damar cigaba da ake sa ran za su farfado da tattalin arziki.